☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER SIX ☘️☘️☘️☘️☘️
*NA*
*HANNE ADO ABDULAHI*
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/
CHAPTER SIX
Sai bayan sati biyu Mallam Jibo ya hakura da alhinin da yake ciki ya koma sana’ar sa. Ko banza yanzu nauyi ya karu a kansa. Honourable dai tun da akai kaninsa kabari bai sake ganinsa ba. Matarsa ma sai mai aikinta ta turo tayi musu gaisuwa a dalilin wai tana jego ba ta iya fita. Amma tana iya zuwa saloon da super market.
Ramatu kuwa sai dai godiyar Allah. Amma duk wanda ya kalleta ya san tana cikin tashin hankali. Sai Wabili tayi da gaske take karbar abinci. Ga kuma Mallam Jibo da kokari. A dan karamin karfinsa haka zai ganganda ya dan samo mata abin kwadayi.
Amma duk da haka sai a hankali. Haka kullum suke kashe lokaci shi da matarsa wajen rarrashi da ban baki. Ganin tana yawan saka su damuwa ya sanya ta fara kokarin danne abin da ke zuciyarta.
Watan Mallam Musa biyu da kwana hudu da mutuwa, Ramatu ta tashi da nakuda. Bata sanar da kowa ba ta yi kwanciyar ta a dakin da take zama. Wabili ta leko sun gaisa bayan na ta fita domin kaye Kayenta.
Kukan jariri ne ya fargar da ita daga wankin da take yi a tsakar gida. Hankide bokitin tayi ta yi cikin dakin aguje. Ita ba haihuwa ta taba yi ba saboda haka ba ta san abin da zata yi ba.
A firgice ta ke duk ta rude. Ramatu tayi mata Magana wacce da ga jin muryarta ka san a gajiye take. Ta ce da ita “dawo kar ki tsorata. Samo zare ki nada min shi da dan dama sai ki bani reza in yanke musu cibiya”. Hannunta na karkarwa ta dauko sabuwar reza a kwandon kayan kwalliyarta. Ramatu da kanta ta nuna mata inda zata daure, sai a san nan suka lura ashe ‘yan mata biyu ta Haifa. San nan ta yunkura ta yanke cibiyar ta mika mata su tana fadin “ga su nan na baki duka. Dama na gaya miki cikin jikina ke na daukarwa”.
Ita duk murna ta hana ta gane mawuyacin halin da Ramatu ke ciki. Da kanta ta leka mallam Jibo ya tula uban wanki yana tayi ta masa albishir da haihuwar da aka yi. Shi ma da saurinsa ya bar abin da yake yi.
Da ganinta ka san ta galabaita. Mallam jibo ya ruga da hanzari gidan Honourable domin sanar da shi haihuwar matar kaninsa. Amma yayi jira ya kai na minti talatin ba Honourable duk da sakon gaggawar da ya tura mai gadi ya fada ma sa.
Ganin lokaci na tafiya ya hakura ya dada bar wa Maigadi sakon ya sanar da shi ya tafi kai maijegon asibiti.
Da kafarta ta shiga taxin da aka dauko domin su tafi asibiti. Ita kuwa wabili sai santin fararen jariran take yi. Su biyu suka tafi asibitin akan shi zai koma gidan Honourable ya fada masa halin da ya dawo ya sameta a ciki sai ya same su a asibitin.
Da ya koma din ma bai samu ganin sa ba saboda mai gadi yace a wan nan lokacin lokacin baccinsa ne kuma ba a tashinsa. Sallahu ya dada bashi akan ya sanar masa haihuwar matar kaninsa da kuma mawuyacin halin da ta ke ciki.
Tashin hankali bai barshi ya ga Baffa dake biye da shi lokacin da ya ke safa da marwa tsakanin gidansu da na Honourable ba. Sai da ya tare mashin san nan ya farga dashi.
“Hawo mu tafi Baffa”, abin da ya iya ce masa ke nan. Su na isa asibiti ya dada tarar da wani tashin hanakali saboda galabaitar da Rahma tayi
Wai a sunan emergency suka je, amma sun fi awa uku suna layin ganin likita. Sai da layi ya zo kansu aka ce ba za akarbe su ba saboda ba a nan take awo ba. Su ma tsaya su saurari bayanin su na yadda haihuwar tazo bagatatan. Amma sam sun ki saurarensu. Sai ma umarnin da ma’aikacin ya bayar na security su fitar da su.
