☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER TEN ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER TEN

 Baffa da sauran dalibai basu samu isa Tokyo babban birnin Japan ba, sai da suka kwana hudu tsakanin iska da tasoshin jiragen sama. Sun ga duniya sabuwa. Sun kuwa sha kallo. Don ma Allah ya hada su da jagora mai kirki. Saboda duk inda suka tsaya, zai basu dama su tambayi abin da suke son sani ya kuma kara musu da bayanin abin da ba su ma tambaya ba.

 Haka zalika ya kan kyale su, su sha kallo su more ba tare da azalzalarsu ba. Sai dai idan ya ga zasu makara wajen komawa cikin jirgi.

 Daga kano Lagos suka fara zuwa. Daga nan suka hau wani jirgin zuwa England. Shi Baffa ya taba zuwa Lagos, amma wan nan yankin da suka je bai san da shi ba.

 To fa tu anan aka fara kauyanci. Kwarewar jagoran nasu a harakar mu’amala da jama’a ita ta saka ya sanya su suka saki jiki da shi.

 A Heathrow Airport na birnin London suka sauka. Sun yi zaman kimanin awa goma sha uku kafin suka hau wani jirgin zuwa Narita International airport a babban birnin Japan, watau Tokyo.

 To a nan nema kauyancin ya dada bayyana, saboda kallo wuyansu kamar zai tsinke. Sun tarar da motocin embassy Nigeria sun zo tarar  su. Sai kuma ga hukumar makarantar da za su je ita ma ta tura wakilanta.

 Nan dai aka gama ciken ciken takardu, san nan aka mika su ga hukumar makaranta. Amma duk da haka jagoransu bai rabu da su ba, saboda umarnin da mai girma Gwaamna ya ba shi na ya tabbatar ya kai su har cikin makaranta.

 Tokyo University (Todai). Itace makarantar da tafi kowacce kyau a kasar. Haka nan kashi saba’in bisa dari na darussan ta da harshen turanci ake koyar da su. San nan ko dalibai sai sun samu zakakurai suke dauka.

 A makarantar ma sai da ya tabbatar komai nasu kamar su registration da ba da dakuna ya kammala. San nan kowanne dalibi ya gane bangaren da zai yi karatu.

 Baya nan ya debe su suka je shago suka sayi sutura dai dai misali wadda zata dace da yanayin kasar na tsananin sanyi da ake ciki.

 Haka nan ya kai su bankin da ke cikin makarantar ya taimaka musu suka bude account, ya zubawa kowanne dalibai allowance din shi, saboda kudin makaranta tun kafin su iso kasar aka gama da wan nan babin.

 Saboda sanin kusan dukkaninsu ‘ya’yan talakawa ne sai da ya dauki lokaci yana koyar da su abubuwa kamar yadda za su yi amfani da ATM da bus ko taxi na kasar.

 Kai hatta toilet sai da ya nuna musu, saboda ba abin da suka gani wanda yayi kama ma da wanda suke gani ko da a finafinai ne a gida Nigeria.

 Akwai wani yaro mai dan barkwanci a cikinsu, idan ya kalli abu ya birgeshi sai yace “Ya Allah, ko ya aljanna take”?

 Wani shima ya sake cewa “ni a aljannar idan na samu haka ma ya isheni”.

 Bayan nan ya yi musu rijista ta koyon harshen kasar, saboda da duk wanda ya san Japanese ya san su mutane ne wadanda suke martaba yarensu da kuma al’adunsu.

 Akwai course da za suyi wanda zai dauke su sati shida zuwa sati goma. Ya danganta da kwazon dalibi. Course din shi zai taimaka musu wajen fahimtar yaren kasar.

 Kafin jagoransu ya tafi ya hada su ya yi musu nasiha da jan kunne sosai da su kiyaye dokokin kasar da kuma na makarantar. Ya nuna musu su irin wadan nan kasashe ba a karya musu doka ko da kuwa ta tofar da yawu ce a kan titi.

 San nan ya ja kunnensu da su rike addininsu, su kuma fuskanci abin da ya kawo su watau karatu. Su kuma hade kansu saboda ba su da kowa sai junansu. Ya ba su lambar embassy Nigeria na kasar akan idan suna da matsala su neme su.

 Su Baffa dai ba wanda ya samu labarinsu sai bayan sati biyu da tafiyarsu, saboda sai a lokacin suka samu natsuwa, san nan kowa ya kira gidansu.

 Murna a wajen Mallam Jibo ba za ta fadu ba. Ga shi dai lokacin da ya kira tsakar dare ne saboda banbanci lokaci wanda ita Tokyo tana gaban Kano da awa takwas.

 A wan nan lokaci da ya kira karfe hudu ne na asuba. Sai da yaji ya na fadin “bari in taso Gwaggon ku”, san nan ya tuna ashe akwai banbanci lokaci.

 “Abba karfe nawa yanzu”? Baffa ya tambayeshi.

 “karfe hudu ne yanzu na dare. Asuba ta ma kusa. Ba agogo a hannunka ne”?

