☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER FOUR ☘️☘️☘️☘️☘️
*NA*
*HANNE ADO ABDULAHI*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/
CHAPTER FOUR
Washegari ta kasance ranar alhamis. Ba Ramatu mai cikin wata bakwai ba hatta wabili ranar sai da ta koma baccin safe saboda bashin baccin daren jiya da suka ci.
Mazan basu tashe su ba. Mallam Jibo ya barrarko musu bakin shayi da burodi wanda harta Baffa da kwanan sa yafi yawa a gidan sa, shi ya sha san nan ya wuce makaranta. Su kuma iyayen suka kama sana’ar su ta wanki.
Ba zato kawai sai ganin motar police sukayi tayi parking a kofar gidan yayin da honourable ya ke take musu baya a tasa karamar motar. Kafin su gama shanye mamakin su suka ji muryar Honourable yana cewa daya daga cikin dan sandan “shiga muje nan ne gidan. Kuma ko duka ya kama kuyi mata sai ta fadi gaskiya”.
“Yaya dakata gidan wa za a shiga kuma wa za a daka”?
“ kai ka kiyayeni. In ma hadin bakin ne zaku gane ni ba a taba ni a kwana lafiya” Honourable ya amsa wa Mallam Jibo a hasale. Shi kuwa kaninsa mamaki duk ya cika shi ya rasa gane me ke faruwa da yayan nasa.
Ganin police din na kokarin kunna kai gidan Mallam Musa, ya sanya Mallam Jibo daka wani uban tsalle yace da shi “kai dakata Mallam. Ba ka san gidan matan aure bane kake kokarin cusa kan ka”.
“ kaga officer kar ka tsaya ya bata maka aiki. Shiga kawai kayi abin da ya kawoka”.
Mallam Musa gaba daya ya daskare a wajen ganin wai wansa uwa daya uba daya ke kokarin keta masa haddin iyalinsa. Bai ankara ba sai kawai ji yayi hawaye na bin idanunsa.
Ya daure muryarsa na rawa yace “Yaya kayi hakuri koma menene muje gidan mu sasanta”.
“ba wata sasantawa da zan yi daku”. Ya juya wajen officer ya ce da shi “me kake jira ne shiga kayi aikin ka”.
Yana kokarin danna kan sa dan zauren gida, nan fa ta fillo ta motsawa wa mallam Jibo. Ya daka tsalle ya hankide police officer nan ya kuma sanya kwado ya datse kofar gidan yana fadin “ina raye ba wanda ya isa yaci mutunci Musa”.
Suka tashi zasu nuna masa karfin shudin yadin khakin su, shi ma kuwa ya ware kwanji ya nuna musu namijin bafilatane yake. Kan kace meye ‘yan unguwa sun taru a kofar gidan ana son jin bayani abin da ya faru.
Daya a cikin police din ya daga kulki zai kwada masa ya murde shi ya kwace. Ganin suna shirin jin kunya a gaban civilian suka fara kurarin arresting din Mallam Jibo da mallam Musa.
“tun farko da haka ku ka yi da yafi wa kowa sauki” mallam Jibo ya amsa musu. Mai unguwa ne ya karaso yana son sasanta abin da ya faru, amma shi ma jikinsa ya mutu don ganin Honourable da kansa ke rigima da kaninsa.
Shi da kansa yaja honourable gefe domin jin ba’asin wan nan tonon silili da yake neman yi wa dan uwansa. Amma abin mamaki ya nuna masa abu daya ya sani shine a kai matar kaninsa police station tayi bayani a can.
Shi kuma ya sake lallabar Mallam Jibo da ya bude gidan domin a je station a tattauna a can ko domin gudun tonon asiri. Shi kuwa Mallam Musa gaba daya ya sandare a wajen zuciyarsa ce ke masa wani irin daci ya kasa ko motsawa daga inda yake. Ko kalma daya ta gagara fitowa daga bakinsa.
Bayan an bude gidan honourable ya kalli daya daga cikin police ce yace “shiga ka fito da ita”. Ya na kokarin shiga Mallam Jibo ya sake jayo shi san nan ya kalli Honourable yace “Yaya ba ka fahimci matsalar ba ashe? Gidan ne wani kato ba zai shiga kan iyalinmu ba ko mai kuwa yake takama da shi”.