Har kasa mallam Jibo ya tsugunna ya na rokonsu da su duba matar nan amma fir suka ki. Ba wanda ya Ankara sai kawai jin faduwar Ramatu suka yi daga kan bencin da suke. Take kuwa jini ya tsinke mata.
Kafin ayi yunkuri kawo gado a dauke ta ita ma kamar mijinta ta ja Kalmar shahada ta rasu. Ba a duba ta tana raye ba, sai da ta mutu aka fara laluben dalilin mutuwarta. Sakamako ya nuna jininta ya yi mugun hawa har zuciyarta ta buga.
Sai a san nan likita ya fara tambayar su dalilin da ya sa ta samu ciwon zuciya. Mallam Jibo na kuka ya ke labarta masa cewar tun da mijinta ya rasu ya lura ta rage Magana da walwala, amma ya dauka ko alhinin mutuwa ne ke dawainiya da ita.
To ashe tun a lokacin mutuwar mallam Musa ta samu wan nan larurar. Ita kadai ta san me take ji a jikinta, amma sanin rashin wadatar da mai kula da su yake ciki ya sa ta yi gum da bakinta.
Ta kan kwana uku bata rintsa ba amma ba ta taba sanar wa da Wabili ba.
Tsakanin Wabili da mallam Jibo an rasa mai bawa wani baki. Wabili sai sambatu take ta na fadin “da ma adda da kika ce ni zaki haifewa wan nan cikin, ashe tafiya zaki yi ki barni”.
Haka suka dawo gida da jarirai guda biyu da kuma gawar mahaifiyarsu.
Baffa duk yana kallonsu yana kuma sauraren abin da ke faruwa. Mallam Jibo bai gaji ba ya sake komawa gidan honourable domin sanar da shi abin da ya faru.
A nan dai yai sa’ar samunsa saboda ya fito raka wasu baki a farfajiyar gidan suka hadu. Yana bata rai da cin magani ya gaisa da shi. A tunaninsa ko wani nauyin yazo ya dora masa na iyalin da kaninsa ya mutu ya bari, saboda fitowarsa maigadi ke sanar da shi zuwan Mallam Jibon sau biyu.
A wulakance ya amsa masa gaisuwar da yake masa yana fadin “ai na samu sakon ka wajen maigadi. Ka san garin yayi zafi nima ba wani kudi ne da ni ba, amma ga wan nan” ya fada yana mai mika masa dubu biyu.
“A’a Alhaji ai komai ya wuce ta haihu ta samu ‘yan tagwaye duka mata”.
“ah to madalla. Allah ya raya. Dama haihuwa ce kake ta wan nan uban sako. Shi ke nan kaje zan zo”.
Sai da ya matse kwallar da ta zubo masa san nan yace “ai komai ma ya kare. Sai dai muce Allah ya karbi shahadarta. Domin Allah yayi mata rasuwa”.
“Allahu Akbar. Allah yaji kanta”.
Bai koma gida ba ya bishi suka koma. Tare da shi akayi mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya. Daga makabarta kuwa gida ya wuce da sunan shi baya son taron zaman makoki.
Ita kuwa Hajiyarsa bata samu zuwa ba sai da daddare ta leko ta gai she su. Ta dan dauki yaran. Itama bata wani dade ba ta yi tafiyarta.
Ba wanda ya sake leko su daga gidan Honourable har aka kwana uku. Ganin haka ya sanya washe gari jairirai na da kwana hudu Mallam Jibo ya sake zuwa neman iznin wan babansu domin yayi musu huduba.
Nan ma shakikin wan mahaifinsu bai nemi yayi hudubar da kansa ba amma ya ba da umarnin Mallam Jibo ya yi musu. Ya kuma bada umarnin a radawa daya Aishatu sunan uwar matarsa dayar kuma sunan mahaifiyarsa Fadimatu.
