AUREN ZAMANI 4

 ** 👩‍❤️‍👨AUREN ZAMANI👩‍❤️‍👨**

WRITTEN BY  RUKAYYA IKRA (UMMU SULTAN)


DEDICATED TO
  
 UMAR ABUBAKAR(DADY UMAR) 


SPECIAL GIFT TO

 KAWATA HINDATU MUSTAPHA🥰😘 


(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

SHAFIN NA KANE DAN UWA  A I INDABO INA GODIYA SOSAI DA SOSAI DA KULAWA💃💃👏

 SHAFI NA UKU

📚🖊️....
**  👩‍❤️‍👨AUREN ZAMANI👩‍❤️‍👨** 


WRITTEN BY  RUKAYYA IKRA (UMMU SULTAN)


DEDICATED TO
  
 UMAR ABUBAKAR(DADY UMAR) 


SPECIAL GIFT TO

 KAWATA HINDATU MUSTAPHA🥰😘 


(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

SHAFIN NAKI NE MY ASMEENAT MARUBUCIYAN BAƘÍN DARE;INA ALFAHARI DA KE;💓💓😘🥰💃💃👏KUBISHI KARDA KUBARI ABAKU LABARI.

 SHAFI NA HUƊU

📚🖊️....Mamaki ammi tafara miya faru hakane khalil bai ɗauki wayarsa ba, anya kuwa lafiya?, 



Daga wayarta tayi ta kira mummy, "yayah khalil fa?dan nayita kiransa shiru bai ɗaga kiranba, kuma malama rabi najira na a makaranta, kinsan munyi zamu haɗu yau, inagidansa yanzu haka", 


Mummy itama mamki abinya bata bai wani jima sosai da fita gida ba, itama ɗaukar wayar tayi tafara kiransa, ina linda ta maida wayan salient dan karda yaji karan a hanasu aikinsu, 


Hankalin mummy itama kanta ya tashi, tashiga kiran salim kosuna tare, amman tasan salim a irin wannan time ɗin baya fita gida, 


Oga salim kwance cikin bargo shida salma, yake mafarki da ɗan uwan nasa cikin wani mawuyacin hali,dan ya ganshi ƙwance da wata suna sex, kiran mummy ya farga da salim daga mafarkin da yakeyi, 


Kasantuwar jikinsu hade yake shida salma wannan dabi ar salma ce, ƙwata ƙwata bata barin nunfashinsu yayi nisa da juna  amanne suke ƙwana, 


Motsinda dayayi na ɗaukan kiran mummy ne itama ta farka, ko kafin ya gaida mummy tuni ta fara magana, " salim ina ɗan uwanka munata kiransa shiru amminku keta nemansa yanzu haka tana gidansa kuma bayanan, nakira nima yafi 5times baya ɗauka ba, Allah dai gasa lafiya", 


Shiru yayi shikansa a ɗaure yana tunano irin mafarkin da yakeyi kiran mummy ya shigo masa, cikin razana ya miƙe yana anbato sunan Allah, tabbas akwai wani abun, "baby kiyi haƙuri bari nafita nadawo aƙwai dan matsala tare da khalil gaskiya",  kiss mai ɗaukan hankali ya manna mata " ki kulan mani da kanki yanzan dawo kinsan saina rama tsungulina ko", 


Dariya tayi itama ta kama hannunsa ta manna masa kiss ɗin "ka kulan mani da kanka pls"


Cikin sauri yazura jallabiya ya ɗauki key ɗin mota, shikansa malam ayuba, yayi mamakin fitowar ogan nasa dai dai wannan time ɗin dan yasan baya fita warhaka, 



Linda kuwa murna kawai take tasami salim a hannunta yanzu sai yarda tayi dashi tunda ta lura bai taba samun irin wannan saƙonnin ba, ko sanbatunsa da yake kiran  sunan khairat bai dameta ba, ita dai tunda ta koyar dashi kuma itama tasami abinda tajima tana nema bazata taba saken da zaya kubuce mataba, sai da tayi ma ishi sannan dan kuwa shikansa salim ɗin hakan namasa daɗi, kowacce siga bawarda linda bata jiyar da salim ba, 


