☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER THREE ☘️☘️☘️☘️☘️
*NA*
*HANNE ADO ABDULAHI*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/
CHAPTER THREE.
Mallam Musa da amininsa Malla Jibo kamar yadda kowa yafi kiransa da shi su suka tsaya tsayin daka a kan gyaran gidan da Honourable yake yi. Kusan komai na gidan da zai dayu irin su ceiling da tagogi da kuma kofofi da kwano sai da aka daye aka sanya wasu.
Komai suna tsaye akai amma hatta tsoffin kayan gidan da ya cire bai iya diba ya bawa kaninsa ba. Sai wani dan jagaliyarsa ya bawa saboda ya sanar da shi yana gini.
Bayan an gama gini da kwana biyu suka kuke suka wanke gidan nan. Bayan nan suka sanya masa labulayen da carpet na kasa. Duk dakunan da kuma falukan gidan suka saka furniture da aka yo odarsu daga kasar China.
Tsoffin kayan gida Hajiya Saratu ta kwashe ta rabawa ‘yan uwanta. Su kuwa masu wahalar ko carpet din bakin kofa ba a basu shi ba. Gida ya fito radau dashi. Ga section din yaransu maza daban. Ga ita nata yankin manne da dakin Amira wacce a lokacin shekararta biyar kawai amma dakin kamar na sabuwar amarya ‘yar gata. Ga kuma na maigidan. Sashen baki kansa abin kallo ne. kai hatta abin da za a Haifa wanda saboda haihuwar akayi wan nan gyara da muhallinsa.
Yadda mazan suka wahala wajen aikin haka matan suka dandana kudarsu. Sa’ar Ramatu Daya, Wabili na tsaye a kanta. Ita ta dauki nauyin yin komai. Ko yunkuri taimaka mata tayi zata hanata.
Allah ya sa ma laulayin ta yayi sauki, da al’amarin yayi mata yawa.
Honourable da iyalensa basu haura sati biyu da tarewa ba, Allah ya sauki Hajiya Saratu ta sake samun ‘yarta mace. Tun randa akayi haihuwar nan Ramatu da Wabili basu huta ba. Kullum su suke fama da aikin biki da kuma abincin baki ‘yan zuwa barka.
Amma duk wahalar nan da suke faman yi mata ba godiya sai hantara da zagi da cin mutunci daga wajenta da kuma danginta wadanda basa hassala mata komai sai zaman diban romon mai jego.
Su kuwa bayin Allah hatta abincin da zasu ba wa mazajensu sai dai su koma gida su dan barraraka musu mai dan sauki. Sau daya suka taba daukar abinci don tafiya su mikawa mazajen nasu, kanwar hajiya Saratau ta hadu da Baffa zai kai wa babansa da amininsa.
Irin taratsin da ta rinka yi kai sai ka dauka barawo ta kama ya saci wani abu mai muhimmanci a gidan. Haka ta dinga yi musu tijara ta na fadin sun kwashe abincin ‘yan barka.
Baffa wani irin yaro ne da baya Magana amma fa akwai rashin mantuwa. Duk da dai bai fi shekaru takwas ba a wan nan lokaci amma tas hoton abin da ya faru ya dasu a ransa.
Haka sukayi ta lallabawa har washe garin suna wanda a nan suka yini cur kuma suka kwana, saboda matar gidan ta saka su aikin masa kwano ashirin da tuwo kwano goma. Taushen abincin ma sai da suka bare mata kabewa kwallo goma.
Wabili duk da ba hidimar danginta bace amma bata kyale Ramatu ta yi aikin nan ita kadai ba. Ga wani Karin takaici sune gyaran kayan miya da su dafa markade da soya shi. In nama aka kawo su zasu wanke su silalashi.
Amma da anzo suya sai kannen hajiya Saratu su dira akai . saboda haka su aiki mai wahala ne nasu amma da suyar na lasawa ta zo sai a karbe daga hannunsu.
Ranar suna baby taci suna kanwar kakarta ta wajen uwa mai suna Safiya sai akayi mata lakani da Iman. Mai jego tana ta canjin kaya ita da ‘yan uwant ana ta dauke dauken hotuna, amma Wabili da Ramatu suna can kicin din bayan gida suna faman aikin naman suna wanda aka yanka raguna biyu da sa guda daya. Shi ma kuwa yana fara kanshi dangin mai jego suka amshe aka hada su da wanke wanke da shara inda ‘yan suna suka bata.
Ko cikin da ke jikin Ramatu basa tausaya wa. Tun jiya da safe su ka bar gidajensu basu suka koma ba, sai washe gari bayan sallar isha. Da zasu tafi hajiya Saratu ta basu turmin irin Allah ya isa tallana din nan wai shine ladar wahalar da suka dauke kwana da kwanaki suna yi mata.
Allah ya sani daga su har mazan su ba don abin duniya su ke yi musu hidima ba, sai don kwadayin ladan zumuncin Allah. Sabanin iyalan gidan honourable da ko yaya suka rabe su sai su dinga ganin kamar kwadayin abin hannunsu ne ya ke kawo su jikinsu.
Comments
Post a Comment