Buya buya ya yi kansa kamar zai dake shi yana fadin “kai har ka isa ka sa min baki a kan harka ta da ta kani na”.
“ai na ga kamar kai burinka ka tozarta kanin naka. Shi yasa na shiga harkar da ba tawa ba. Kuma na fada na kuma fada babu mai shiga gidan makocina ya keta masa haddin iyalinsa ina raye”.
“kai ku yi min maganinsa”, Honourable ya umarci police din. Take kuwa su biyu suka yi kansa da duka ya na rama wanda zai iya yana kuma kokarin tare wanda zai iya.
Ganin suna kokarin yi wa abokinsa illa, ya sanya Mallam Musa shiga tsakanin wanda hakan shi ma ya yi masa sanadin samun nasa rabon dukan. Ganin lamarin yayi tsamari ya sanya mai unguwa rokar police din da su dakata, san nan ya umarci Mallam Musa da ya shiga ciki ya fito da matarsa da kansa.
Cikin tashin hankali ya shiga ya sameta, saboda hayaniyar ce ta tashe ta daga baccin gajiyar gidan sunan Honourable da ta ke yi. “sako hijabin ki mu je”. Shine kawai umarnin da ya bata. Ita ma kuwa ba tare da wani jinkiri ba ta bi umarninsa duk da ba ta san abin da ya haddasa hayaniyar da ta ji a waje ba.
Kafafunta da suka kumbura saboda nauyin cikin da ke jikinta ta ja da kyar ta bi bayan mijinta. In ka gan ta zaka dauka haihuwa ko yau ko gobe, amma cikin nan watan sa bakwai ne kawai.
Da kyar ta yunkura ta hau motar shiga ba biya da su ka zo da ita, wanda ita ma honourable ne ya dage sai a cikinta zasu tafi. Har da mai unguwa aka dunguma zuwa station din. Sai a nanma suka ji laifinsu inda Hajiya Saratu ke tuhumar facalarta watau Ramatu da laifin satar mata Sarkar ta ta gwal wacce ta yi fitar suna da ita.
“wallahi ban satar mata komai ba” ta fada cikin kuka.
“Kwantar da hanakalinki Ramatu. Ni ma na tabbatar ba zaki dauki kayan kowa ma ballantana kuma kayan a gidan Yaya” Mallam Musa shima ya fada idanunsa cike da hawaye na ganin tozarcin da wansa uwa daya uba daya yake yi masa. A ranar ya godewa Allah da iyayensu sun mutu basu ga wan nan bakin ciki ba.
“Au to kace hadin baki ne abin naku. Tun da har kana iya kallon idona ka zageni”.
“yaya wane irin zagi kuma na yi maka”?
“tun da ka iya kallon idona ka ce na yiwa matarka sharri ai ba zagin da ya fi haka”.
Mai unguwa ya sake cewa a aika Hajiya Saratu tazo saboda a ji ta bakin kowa. Nan ma kuwa Honourable yayi tsallen arziki yace matarsa jego ta ke ba zata fito daga gida ba.
Mallam Jibo ya sake fadi cikin zafin zuciya yace “tun da aka fito da mai tsohon ciki ai kuwa mai jego ma dole ta fito”.
Honourable ya sake yin kansa da hargagi, amma DPO ya nuna masa cewar dole mai kayan itama ta zo. A ka tura gida aka taho da ita. Ta maida zance ta ce wa da DPO bayan mutane sun ragu ta umarce ta da ta shiga ta gyara mata dakinta.
“ke kin shiga gyaran dakin na ta “?DPO ya tambayi Ramatu.
“Kwarai na shiga. Duk kayan barkar da ta samu ma ni na jera mata su a cikin sif dinta”. Ramatu ta fadi tana kuka.
“ki na cikin jerawar ke nan ki ka ga Sarkar ta ta ki ka dauka”.
