☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER SEVEN ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/


TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09



CHAPTER SEVEN

   A wan nan rana da misalin karfe biyar na yamma, Wabili ce a dan tsakar gidanta tana ta daddaga ‘yan rigunan yara na gwanjo, sai murna take yi kamar kyauta aka bata, ba saya tayi ba.

 Kayan ‘yan dagwas da su masu kyan gaske. A haka Mallam Jibo ya shigo ya tarar da ita.

 “Maman biyu ashe kin dawo”?

 “na dawo Mallam kuma kasuwa tayi kyau” ta amsa masa.

 “kalli kayan da na samo musu”, tana fada tana daddaga rigunan domin mijin nata ya gani.

 “Lalle ‘yan biyu za a sha kwalliya. Yanzu duk kyawun kayan nan kayan sanyi ne”?

 “ai kuwa sun yi kyau sosai. Dashin nan da na dauka yayi min albarka gashi har Baffa ma na samo masa kaya seti uku da rigar sanyi guda biyu”.

  “ma sha Allah” ya amsa mata shi ma yana taya ta daddaga kayan. Ina Zahra da Humaira ko bacci suke yi”?

 “Ai suma sun sha kasuwa muna dawowa na basu madara sai barci”.

  Shiru yayi san nan ya nisa yace “Na sake zuwa wajen honourable batun yaran nan amma kamar ko yaushe yace in tsimaye shi”.

 “kai ma Mallam meye amfanin zuwa wajen nasa. Kana gani tun ranar da aka kai Adda makwancinta, bai taba waiwayar yaran da suka rasu suka bari ba. Ka kyale shi akwai gobe”.

  “Na san da haka Wabili. Amma hakkin shari’a nake dubawa ba wai tunanin mu na dan Adam ba. Mu ba jinin yaran nan bane. Yafi mu karfi a kansu. Yanzu kin ga ga jarrabawar da Baffa ya rubuta kuma kina jin ance idan yaci makwarantar gwamnatin tarayya zai tafi. Ta ai kin ga bai kamata in dauki yaro har wani gari ba tare da sanin Baffansa ba”.

 “Ni fa na fahimce ka. Amma shi zuwan da kake yi gani yake kamar wani abu kake nema, ai shi yasa yaki yarda ya ganka”.

 Wan nan ita ce babbar damuwar Mallam Jibo. Shi ba nauyi yake so Honourable ya taya shi dauka ba. Yana dai son ya dinga bashi hakkinsa na shakikin dan uwansu, amma hakan ya gagara.

 Ko sau nawa zai je gidan nan ba zai samu ganinsa ba. Bai san da cewa shi da kansa ya bawa maigadin gidan umarnin in dai Jibo ne yazo kar ya kurkusa ya barshi ya shiga gidan.

  Saboda haka kullum a baya nan yake samun amsar daga wajen maigadi. Yana iya kokarinsa a kan yaran da yanzu haka sun kai wata shida da haihuwa. Ba su san wata uwa ba sai Wabili. Haka zalika Jibo suke wa kallon mahaifinsu. Ballanatana Baffa da shi yana da wayonsa.

 Yaro ne mai kwazo da hazaka. Gashi dai makarantar gwamnati yake zuwa, amma ma sha Allah kansa yana ja matuka.

Ya shiga shekara ta tara headmasater ya sanya shi sunansa cikin daliban da zasu zana jarrabawar Federal.

 Abbbansa kuma ya hakikance in dai kokari ne zai sa a ci to shi kam zai haye in sha Allah. Wannan dalili ya sa yake son sanar da wan mahaifinsa abin da yake ciki amma hakan ya gagara.

 Ya hakura ya barwa Allah lamarin. Su Fatima wacce su kayi wa lakani da Zarah, Aisha kuma suna kiranta da Humaira nada wata goma a lokacin Baffa nada shekara tara jarrabawar su ta Federal ta fito. Kuma Alhamdulillah ya samu nan Kano.

 Yau dai da Jibo yaje gidan Honourable Allah yai masa gam da katar, saboda sun rako wasu bakinsu ke nan shi da hajiya Saratu shi kuma ya na shigowa gidan.

 Kamar sun yi shawara nan da nan annurin fuskarsu ya dauke saboda ganin Mallam Jibo.

Kamar yadda ya saba har kasa ya tsugunna ya gaishe shi. Shi ma kuwa ya amsa da kyar. Ita kuwa hajjaju daga lafiya bata kara tanka masa ba.

 Duk da haka ya daure yace “Allah Raini batun yara ne nazo in maka bayani, saboda shi Baffa bana zai tafi babbar makaranta……”

 “Wacce irin babbar makaranta”? ya katse shi da ga maganar da yake yi. Zai kara kora masa bayani yace kaga “Ni ba zan yi maka karya ba. Ba kuma zan dau abin da yafi karfina ba. Duk wani mai hankali ya san yadda karatu yake a wan nan zamani. Kai da bakayi bokon ba, ba gaka nan kana rayuwa ba.

 Saboda haka shima ka tura shi wajen malamin da kayi karatun a wajensa. Su kuma sauran yara biyun ai ka san rugar dangin uwarsu ka kai su can. Tun da dama kowa ya san in dai mutuwa ce ta ratsa, dangin uwa ke daukar rikon yara.

 Kuma banda haka ma ni yanzu zancen dana ke maka na samu wani aiki a Abuja can zan koma. Ita kuma rayuwar Abuja zafi gareta ba kamar nan ba, saboda haka ba zan iya daukar Karin wasu yara akan nawa ba”.