Dagashi tayi "my love tashi ka watsa ruwa dan karda ayita jiranka awaje ko, kabani dukkan wani love danake buƙata daga gare ka, ina fatan gobe zamu sake haɗuwa bye dis time ko tana kai masa wani irin kissa abisa kirjinsa, 


Kamashi tayi cikin salo tana shafa jikinsa tayi toilet da shi, da sakar masu ruwa, shidai salim yakasa aikata komi,saƙonnin da linda tarinka aika masa yake ƙara tunawa, 


Baya iya aikata katabus saida ya watsa ruwanne ma yaɗanji wani sauki, cikin kissa tabi duk jikinsa da cream ta bashi kaya ya maida turare kam kala kala  tashiga feshe jikinsa da shi, 



"My love ga phone ɗinka naga tanata haske inaganin kirane fa,"


Cikin sauri sauri ya ɗauki wayansa, miss call  ɗin daya gani ne barka tai ya dawo dashi cikin hayyacin sa, da sauri ya fara danna number ɗin ammi dan tunda yaga kira haka yasan aƙwai wani abun, Allah yasa badai khairata bace tayi wani aika aikan, 



"Khalil ina kashiga hakane?duk kabi ka tayar da hankalinmu, sai kayi maza kazo gidanka cikin sauri inason ganin ka, ga salim nan ma basai ka kirasu ba dannasan kaga kiransu,"


Bata tsaya jin amsarsa ba takashe wayan, rugume linda yayi ajikinsa, "ina godiya my love kisaurare ni gobe insha Allah", 



Cikin shagwaɓa irin batasan surabu ɗinnan take magana,  "my love way da daddare pls,i need u kusa dani gaskiya", ogogon hannunsa yake ɗaurawa,  "okk kibari zanduba mudaiyi waya bye", 


Yana faɗin haka yayi waje cikin sauri, gidansa ya nufa da gudu yake jan motar, 



Boy friend ɗin linda kamar jira yake khalil yafita, ya kunno kai ɗakinta,  ya sameta ne ƙwance tana kallon waya yasaba binta bisa gadon, mizaya gani, linda da khalil ne sunata wasanninsu, tashin hankali, 


"Linda daga ina kuma kika sami wannan guy ɗin, kiga yarda kike ayyuka dashi koni baki taba mani wannan abunba, aiko zan ɗauki mataki akanku, yana shirin fizge wayan hannunta tayi wuf ta rike wayan da ƙarfi, wallahi habib baka isaba, sanann kuma babu abinda zaka iyama salim muzuba nida kai, malam fitar mani daga ɗaki kawani shigo mani kamar kaɗauki izini na", 


Kallanta kawai yake yaushine linda take gayama magana haka sabida tasami sabon kamu, "while zamu haɗu wlh muje zuwa linda aike daga habib baki kuma samun wani wallahi", Ya buga kofa yayi waje cikin sauri, 



Khalil cikin sauri ya isa gida,yana mamakin minene ke faru haka, a guje yayi parking mota kusa da ta salim ya shiga cikin gidan, abinda yafi ɗaure masa kai waɗannan gigga giggan mazan ga kuma motar kaya abakin get anata yin ɗayan fat ɗin gidansa dasu mike faru hakane?


Sallama yayi cikin sanyin murya, ammi zaune gefe da waya ahannunta, salim nadaga gefe yana waya da salma, 


" barka da isowa, ina kashiga hakane kanemi tada hankalin mutane daga ina kake?" Sosa ƙyaya yakeyi yana inda inda, "tambayar ka nakeyi dan baka office tunda nabi chan", 


Wani shirun ya kumayi chan wata dabara ta faɗo masa, " bayan nafita daga gida shine muka haɗu da nabil yace nazo muje naga sabon gidansa, toh ƙwata ƙwata namanta da phone ɗina acikin mota sai da ya nemi number ɗin wani friend ɗinmu nazo ɗaukowa naji shiru ashe tana mota,"


Shiru gurun ya ɗan ɗauka,ammi ta kwalama nadiyya kira tafito 


"Khalil ga matar kanan jiya aka ɗaura auranku da ita, tunda ita wannan batasan miye ciwan kantaba maza maza kabani takardan ta gida zamuje da ita sai tanemi wani kalanta me irin mugun halinta suzauna tare, amman bazata zama silan lalata mani kai ba sunanta nadiya dɗiyace ga malam rabi kasan dai malama rabi ai", 



