☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER TWO ☘️☘️☘️☘️☘️
*NA*
*HANNE ADO ABDULAHI*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09
CHAPTER TWO
Zaune take a tsakar gida tana kishingide tana shan iska. Hannunta dauke da littafin iziyya tana bitar karatun da aka basu na islamiyyar matan aure da take zuwa a nan unguwarsu.
Tana jin sallamar ta fadada fara’ar ta saboda ta dauki muryar mai sallamar.
“ Yaya Ramatu ina ta sauri in shigo in miki shara da wanke wanke, amma ga dukkan alamu yau kin riga ni”.
Ta tashi daga kishingidar da tayi ta gyara zamanta da kyau, sanna tace “kar ki damu Wabili. Yau ai jikin nawa da sauki. Kuma Mallam ma kafin ya fita sai da ya share min ko ina. Ni kuma yau da naji jikin nawa da sauki sai na karasa wanke wanke”.
“Kash amma dai Yaya da kin kyale na shigo na gyara komai da kaina”.
“Haba abin kullum. In bai cin ma ke mai kokari ce yau she. Hada aikin gida biyu ai ba karamin abu bane”. Ramatu ta fada tana mai gyara kishingidar da tayi ta zauna da kyau.
“kaji Yaya dai da wani irin zance. Aiki kam ai babu. Ke dai Allah ya baki lafiya”, inji Wabili.
Ramatu ta nisa, sannan tace “ai ni wannan laulayi ban taba irin sa ba. Domin ko barin dana yi sau uku babu wanda ya bani wahalar da nake fama da ita yanzu”.
“To ko dai sanadin barin da kika yi yiyyi ne yasa kike samun matsala yanzu”?
“Anya kuwa. Kin san kwanaki can da Alhaji mai Rabo ya raba zakka ya bawa Mallam, haka ya dunkule ta ya kaini can babban asibiti aka dubani. Kuma sun ce ba komai laulayin ne kawai ya saka ni a gaba”.
Wabili tace “to Allah ya baki lafiya. Ni kuwa idan na ganki da cikin nan ji nake uwa in cire shi daga jikinki in mayar nawa”.
Ta dafa ta sannan tace “da iznin Allah kema zaki samu naki. Kuma wannan din ma ai ke zan haifawa”.
Wabili tace “Kwarai na sani ni zaki haifawa. Daurewa zaki yi ki samo ‘yan biyu. Ni daya ke daya. Ko da yake ko haka aka yi, na zarta ki da guda daya tun da ni ina da Baffa”.
“Ai kuwa lalle kam kina da Baffa. Wanna din ma kar ki damu ko guda nawa ne zan bar miki su gaba daya. Kuma in sha Allahu kafin ki yaye su kin samo musu kani ko kanwa”.
“Amin Allah. Ni bani na damu da haihuwar nan ba. Tausayin Mallam nake ji, yadda ya damu. Rannan har cewa yayi ko dai ya sallameni in je in auri wani ko na samu rabona.
A nan ne ma nayi masa jan ido nace idan dai ya gaji da zama da ni ne ya gaya min. amma ya sani ko sallamata yayi ba in da zani tun da dai yaya na ne shi sai ya rike ni idan ya haska ya ga mai haihuwar sai ya aura min shi. Tun da shi yana da madubin gane wanda yake.
haihuwa da wanda ba ya yin ta.
To ganin raina ya baci shi ya sanya ya daina maganar”.
Ramatu ta kama baki sanan cikin mamaki tace “lallai Wabili Hausa ta nuna a bakinki. Kuma ki daina ganin laifinsa. Ba zaki gane irin bakin cikin da Haule ta dasa masa akan maganar rashin haihuwar nan ba. Zagi da gori ba irin wanda bai sha shi a wajenta ba. Ina ga shine dalilin da yasa baya son ya takura miki. Ganin kin dan kwana biyu sai yake ganin kamar matsalar daga wajen sa ne”.
“Matsala kam babu sam. Kuma ni Alhamdu Lillahi. Ko ban Haifa ba ai kin Haifa min ga kuma wani ko wata zaki kara Haifa min. Kullum addu,ar da nake musu ke nan Allah ya yi musu albarka”.
Irin wannan zama mai dadi shi ke wanzuwa tsakanin makotan guda biyu. Yadda Allah ya hada kawunan mazansu, suma haka matan suke kokarin zama na mutunci da junansu.
Ba su da sa ido a harkar juna balle kyashi da hassada su samu matsugunni. Duk da ba wata wadata ce da su ba, amma Allah ya saukar musu da wadatar zuci da kuma gamsuwa tare da yaba kokarin mazajensu.
Ba irin haka Ramatu ta zauna da Haule ba, watau matar Mallam Jibrin ta farko. Da farko ta so ta jata a jiki. Ta kuma yi iyakar kokarinta ta koya wa Ramatu mugayen halayenta.
Sai aka samu akasi. Ita Ramatu mai kiyaye hakkokin mijinta ce. Sabanin Haule da duk dokar da ya kamata ta kiyaye kamar ce mata ake je ki ki karya doka kaza.
Da taga ta kasa jan ra,ayinta, sai kuma tsangwama da tsana ya biyo baya. Sa’arta daya zamanta a gidan aurenta bai cika yawaita ba saboda da ita ta iya karauka gidajen masu kudin unguwarsu.
Wulakanci da nuna mata ba ta kai din da suke yiba bai dameta ba. Ita dai burinta a ce tana hulda da masu kudi. Har lakani ake mata a unguwar da ‘yar uwar masu kudi. Kullum lissafin labarinta baya wuce wane kaza shine kakana, alkalinmu kanin tsoho na.
Haka yaran mata zasuyi ta zolayarta suna dibanta tana shirga musu karya.
Ga shegen cin bashi da shiga rigimar cinki. Wadan nan halaye nata su suka saka duk da hakurin Mallam Jibrin ya hakura ya sawwake mata.
Bayan nan ne kuma ya auri cousin dinsa. In da ita kuma hali ya saba matuka saboda duk wasu munana halayen tsohuwar matars ita Wabili bata da su. Ga kuma hade kansu da sukayi da matar amininsa
Allah yabada saa yakara basira
ReplyDelete