 Yana gama fadin haka ita ma hajiya Saratu ta fara bayanin “kuma gaskiya ni yara sun yi min yawa bazan kara daukar hidimar wasu in kara akan tawa ba”.

 Basu bashi damar ci gaba da bayani ba sukayi shigewarsu gida suka barshi. Har bayan tafiyarsu ya dan jima a tsugunne yana takaicin halin wan amininsa.

 Haka ya hakura da ya juyo gida. Yana shiga Baffa na dawowa daga makaranta. Yana daga dan soron gidan ya makale yake sauraron abin da wan mahaifinsa yayi wa Abbansu.

 Shi da Abbansa zai gane ma da ya daina zuwa wajen mutumin da yake cewa wai Baffansu ne. Ya raya a ransa yadda baya son su shida kannensa haka shima baya son a dinga alakanta shi da Baffansa. Wan nan shi ne tunanin da ya darsu a zuciyar Baffa.

 Sai da ya bari sun gama tattauna batun Baffansa san nan ya yi sallama ya shiga gidan. Nan kuwa uwar goyonsa ta tare shi da murna tana fadin “sannu da zuwa uban masu gida, yaro dan albarka”.

 Murmushin da ya saba in ta na masa irin wan nan barkwanci yayi. Yana ajiye jakarsa ya shiga dakin guga inda nan yake kwana, ya cire uniform dinsa.

 Shiru tana jira ya fito ya dauki abinci, bata ji duriyarsa ba.

 “wai Baffa ina kake ne. kazo kaci abinci ka shirya zuwa islamiyya”.

 “Gwaggo ina zuwa kayan gugar Abba nake jerawa. Kuma ma yau na dau azumi”.

 “Yanzu da nace kar ka dau azumin nan ashe da safe da na shiga wanke bayi baka karya ba ka gudu”.

  Bai amsa mata, ba sai da ya fito daga dakin tukunna san nan yace “Gwaggo kiyi hakuri so nake in dinga aikawa Inna da Baffa lada kabarinsu shi ya sa nake yawan azumi kar ladan yayi musu kadan su rasa abokin hira”.

 Wata kwallar tausayi ce ta zubo mata. Yana ganin haka yace “Gwaggo ki dai na kuka. Abba yace mu daina kuka mu dinga yi musu addu’a ita za ta same su a kabarinsu”.

“Gaskiyar ka uban manya. Allah yaji kansu. Yanzu zo ka gaya min mai za kayi buda baki da shi in girka maka ka sha ruwa da shi”.

 “Inna ki rage min awara kar ki sayar duka sai in sha da kunun da kike sayarwa. Yanzu in kin gama dama kunun bani in kaiwa Baba mai shayi tun da kin ga teburinsa kusa da filin balla yake yace in dinga ajiyewa yana sayar min, sai in wuce islamiyya”.

 “Allah sarki Baffana. Allah yayi maka albarka. Amma na ga kamar da sauran lokaci shiga makarantar ta ku”.

 “A’a Gwaggo. Ina son inje inyi sharar makarantar islamiyyar, tun da naga Abba ba shi da guga da yawa”.

 Tana dada goge flask din da ta ke kulla kunun tsamiya da na gyada wanda ake fitar mata da shi talla. Kuma da an fita da shi da kyar yake haura awa daya bai kare ba saboda dadinsa da kuma yadda take tsaftace shi.

 Tana yi tana fadin “kasan mallam bai cika son kana kama masa gugar nan ba da wanki. Yaushe kayi karfin da zaka iya aikin karfi irin haka”?

 “Ina da karfi” ya fada yana mai nuna mata sangalalen hannunsa”.

 “Ai kuwa ga karfi nan baja baja”. Ta fada tana masa dariya.

 A haka sukaci gaba da lallaba rayuwarsu. Idan yaga Abbansa ya tula wanki haka zai zage ya dage sai ya taya shi. Duk kokarin sa na san hana shi yaci tura. Abban na wanki shi yana dauraya ko shanya ko dauko ruwa.

 Idan dare yayi ya ga sauran guga balle ma da yake da daddare aka fi kawo wuta haka zai kuke ya na goge masa kayan customers din sa.    Sai idan yaga dare ya yi sosai ya leka ya hana shi. Yaro ne mai kokari da kwazo. Aikin da zai yi ba lalle dan shekaru sha shida yayi shi ba.

 Ba shi da buri irin ya taimakawa marikansa. Honourable sun cire shi daga lissafinsu. Da dan abin da Allah ya hore musu suke daukar dawainiyar yaran da ba nasu ba, ba ma kuma jinisu ba.

 Humaira da Zarah nada wata goma sha hudu  sun yi dumurmur da su gwanin ban sha’awa. Tuni an yaye su daga madarar awaki da suka sha suka rayu. Sai dai saboda Wabili bafullatana ce ba ta rabo da kiwo a dan tsakar gidansu.

 Suma kuma Baffa ne mai kokarin kula mata da dabbobin duk da basu cika haura hudu ba saboda rashin fili. Duk kuwa abin da ta samu na cinikin awara da kuma ribar dabbobin  da kuma kunun da take yi a  jikin Baffa da kannensa yake karewa. Komai ta samu su takewa hidima da su.

 Shi ma kuwa Jibo ya dage da sana’ar sa ta wankau. Kuma Allah ya rufa musu asiri. Dan dai abin hidimar iyali baya gagara.

Comments

Popular Posts