Wani irin razana yayi gami da wani irin juyi a time guda, shi kanshi salim ɗin yadan razana sosai da wannan mataki na mummy, anya kuwa mummy nasan khairat kuwa, da kanta tamata kishiya sannan kuma tace saiya saketa, 


" banason dogon nazari ina jiranka yanzunnan wannan matakin da naɗauka ne kuma wallahi babu fashi a cikinsa"


Aguje yayi gurunta ya dafa gwaiwarta, "ammi akanmi zaki rabani da matata dan Allah ammi kiyi haƙuri zata gyara inason khairat duk mugun halinta, kiyi haƙuri kibar mani matata mummy, na ɗauki karin auran da kika mani amman kibarta agidan ta ammi dan Allah", 


Yana faɗi yana zubda ƙwalla, " karda ka kara jayayya da magana ta, maza maza ina jiranka, bairo da paper tamiƙo masa "maza maza inajiran ka",  cikin sauri  sauri salim shima ya sauko, "ammi dan Allah kiyi haƙuri, wallahi ƙanwata zata gyara dan Allah ammi kiyi haƙuri", 


Ammi ko kallo basu isheta ba,  "karda na kuma magana wallahi ranku zaya bachi, kunason ku koyi jayayya ne abinda bansan ku dashi ba, wallahi karda kubari raina ya baci maza maza inaji ranka", wata irin tsawa ta daga masa cikin sauri yana ƙwalla ya rubuta mata saki ɗaya rubutun ma ahargitse yayi shi, yana miƙama ammi yayi fat ɗinsa cikin sauri, 


Salim shi kansa saida yayi ƙwalla koba komi khairat ɗin tare suka tashi kuma ɗiyar ammin ce, 


Ta juya ta kalli salim, "inason ka haɗakan nadiya da salma, sannan inda hali inason salma tazo yau ɗinnan dan ta kama mata kafin ma aikatanta su iso,nadiyya ga gidanki nan, ina ƙyautata zatan bazaki taba bani kunya ba, maza kibi mijinki kibashi haƙuri kafin ƴar uwarki tazo,"


Mikewa ammi tayi tsab tayi gaba bawanda ta kalla acikinsu bare subata tausayi, khairat kuwa daƙyar takai kanta gida, dakin mummy tayi da sauri tana kuka, mummy nazaune aiko aguje tayi kan mummy tana kuka, 


"Mummy ammi da kanta tamani haka,ta koroni kuma yayah khalil yasake ni mummy, wallahi inason mijina mummy kuma tamasa aure dan tashigo da wata gidan harda komi nata tace matar yayah ce", 



Tausayi tabama mummy dan tasan tsab ammi zatayi abinda yafi haka, "kiyi haƙuri kinji khairat babu wanda zaya maki kishiya bare yaraba ki da mijinki, kiyi shiru tashi kije ɗakinki kiyiwanka kiyi sallah kifara addu'a bari naji abinda ke faru dan bansan komi ba akai", 



Harzata fita mummy ta tuna da zata iyakinyi  sallah bari tatseda ta, "khaira takira sunanta, dawo kishiga nan kiyi wanka kiyi sallah, bayanzu zakije ɗakinki ba, kiyi komi anan, aikina da wasu kayan ananma", 


Dady ne ya fito cikin wata tsadaddar shadda, "wai miyake faruwa ne a gidanan haka?ya naji kukan baby kuma? Daga sama sukaji muryan ammi,  


"nida itane nayi abinda ya dace ne, yarinya batada kunya babu kamun kai, inbama Allah yasa khalil nada haƙuri ba, yana juriya da kuma tawakkali aida tuni yana gadon asibi ko kuma yawan bin matan banza, ina nataba ganin irin wannan mugun halin nata, 


Toh wallahi naɗauki mataki kuma yazauna tunda tabari nayi fushi akan wannan halin nata", 



Dady mamakni irin ammi yakeyi, idan fa tayi niyyar abu babuwan da ya isa ya tsedata idanba ikon Allah ba, dan macce ce mai addini ga kuma sanin haƙƙin mutane, shiyasa amintarsu tazo daya da malama rabi, yasha ganin mata da yawa suna zuwa tana gyara masu aure, dole ya haƙura yabi wannan tsarin nata da tayi, 

