☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER TWELVE ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER TWELVE

 Shekarar da Baffa ya gama degree. A wan nan shekara ne kuma ‘yan biyu Gwaggo suka shiga JSS 3, yayin da autar mata watau Hamida, da kuma Walid autan Gwaggo ke take musu baya.

 In ba wanda ya san asalin tarihin su ba, ba wanda zai ce dukkaninsu ba ‘ya’yan mutum daya ba ne. Duk abin da Gwaggo za ta saya komai girmansa ko kuma kankantarsa guda uku zata saya. Idan kuwa ba ta da sukunin sayen uku sai dai kowa ya hakura.

 Kuma duk abin da ta saya sai Humaira da Zahra sun zaba san nan a bawa Hamida. Saboda a cewarta ita ce karama.

 Dai dai misali, Allah ya rufa musu asiri. ‘Yar cima da sutura dai dai ta dan talaka su na da shi. Day scince ta unguwa uku da gwamnati ta bude, nan suke zuwa. Sai kuma islamiyyar masallacin Faruk da suke halarta.

 Ba za ace sun kai Baffa kwakwalwa ba, amma suma sune jagororin ajujuwansu. Hamida dagewar ta ce ta sa ta zama mai kwazo. Saboda duk da tayi hankalin fahimtar Ya Baffa wayo ya yi mata ba dawowa zai yi  ya tafi da ita ba. Amma duk da haka tun da ya bata umarnin ta yi karatu, to kuwa umarninsa ta ke bi.

 Ta daina fada da kowa saboda Ya Baffa ya hana ta yiwa na gaba da ita rashin kunya. Duk da baya ganinta, amma duk wata doka da ya gindaya mata, ta kiyayeta.

 A unguwa Wabili ta samu labarin auren Amira, babbar ‘yar Honourable. Yaron sa’an Amir ne yayanta, kuma mahaifiyarsa Hajiya Hadiza kawar Hajiya Saratu ce matar Honourable. Sai dai fa tarbiyyar da suka yi wa ‘ya’yansu ba iri daya bace. Shi Faruk Abubakar Sani natsattsen yaro ne. Ya kammala karatunsa a oil and gas. Kuma har masters gare shi a wan nan fannin.

 Zamansu a England ya dasa shakuwa a tsakaninsu. Shi ya dinga kula da lamuran Amira, saboda ganin yayyunta guda biyu duk babu na zabe. Sa idonsa a kan ta kamar yadda wa zai yiwa kanwarsa ne.

 Tana shekara ta biyu da fara degree dinta,ya gama masters dinsa ya dawo. Kuma da first class ya fita. Yana gama bautar kasa kuwa kamfanin SLUMBERGER suka dauke shi aiki suka tura shi reshen su da ke Warri.

 Amir da Saddam kuwa sai dai neman sauki. Shi dai Saddam ya kukkula ya samo wata diploma a wata makaranta da hukumar kasar nan bata yarda da ingancin ta ba. Shi kuwa Amir yadda yaje haka ya dawo, sai dabi’un banza da ya koyo.

 Tare da Faruk aka kai su makaranta. Komai nasu daya, amma daya ga tafiyarsu ba zata zo daya ba, sai yaja jikinsa. Ya sanar da mahaifiyarsa tabargazar da su Amir suke yi, ta dan yi wa Mommy shagube akan ta sa ido a kan lamarin yaranta. Amsar da ta bata, ita ta sanya ta zuba matai do.

 Mommy na budar baki tace wa da umman Faruk watau Hajiya Hadiza “ki kyale masu kawo miki labarin karya a kan yaranki. Ki yadda da su a duk inda suke. Mutane hassada garesu. Daga an ga ka samu daukakar da za ka tura yaron ka karatu sai a dinga nuna maka zuwa karatu waje lalata yara yake yi”.

 Jin haka yasa Umman Faruk ta dauke ido akan lamarinta. Haka shima Faruk tun yana tabukawa ya dan yi musu nasiha har ya hakura ya daina. Ga su da kashe kudi kamar masifa.

 Haka kawai ana zaune sai su buga waya suce da iyayen suna bukatar kudi. Take kuwa za a tura musu ba bincike ba komai.

 Wani abu da Amir ya taba yi ya daure masa kai. Suna zaune a cafeteria makaranta suna cin abinci, sai wani abokinsu mai suna Sadi yace “na rasa yadda zan yi da old man din nan. Duk sanda ka ke neman kudin sai ya yi drilling dinka. Wanda aka sa a dok din kotu ma ya fika ‘yanci”.

 Duk su ka sa ka dariya. Amir yana budar baki yace “ni kuwa bani da wan nan problem din. Bari ma ku ga yadda ake yi”.

 Take ya danna wayarsa ya kira babansa. Bayn sun dan gaisa ya ce “Emh Daddy dama wani kudi ne za a biya na wasu courses guda biyu face book da twitter. Kuma ance idan bamu biya ba, ba za a barmu mu rubuta jarrabawa ba”.

 Take kuwa Honourable ya tambaya nawa ne, ya amsa masa da cewar kowanne dala dari biyar ne. Suna nan zaune kuwa alert na dala dubu ya shigo masa..

 Cike da mamaki Faruk ya ce “wai kana nufi Daddy bai san twitter da face book ba”?