“Na ranste da girman Ubangijin halitta ban dauki komai ba. In da na ga komai haka na jera na gyara mata”. Itama ta amsa wa DPO tana mai share hawayen da yake ta kwaranyo wa daga idanunta.
Nan dai DPO ya ci gaba da kokarin tursasa ta da ta yi confessing satar da ta yi. Ita ma kuwa ta dage akan iya gaskiyarta ke nan.
Sai ya sake canza akalar tambayar ta ta da cewar bayan ita waye ya shigo dakin.
Tace “bayan na gama na shiga bayi ina wankewa Amir ya shigo neman Hajiya”.
“Kul! Ahir dinki. Kar ki kuskura ki yi masa Kazafi. Yaron da bama ya cikin unguwar shi ne kike neman kala ma sa satar da kowa ya san ke kika yi ta”.
“waye Amir din”? DPO ya tambaya.
“Shine babban da na. Amma zo muje daga ciki” Honourable ya ce da DPO. Nan suka shiga wano ofis sabanin inda sauran suke tsaye. Bayan kamar jiran minti goma suka fito.
Nan kuwa DPO ya fara muzurai yana kurarin ko Ramatu ta fito da sarka ko kuma su kulle ta. Ba irin rokon da su mai unguwa ba su yiwa Honourable da matarsa ba, amma sam suka dage su sai an biya su Sarkar su.
Aka tambayi kudinta suka ce dubu dari da tamanin. Aka tambayi Mallam Musa yadda zai biya kudin satar da aka kala wa matarsa ya nuna babu su.
“Ai kuwa ko gidansa ne sai ya siyar ya biya ni kudin sarkata”.
Babu yadda ba ai da su ba su hakura, amma suka kekasa kasa suka ki. DPO ya yi hakuri ya bada belinta ma yaki. Haka suna kallo aka tankada keyarta aka shiga da ita cell aka kulle. Aka kuma gaya musu matso basu biya kudin Sarkar nan ba sai dai tayi ta zama a kulle.
Shi kam Musa dabara ta kare masa sai zafi da zuciyarsa ke yi masa. Mallam Jibo ne ma mai dan kokari tabuka wani abu.
Kai in gajarce muku labari a wan nan rana aka yi cinikin dan kurkuran gidan da Musa yake rayuwa a ciki. Da yake ciniki na gaggawa ne ma, gidan sama da dari uku, da kyar aka samu dillalai suka saye shi dari biyu da goma.
Suka cire la’ada dubu goma. A ka bashi dari biyu. Ita ma nan take aka cire dari da tamanin aka biya Hajiya Saratu kudinta. Police suka ce za a biya kudin takarda da biro da na mai da suka je suka dauko mai laifi. Su ma su ka yagi wata goman. Suka sake samun wata biyar na beli wanda akace free ne.
Nan dai ciki lokacin da bai haura awa biyar ba aka gama shari’a tsakanin mai karfi da marar karfi aka yanke hukunci ba tare da neman wata kwakkwarar shaida ba. A kuma cikin wadan nan ‘yan awoyi ne Musa ya rasa gidan da ya dauki shekaru kafin ya samu ya hada shi.
Shi dai Musa burinsu a fito da Ramatu daga inda aka kulleta. Ba su suka bar station ba sai bayan magariba, wanda tun kan azahar aka fara takaddama.
Suna isowa suka tarar da wata jarrabawar daga Ubangiji. Wanda ya sayi gida yana bukatar gidansa nan da sati biyu, saboda wai zai saka dansa da zai yi aure watan gobe a ciki.
Musa ya daga hannunsa sama yace “Allah nagode maka . Allah ka bani wuyan dauka”.
Jibo yace “ka ga zaman duniya ba na kiyama ba dawo gidana da zama. Ku dau daki daya mu dauki daya mu ci gaba da sana’ar mu a daya.
Duk abin da ake yi Baffa bin su kawai yake da ido. A tunanin su bai fahimtar komai, amma ba tare da saninsu ba yana hankalce da duk abin da ke faruwa. Saboda kawai shi ba mai yawan magana bane sai ka dauka bai san komai ba. Amma duk ya san abin da ke faruwa.
Comments
Post a Comment