☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER FIVE ☘️☘️☘️☘️☘️

           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER FIVE

  A washegari kuwa Wabili da mijinta suka dukufa gyara wajen da Ramatu da mijinta zasu zauna. Sai da ta gama ta zaga ta shiga gidan su ta tarar da su sun zauna jugum jugum. Ba matar ba, ba mijin ba.

 Bayan ta gai da Musa ta ce da Ramatu “Adda ina kayan suke in fara mikawa Mallam”?

 Tana kokarin yunkuruwa suka ji muryar Mallam Jibo. Musa ne ya je ya shigo da shi. Su suka dage suna kokarin fitar da kayan suna kuma kokarin shiga da su gidan Mallam Jibo. Ramatu kuwa sai fadi take “wallahi mallam ban dauki kayan kowa ba. Na rantse da Allah ban daukar mata kaya ba”.

 Mallam Jibo ne yace “don Allah ki bar zancen nan haka. Kowa ya san bake ki ka dauki kayan nan ba. Kaddara ce Allah ya kawo mana ita”.

 Shi dai Musa ya kasa cewa komai. Bayan an gama kwashe komai, suka fito daga gidan. Mutanen unguwa ne jingim suna kallonsu kamar wadansu bakin halitta. Wani abu ne kamar kashi ya taso ya tokarewa Jibo a makwogwaransa. Take yaji numfashinsa ya na daukewa.

 Ya dafe kirjin yana jan salati. Mallam Jibo da wasu ‘yan unguwa da suke kallon abin da ke faruwa suka yi kansa da nufin kawo masa dauki.

  Wasu na kuwwar a kai shi asibiti. Ya rike hannun Jibo alamun son yin Magana da shi. Cikin murya kasa kasa yace “shiga da ni gidan ka”.

 Cikin gidan aka shiga da shi kamar yadda ya umarta. Ramatu na kokarin shiga da tabarma dakin da aka bata a gidan Mallam Jibo sai gani tayi ana shigo da mijinta a rike wajen mutum hudu sun riko shi.

 Ba ta san lokacin da ta yar da kayan hannunta ta nufi wajensa da sauri ba. Dan kishingidar da shi akayi bakin barandar tsakar gidan. “yi sauri Wabili kawo mana ruwa” in ji Mallam Jibo.

 Ramatu kuwa na tsugunne a gabansa tana kuka. Ta na fadin “Mallam ka yi hakuri. Wallahi ban dauki kayan kowa ba”.

 “Yi shiru Ramatu nima na san baki dauki kayan kowa ba. Amma Allah ya na jarraba bawansa ta hanyoyi da dama”, ya amsa mata cikin muryar da daga ji kasan cikin karfin hali yake Magana.

 Wabili ta iso da ruwan Mallam jibo ya tallafi kan sa Ramatu ta kara masa ruwan. Ya kuwa sha mai dan dama, san nan ya janye kansa alamun ya ishe shi.

 Duk abin dake faruwa Baffa na makale a bayan kyauren gidan kamar yadda yayi jiya da ake rigimar police yana kallonsu.

 “sannu Musa”.

 “yawwa sannu Jibo. Na gode da kaunar da kanuna min. Allah ya saka da alkhairi. Ka yi hakuri ga amanar iyali na na baka”.

 “wacce irin magana kake yi. Bari Mallam Sanusi yaje wajen mai Unguwa yanzu zai zo da mota a kai ka asibiti”.

 Wani irin kallo ya yi masa mai tsawon gaske. San nan ya saki ajiyar zuciya yace “kayi hakuri. Baffa…….. Ramatu da da da ka kk kulllla”….. Bai karasa fadar abin da yayi niyyar fada ba, harshen sa ya karye sai ya fara Kalmar shahada. Yana kaiwa karshe Allah ya yi ikonsa a kansa.

 Mutuwar ta girgiza Ramatu matuka. Take tayi luu ta fadi Wabili ta tare ta. “shiga da ita ciki”. Shine kawai abin da Jibo ya iya fadi.

 Haka tattage  ta shiga da ita daki. Ta kasa kuka sai wata irin ajiyar zuciya ta ke saukewa. Duk abin da ya faru akan idanun Baffa suka faru. Yana nan make a maboyarsa bayan kyauren gidan. Shi bai san mutuwa ba, amma salatin da yaji mutanen da suka taru damkar a kofar gidansu ya saka shi sanin wani abin tashin hankali ya same su.

 Wani makocinsu ya je ya sanar da honourable mutuwar kaninsa. Malamai sun yi gaskiya da suka ce da yawa masu ihu idan an yi mutuwa munafukai ne. To shima haka ya cika musu waje da kwarmaton kaninsa da shi kadai ne yayi saura masa a duniya yau mutuwa ta raba su.

 Yadda ya dinga nuna tashin hanakali kamar bashi ne jiya ya dinga ci masa mutunci ba. A haka a ka hada mallam Musa aka kai shi gidan sa na gaskiya. Gidan da kowa sai yaje shi. Kuma alamu sun nuna yayi dace. Allah ya sa mu dace.

 Ya rasu ranar jumma’a. Aka sallace shi a masallacin jumma’a na unguwarsu. Mutane da suka yi dafifi wajen raka shi makwancinsa ba a Magana. Daga makabarta honourable ya sallami jama’a a kan cewa baya son zaman makoki.