" haba ammin su miyayi zafii haka mikuma ya faru da baby ne, itafa kaɗai ce yar maccen damuke gani miya farune haka"


Shiru tayi tana kallonsu, "watau alhaji dole dukkanku kuyi haƙuri da abinda na yanke batare da shawara ba, tabbas nayima khalil aure da yarinyan malama rabi warda tadawo karatu daga sudan, kuma ga saƙontanan ka riƙe a hannunka shine dai dai da ita, idan tasami miji tayi wani auran", 



Razana yayi sosai da sosai dajin wannnan babban hukunci,  gyara murya yayi "hajiya asma'u zan ɗauki komi amman bazan ɗauki saki ba, tabbas yau zata koma ɗakinta", 


Sallaman wasu mata ne ya dakatar dasu, amman duk da haka saida tace " alhaji dan girman Allah karda ka ruguza mani tsarina kabari tukuna"


Amsa sallamarsu mummy tayi aka nuna masu daƙin da suke zama dan tattaunawa da mata masu matsaloli,



Cikin sallama ammi ta nufi gurin, tace dasu dan Allah idan babu damuwa suhadu a makaranta yanzu tanada uzuri kuma zasu sami malama rabi agurin, sukayi sallama, makarantan kuwa sukayi, 



..........nabila da mujaheed suka sauke bilkisu bakin get, harzasu tafi, tajuyo jiki babu ƙwari "na gode sosai da temakon da kuka bani" girgiza kai kawai nabila tayi, tace "idan babu damuwa inasan ganinki a makarantan malama rabi gobe insha Allah,"



Mujaheed shidea kallon irin ƙarfin halin matar tasa yakeyi, "swthrt kina ƙoƙarin gyarama ma mutane aure fa, tabbas kinada babban rabo agurin ubangiji tunda kema kina daraja naki,"



Baban fatee yana isowa damasu ɗaukar kaya ya taranda anwuce da bilkisu, umarni ya basu suka ƙwashe kayanta tsab sai gidansu, 



Zama yayi yanata tagumi yana juyayin irin rashin mutumcin da yarinƙa aimata ma hajiya, gashi ita kaɗaice maijure duk wata fitina tashi, tabbas yanzu yasan ba'a raina matan farko matuƙar basu wulaƙanta kansu, dan yasan wasu sukeja ma kansu, amman irin maman fatee ta wuce komi, 


Yadaga kai ya kalli yaransa sannan kuma ya kalli mahaifiyarsu, "agabansu zanbaki haƙuri hajiya dan suma sutayani baki hakƙurin, ina mai matuƙar jin nauyi da kunyar abinda nake aikata maki, tabbas nacika butulu, maiyima ubangiji godiya abisa ni'imar samunki ba, sai na nuna garajena tahanyar aure aure, gashi yanzu duk sun tafi sunabarmu, kiyi haƙuri insha Allah hakan bazata sake faruwaba, 



Bilkisu na tunkaran cikin gidan, mahaifiyarta tayi karo da ita tafito daga falon babansu," bilkisu lafiya haka ko waya babu mike faruwa ne naga kamar fuskarki akunbure take, "



Shiru tayi babu amsa, suna haka sukaji anata buga get, abbah ne yafita ta gaba, yana zuwa yaga motar kaya suna shirin fara zuba kayan agefen titi, salati yasaka cikin tashin hankali yake kiran 


"hajiya zoki gani hajiya zoki gani!!!!," 



Dasauri hajiya tafito ko mayafi babu, wani irin salati tasaka, tana faɗin "wannan ai kayan bilkisu ne" tafa hannu taketa famanyi tana faɗin shikennan bilkisu takashe auran, shikenan  bilkisu zaki tona mana asiri dan ubanki,"


Ciki ta koma da gudunta aikuwa bilkisu nanan tsaye tana shukkun  ƙarasawa sauran ƴan uwanta su kamata da duka, jin wani wawan mari tayi a kuncinta tabita ta haye tanata duka, hayaniyyar surutan ummin bilkisu ya fiddo sauran ƴan uwan nata, 


Daƙyar suka amshi bilkisu a hannun ummi, "toh saiki zo kinemi  wani gidan dan ubanki badai wannan gidan ba, muna zaune lafiya ki kiramana fitina, shikenan gakunan harku uku azaune a gida duk zawarawa, gara hindatu mijinta ne Allah yamasa rasuwa, ammanke da hannatu kilan bakin cikinkune zaya kasheni,mutumi maikirki kullum saiyayo cefane ya miko gidannan kayan abinci basa ɗauke mana amman kikamana baƙin ciki ko?"