 “Kai manta da shi. In ban da musun siyasa ba abin da ya sani. Da dai yadda za a hayo butocin campaign ne ya iya ko kuma yadda za a murde zabe. Amma da ga nan basirarsa ta kare”.

 “Meye kuma butar zabe”? Faruk ya tambaya.

 Dariya saddam ya saka. San nan yace “ai in ka ji dan siyasa yana cewa a debo buta mota goma, to ya na nufin a debo wadan da za a bawa kwaya su sha su hargitsa waje idan zabe bai favouring din su ba”.

 Shi kam Faruk ganin akidarsu ba daya ba ya sa ya ja jiki daga garesu. Saboda shi tsabar biyayya, kudin shekara ake saka masa a account dinsa, amma ko fatara zata kashe shi ba zai taba daukan sama da abin da iyayensa suka kayyade masa ya kashe ko wane wata ba.

 Haka zalika akwai lokuta da yawa da iyayen zasu bukaci kara masa kudin, amma shi da kansa zai nuna musu ba ya bukatar kudin. Saboda shi mahaifiyarsa a gabanta ‘ya’yanta suke daukar karatu addini. Kullum kuma suka gama karatu sai ta nanata ‘FA INLAM TAKUN TARAHU FA INNAHU YARAKA’.  Watau idan ka kasance baka ganinsa to shi ya na ganinka. Saboda haka su ka  tashi da tsoron Allah yana ganinsu a duk inda suke. Hakan ya basu damar yiwa yaransu tarbiya irin wacce addini yake so kowanne dan kwarai ya samu.

 To wan nan bawan Allah Nagartaccen mutum shi Amira ta samu sa’ar aura.

 Tana dawowa kuwa wanda kafin lokacin sun dai daita kansu aka saka bikinsu. Ita da kanta ta taka har gidan Mallam Jibo ta kai musu goro da katin bikin ta.

 Wabili da Mallam Jibo sun dauka iyayen ne suka turota. Haka kuwa suka dau kwalliyarsu dai dai su. Tun da suka je wajen bikin nan kuwa, suke famar wanke wanke da share share.

 Dama ga ‘ya’yan nata da kwazo kamar ita. Da sunga wuri ya baci zasu taya Gwaggonsu su gyara. Aikuwa ko bayan biki, sai Mommy ta mai da su bayinta. Duk san da za ta zo gari zata ba wa mai gadi sakon lallai ya sanarwa Humaira da Zahra su zo su gyara mata gida.

 Wabili ta so ta ki wan nan amma sai Mallam Jibo ya nusasshe ta da cewar Mommy ta fi su iko da ‘ya’yan Mallam Musa.

 A fusace tace “amma saboda Allah Mallam haka zamu zuba mata ido ta mayar da yara kamar bayi”?

 “Na fahimci bacin ranki. Nawa yafi naki baci. Amma abin da ya sa nake lallabasu, idan suka bukaci karbar yaran nan bamu da hurumin hana su. Tun da yanzu sun ga yaran sun isa moro. To kuma kin san tabbas suka karbe su, sai abin yafi haka muni”.

 A haka ta hakura da hawan kawarar da hajiya Saratu take yi musu ita da yaranta.

 Suna cikin haka Baffa ya kammala masters dinsa. Suna ta murnar ya kusa dawowa, sai yake sanar da su, saboda sakamakon da ya samu a jarrabawarsa an dada ba shi damar yin degree na uku.

 Sun yi murna da daukakar da yake samu, amma fa kewarsa tana damunsu. Musaman ma Hamida da ranar da ta ji labarin ba zai dawo ba kwana tayi ta na kuka. Da yayi waya ma kin karba tayi. Sai da kyar ya samu ya rarrashe ta.

 Babban kamfani kera jiragen kasar Japan masu aiki da lantarki watau electric trains, mai suna Hitachi Train, su suka dauke shi aiki a matsayin daya daga cikin masu kera jiragen. A lokaci guda yana ci gaba da karatun nasa.

 Hutun da Amira ta zo daga Warri, shi ya hargitsa rayuwar gidan Mallam Jibo. A wan nan lokaci Amira ta haihu ‘yan biyu mace da namiji. Khadija da ake kira da Amal sai kuma Abubakar da suke kiransa da Sadik, watau sunan mahaifiya da kuma mahaifin mijinta.

 Complain take yiwa Mommy na matsalar mai aiki. Take kuwa Mommy ta ce mata “ga kanwarki nan. Dauke ta ki tafi da ita. Dama wan nan karatun nasu na sha kurarka ba wani abin kirki suke yi ba. Dauketa kawai ku tafi ki huta larurar jagaltun masu aiki”.

 Mallam Jibo bai samu arzikin a kira shi a yi masa bayani ba. Mai gadi kawai aka turo akan Mommy tana neman Humaira da Zahra. Sun shiga gidan suka ci karo da Honourable ya rako wani bakonsa wanda ya kasance senator ne.

 Honourable na masa zance shi kuwa hankalinsa yana kan kyawawan ‘yan mata guda biyu.  Su ka durkusa suka gaishesu. Muryar Humaira yaji wanda ta saka shi a cikin shauki.

 Shi kuwa suna kokarin gaishe shi sai muzurai yake yi musu. Sai da suka shiga cikin   gidan san nan ya dauke idon da ya raka su da shi.

 Ganin yana kokarin rasa natsuwara ya sa yayi sallama da Honourable ya shiga motarsa.

Comments

Popular Posts