 Sai wajen la’asar hankali ya dan kwanta, Wabili ta fara jajen neman Baffa. Duk an duba ba a ganshi ba. Ashe dan marayan Allah har makabarta ya bisu ba tare da sun ganshi ba.

 Sai da kowa ya watse san nan ya tafi kan kabarin mahaifinsa yayi tsaye. Shi ya kasa kuka. Ba shi kuma da cikakkaen wayon da zai yi masa addu’a. sai daga baya ya tuna idan sun je ta’aziyya da iyayensa ya kan ji suna fadin “ya hakuri. Allah yaji kan musulmi. Allah yayi musu rahama”.

 Tuna wan nan kalami sai shima ya tsugunna gaban kabarin yace “baba ya hakuri. Allah yaji kan musulmi. Allah yayi musu rahama”.

 Bayan nan sai ya rasa me zai ce sai kawai yayi kwanciyarsa a gefen kabarin, yana kallon kabarin kamar baban nansa zai fito su tafi gida.

 Har bayan la’asar ba Baffa ba labarinsa. Wani yaro Wabili ta tura kofar gida inda mallam Jibo ya shimfida ‘yar tabarma da makotansu guda biyu suna amsar gaisuwa. Nan aka sanar da shi rashin ganin Baffa.

 Nan fa hankalinsu ya tashi.

Har makarantarsu an je neman sa ba a ganshi ba. Sai goshin magariba wani mutum ya shaida musu ya hange shi dazu a hanyar makabarta.

 Wajen su biyar suka runguda suka nufi makabartar. Allah da ikonsa nan kuwa suka same shi a gefen kabarin mahaifinsa yana kwance.

 Kowa a cikinsu sai da ya zubar da kwalla a yanayin da suka ganshi.

 Mallam Jibo yayi karfin hali ya karasa kusa da shi. Yace “tashi Ahmadu. Zo mu tafi gida”.

Sai a lokacin ya farga da zuwansu wajen. Ba tare da yayi wa kowa Magana ba ya mike ya shige gaba suma cike da tausayinsa suka bi bayansa.

 Ko shigarsa gida bai sanya Ramatu kuka ba kamar yadda da yawa ganinsa ya saka su sabon kuka. Ita kam sai dai ta bi wan nan da kallo ta bi wancan da kallo. Sai ta koma kamar wata gaula wacce bata fahimce me ake cewa ba.

 Ko gaisuwar da makota ke shigowa sai Wabili ce ke amsa musu. Sai washegari ne ma da wata gwaggon ta tazo daga rugarsu sai a san nan ta samu kukan ya zo mata. Shima tana yi tana fadin “Mallam ka yafeni. Wallahi ban dauki kayan kowa ba”.

 Mallam Jibo kuwa yayi wani fayau da shi, sai ka ce wanda ya tashi jinya. Wabili ce mai dan karfin halin saka shi ya sha dan farau faru ko kunu, amma batun abinci da ga shi har Ramatu sun kasa ci.

 Baffa kuwa dama da yake mai shiru shiru ne baya wa kowa Magana, sai dai ya dinga bin mutane da kallo. Da ya dan faki ido ya falla da gudu ya nufi makabarta yayi kwanciyarsa gefen kabarin mahaifinsa.

 Kullum haka Mallam Jibo yake jigilar zuwa ya dawo da shi. Bayan an yi uku ya zaunar da shi yace “Baffa me yasa kake zuwa kabarin babanka ka kwanta”?

 Kamar ba zai ba shi amsa ba, sai can ya dan nisa yace “Baba shi kadai ne a can shine nake zuwa in taya shi zama kar yaji tsoro”.

 Shafo kansa yayi yace “kayi hakuri ba shi kadai ba ne”.

 “To shi da waye. Naga kai ka taho su Baba mai shayi ma duk sun taho ba kowa a wajensa. Ga Inna da Gwaggo duk suna gida”?

 Sai da ya matse kwalla san nan yace “shi da ayyukansa na alkhairi ne. Ka san babanka yana yin salla a masallaci ko”?

 Gyda kansa yayi bai yi Magana ba.

 “To ita sallar ita ce take zuwa tana taya mutum zama a cikin kabari”.

 “ke nan duk sallar da Baba yayi za ta taya shi zama a cikin gidan kasan da aka ajiye shi”?

 “kwarai kuwa Ahmadu”.

 Sai yaga yana murmushin mai nuna alamun farin ciki. Tamabayarsa yayi ya ce “murnar me kake yi”.

 “Na san Baba yana sallah da yawa saboda haka sallah masu yawa zasu taya shi hira. Amma Abba idan nayi wata sallar na tura mi shi zata taya shi hira”?

 Ya shafi kansa san nan yace “ai ba sallah ka dai ba. Duk abin da kayi mai kyau sai an kai masa aikin cikin kabarinsa”.

 Cike da farin ciki yace “daga yau zan dinga aikin lada saboda a kai wa Baba kabarinsa”.

 “Yawwa Ahmadu baban manya. Haka nake son ji. Saboda haka ka daina zuwa kabarinsa, saboda ba a son zuwa kullum kullum. Maimakon haka ka dinga ayyuka masu kyau da Allah yake so sai a tura masa su kabarinsa su dinga taya shi hira”.

  “tam” shi ma ya amsa masa da murna a fuskarsa.

Comments

Popular Posts