Abba ne yashigo yana bata baki "kiyi haƙuri saratu karda hawan juninki ya tashi, ba abinda nafi tsoro irin karda ya ƙwace ɗan gidan nasa mukoma zaman haya nida wadannan yara a 2bedroom", 



.....nadiya datasan kantsiya kuwa ɗakin tabi khalil,gabansa tafaɗa tana lumshe idanu cikin sanyayar murya warda ta hada da salo take anfani, " wannan yanayin baidace da sahibin annuri ba, kaine mafi hasken dukkan samarin duniya, godiya nake miƙawa ga ubangijin sammai da ƙassai da yabani wannan ɗan ɗasheshen saurayi a matsiyin mijina, tabbas nasan nazarce mata masu tarin yawa, dan Allah kayi haƙuri da dukkan abinda ya faru, kayi haƙuri domin nima yau kadai nasan waye Allah yabani a matsayin mijina,ina alfahiri da zabinda ammi da momy na sukamani dan kuwa nasan bazasuyi mani zaben tumin dareba, dariyan da walwalan mijina kawai nake songani, konima hankalina ya ƙwanta, dan inacikin halin bugun zuciya, kuma kai kane kaɗai ne maganinta mijina, kabani damar samun aljannata nima mijina", 


Tunda tafara yakebin ilahirin jikinta da kallo, tako ina batada wata maraba da khairat ɗinsa, amman shi yanzu tsoran ƙyawawan mata yakeyi wallahi, amman kuma gawata ita kuma tazo masa da nata sabon salon, 


Hakanan yatsinci kansa cikin wani irin mugun son yarinyar dan kuwa  kalamanta baƙaramin ratsa zuciyarsa tayi ba, 



Hannu yasa yakai fuskarsa yaɗan goge wasu ƙwalla dasuka faɗo masa, me makon ya maida yahannu ya ajiye aa sai ya kamo hannuwan nadiya ya ɗaura bisa cinyarsa,


Karda kiyi kuka sahibar annuri, warda tazo da wani haske mai haske fuskan masoya, tabba za ki sameni yarda kikeso, za ki sameni tamkar mijin hajiya gareki, ina alfahari da samunki nadiya, Allah ubangiji ya bamu zaman lafiya ameen"


Miƙar da ita yayi tsaye, "yanzu miye kike buƙata mijin naki yafara aikata maki?"kinsan yanzu nizan rinƙa komi kafin", bata ankara ba saiji tayi ya rungumeta jikinsa yana hamdala, sallamar salma ne yasa ya saketa "kije ga matar bros nan tazo duk  abinda ya kamata zata nuna maki dan kuwa ita sarauniyya ce acikin mata, Allah yasa nima tawa sarauniyyar ce warda zannuna a duniya"



Murmushi tayi tafito daga fat ɗinshi, wani corodo ne maiɗan tsayi marabar sa da falo wanda daga gurinne zakayi sama sai fat ɗin da khairat ta bari, 


Abinka gamasu wayewa, ga kuma ilimin kowa na alfahiri dashi, salma ta budɗe baki "sannu da zuwa a maryanmu tabbas kinzo da sabon tsari, irin wannan bazata haka, daman kinanan rowan face ɗin taki kika rinƙa mana kenan?"