 “Abba akwai sai dai lokacin ba iri daya bane. Saboda a nan yanzu haka karfe shabiyu na rana. Har mun wayi gari”.

 “Ikon Allah. Kaji wata hikima ta Ubangiji. Duniya daya kowa da lokacinsa. Sai yanzu na dada yarda da ka ke gaya min duniya na juyawa. Ashe idan mu ta kaimu wajen dare sai ta kai wani bangaren wajen rana”.

 “Hakane Abba. Abba ina Hamida”.

 “Gata nan. Ai tun da na shiga tashin Gwaggon ku. Tana jin na kira sunanka ta mike kamar da ma ba bacci take ba”.

 “Abba don Allah ba ta wayar”.

 Ya na mika mata ta kasa maganaa sai kuka. Tana jin su Humaira na mata masifar idan ita ba zata yi magana ba, su ta basu wayar. Gwaggon ce ta karbe wayar tana fadin “sakarya. Ki yi magana kinki sai kukan banza kike yi wa mutane. Kin barshi yana ta asarar kudi”.

 Sai bayan ya gaisa da Gwaggon ita ma ta dora da nata tambayoyin yana amsa mata. Amma fa hankalinsa yana kan shesshekar kukan Hamida da yake jiyowa.

 “Gwaggo ba wa Hamida wayar”.

 Maimakon ta ba ta kamar yadda ya nema sai ta mikawa su Humaira. Su kam bayan sun gaisa jan kunne ya dinga yi musu a kan su kiyaye batawa Hamida rai. In ba hakaba idan zai dawo ba zai musu tsaraba ba.

 Hatta Walid sai da ya gaisa da shi san nan suka mika wa Hamida wayar. Ta na jin muryarsa sai wani kukan ya sake balle mata.

 Gwaggo kuwa sai dada fadi ta ke  yi “idan ba zakiyi Magana ba ki kashe kina masa asarar kudi. Gashi ance kira dagga Saudiyya ma tsada gareshi bare wan nan kasar da ance a bangon duniya take”.

 “Fita daga dakin”, shine umarnin da Baffa ya bata. Ba tare kuwa da tace da kowa komai ba ta fice da wayar a hannunta.

 “kin fita”?

 Daga masa kai tayi kamar yana ganinta. Amma har a lokacin ta kasa furta ko kalma daya.

 Shesshekar kukan nata ita ta dada daga masa hankali. Ga shi dai a lokacin bata haura shekara takwas ba amma kuka take yi kamar wata babba. Shi ma daga nasa bangaren sai yaji kamar zai yi hawaye.

 Shi ya daure yace “Hamidan Baffa, kukan me ki ke yi”?

 Ba ta ba shi amsa ba sai wani kukan da ya kubuce mata.

 “Hey! Hey! Come on kiyi shiru haka ya isa. Ba kya so in yi karatu mai kyau idan nadawo in samu aiki mai kyau. In gina mana katon gida. In sayawa Abba mota. In kai su Makka shi da Gwaggo”?

 Cikin muryar kuka tace “Ina so. Amma mai yasa ka gudu ka bar ni”?

 “Ki yi hakuri Hamida. Tafiyar ce ta zo a haka. Amma idan ba kya so in ginawa Abba gida mai kyau sai in dawo”.

 “Mhm Mhm. Kar ka dawo. Kokuma ka zo ka dauke ni, mu tafi tare”.

 “Yawwa Hamida haka nake son ji. Yanzu abin da za ayi. Ki dage da karatu a makarnta ki zama mai kokari sosai. Idan kin ci jarrabawa sai in zo in dauke ki kema kiyi karatu mai kyau a nan”.

 Nan da nan kuwa ta washe ta fara dariyar murna. Nan dai ya ci gaba da rarrshinta. Da ta yi korafin Gwaggo na dukanta, nan ma ya ce da ita ta daina yiwa Gwaggon rashin ji. Duk abin da aka saka ta tayi da kyau. Ta kuma daina wasa ta dinga karatu sosai, saboda ta dawo wajensa.

 Sai da katinsa ya kare san nan ya hakura.  Daga ranar kuwa kowa ya ga canji a rayuwar Hamida. Don ko Walid ne ya aiketa zuwa zata yi saboda Baffa ya ce ta dinga yin duk abin da aka sakata.

 Karatu kuwa kamar ana jona mata caji, ba bokon ba, ba Arabi ba saboda dokar da Baffa ya bata ke nan. Ita ko ba ya nan ya kafa mata doka, haka za ta bi dokar.

 Wata irin shakuwa ce a tsakaninsu. Yadda ya damu da lamuranta, haka ta damu da na sa. Dan kudin break kuwa da ake bata ta daina sayen komai saboda so ta ke ta tara ta sai kati, saboda Abba ya gaya mata cewa kira can kasar ya na da tsada.

 Bayan kiran farko, ya sake kiransu bayan sati biyu. A nan ne Abba ya ce masa kar ya sake kiransu, idan sun samu sukuni su zasu kira shi. Jin haka shine ita kuma take tara kudi domin ta samu isassu ta sai kati ta dinga kiransa.

Comments

Popular Posts