Wabili ta koka tayi korafin rashin kirkin Honourable. Amma shi mallam Jibo duk da bai zaci haka daga wajensa ba amma nasa mamakin ragagge ne.
Duk kuma abin da yake faruwa akan idanun Baffa da kuma kunnuwansa suke gudana. Ranar suna kuwa aka rada wa yara sunan da baffansu ya bada umarnin a rada musu.
Ko za a mutu ba ci abinci a gidan Mallam Jibo ba, da ya samu dan kudinsa madara jarirai zai fara saya. Ya kan ce “mu zamu iya hakura mu ci ko meye. Amma su dole sai madara za su iya sha”.
Suna da sati biyu akuyar da Wabili ke kiwo ta haihu. Shi kuma a wan nan rana ya buga ya buga bai samu komai ba, ya dawo gida ya tarar da yara nata kuka madara ta kare. Bai ankara ba sai gani yayi Wabili taje ta tatso nono akuyar nan ta fara basu. Sai a lokacin ya tuna a rugarsu su kan shayar da jarirai nonon akuya.
Yara kuwa da suka samu suka kama kwankwanda har sai da suka koshi. Amma duk da haka bai hakura an ci gaba da basu ba, sai da ya tambayi shawarar wani ma’aikacin asibiti nan kusa da su. Shi kuma ya sanar da shi tama fi ta gwangwanin lafiya.
Ai kuwa suna fara sha in ka gansu kamar ‘ya’yan turawa don kyau. Bul bul da su.
A bangare Baffa karami kuwa ya dage da sallar nafila da kuma azumi wai don yana son ya dinga turawa innarsa da baffansa lada da zai dinga taya su hira a kabari. Sai Abbansa watau mallam Jibo yayi da gaske yake yarda ya ci abinci saboda kullum cikin azumi yake.
Duk wan na ta shin hankali da yake ciki shekarunsa takwas ne kawai, ya zama maraya gaba da baya. Ba shi da gata sai na aminin mahaifinsa.
Ana cikin haka sai kuma wata sabuwa ta bullo daga gidan Honourable. Amir ne mijin kanwar babarsa me suna Gaji yayi kararsa a dai police station din da aka yi karar Mallam Musa.
Wani dan unguwar ne yaje ya sanar da Mallam Jibo. Suk isa station din har da su mai unguwa domin su dorar da labarin da suka ji.
Shi dai mijin Gaji ya yi karar Amir ne kan ya shiga gidansa yayi wa matarsa duka. Aka tamabaye shi dalili dama kuma a mankas din sa yake yace sarka ya bata ta sayar masa sama da wata hudu ba sarka ba bayanin ta.
Uwarsa ta tashi zatayi tashin hankali Gaji ta tona musu asirin tace “sarkar da ki ka kalawa kanin mijinki satarta itace dai wacce danki ya dauko ya kawo min. kuma tun a lokacin na sanar da ke ki ka karbi abarki kika yi mukus.
Ai da sai ki sanar masa da cewar kin karbi abarki. Amma haka kawai yaro yai shaye shayensa ya shiga har gidana ya lakada min uban duka kuma ace ba zan yi kararsa ba”.
Mai unguwa da Malla Jibo sai murna suke yi, saboda wanke matar Mallam musa da Allah yayi duk da hakan yayi sanadin rasuwarsu. Ganin haka ya sa Honourable saka DPO ya kori kowa daga station din suka shiga ciki aka sasanta.
Wan nan abu da ya faru ba karamin kona ran Hajiya Saratu yayi ba. Ta kuwa kullaci Jibo a ran ta, kamar shi ya aika Amir yayi satar. Saboda haka ta dage da zuga Honourable da ya dauke masa wuta tun da da shi ake hada kai a tozarta masa dan sa.
Lokacin da Jibo ya dawo gida yake bawa Wabili labarin abin da ya faru Baffa na gefen tabarma yana home work. Tas ya nade duk abin da ake fada, amma yadda ya basar ya ci gaba da rubutunsa kamar hankalinsa ba a wajensu yake ba.
Ya kuwa yi saving dinsa a memory card na cikin kwakwalwar sa ya hada da na baya duk ya adana.
Comments
Post a Comment