Cikin barƙwanci suka saba dajuna sosai, haka salma ta dage suka gyara gidan tsab, daman salma da ƴan guzurinta a jakka, 


"Tau amaryanmu bisimillah ga wannan kiɗan fara dashi, nasan kinsan komi sai dai karda ace muma bamuyi namu ba," dariya sosai nadiya keyi wanda yaƙara burge salma, tabbas ammi tasan kantsiya, yanzu ne anty khairat zatasan kuskuran da ta tafka, wannan daga ganinta khalil saiya mori rayuwa, 



"Kibari sis wallahi takanas su momy suka kira maman mujaheed dan waɗannan kaya, nikam wallahi harnagani da shansu, banda waɗanda friend suka rinƙa ɗirka mani tun a sudan, 


Kinsan momy tajima tana bani labarin my husban, Dan Allah kitayani addu'ar sama masa farin ciki a rayuwarsa sis, dan naji yarda suke yabonki tunkafin inshigo nakejin labarinki sis salma, tabbas zakizama wani kinshiƙi nacikin jikina, kuma dangi sai sunyi alfahari damu, zamu zamar masu tamkar ƴan uwa yarda mazajanmu suke, ina fatan zaki bada haɗin kai sosai sis salma yarda nasami labarinki"


Murmushi salma tayi, ita dai sosai nadiya tayimata, tabbas zasuyi zumunci yarda take faɗi, amman insha Allah bazata taba samun komi daga gareta ba na rayuwar khairat da khalil sai dai taji awani gurun, ko ba komi itama khairat bata taɓa nuna mata wani sauyi ba, sabida haka sirrinta duk yarda zasuyi shiri da nadiyya bazata jishi ba, 



"Karda kidamu ƴar uwa ki daukama ciki ɗaya muka fito daga yau, nima ina godiya da yarda kika karɓeni Allah yabarmu tare yabamu zuriya ɗayyi ba ameen"



Kharat zaune a falon mummy dady nata bata baki, harya fita, bayan tayi wanka tayi sallane, ta tuna da nabila, wayarta ta jawo warda tunda tashiga cikin wannan yanayin bama tabi kansu ba, takira nabila,  cikin kuka tace,  nabila khalil ya sakeni kuma da gaske wannan yarinyar matarshi ce, ina gida dan Allah da safe kisame ni agida,"


Kamar daga sama taji ammin ta  "ai baki ba sauran zaman gida, islamiyya zaki fara zuwa kullum safe da rana wannan wayan ma ɗaya kawai zanbarki dasu, tunda nabilan nazuwa kunhaɗu achan duk abinda zakuyi mutane na kallon ku, wallahi kinbani kunya khairat, yayah ni nafita inada baƙi a makaranta sai kunzo", 


Duk yarda linda taso samun khalil da daddare abun yaci tura, dan kuwa nabila tariga da tahargiza masa lissafi, yarda yaga angyara gidan wani sabon ƙamshi da bai taɓasan irinsa ba yake ziyaran hancinsa, duk wata kunya ta amare tsab ammi tariga ta cirema nadiya ita, cikin wata hadadɗiyar gown yaganta tana cikin gyaran gashin ta, 


" haba mana heartbeat karda kiwani wahalan da kanki, kinga dare yayi fa sosai gashi kingaji wanann iri  gayu haka, kibarshi mugabatar da nafila sannan ko?"


Ƙugunta ya kamo yana kallonta yana tuna khairat, amman yana ƙoƙarin kawar da tunanin dan karda ta ganeshi,zomuje muyi alwala tare ko?


Toilet suka nufa, dan yin alwala, 


Ammi kuwa zaune take dawasu mata sunshigo gurinta da daddre dan karda mutane sugansu, 


"wallahi ammi kinga yarinyanan mijintane ke kamata tana waya da wani waishi saurayinta datayi a makaranta", Shiru tayi tana nazarin wannan mummunan magana



Oga khalil kuwa tsaf ya ɗauki nadiya sai bisa sallaya;daman sun gama tsara komi ita da salma;gurin sallah daban suka ware da komi da komi na idaba duk suna gurin,alƙur'ani duk gasunan kowanne da ma ajinsa duk wanda ya kalla gidan saiya burgeshi dan ya ƙawatu abinka da ƴan zamani,


ko basira rashin tsabtane amman tsarin komi natama haryaso yafina nadiya;



suna idar da sallah yakama goshinta yafara jero addu'ar neman alkairin rayuwa da tsari gami da samun zuriya d
ɗayyiba;












Alƙalamin ƴar mutan katsinawa ruƙayyat ikra(ummu sultan)

Comments

Post a Comment

Popular Posts