☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER NINE ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER NINE    

 Baffa yana da shekara goma sha shida ya kammala secondary, yayin da su Humaira suke aji uku a primary, shalelensa watau Hamida ta na aji uku. Ranar speech and prize giving daya, hukumar makaranat da kanta ta gayyaci Mallam Jibo. A ka ajiye shi a bangaren manyan baki ba tare da ya san dalilin yin hakan ba.

 Baffa a ka saka yayi bayani a matsayinsa na shugaban dalibai. Kamar ko da yaushe cike da kwarin gwuiwa ya karbi microphone. Bayan yayi sallama da gaisuwa ga manyan baki da iyayen da kuma malamai, san nan ya ci gaba da cewa “yan uwana dalibai ba ri in baku wani labari. Akwai wata bishiya ta gora wacce Chinese suke da ita. Idan aka shuka ta za a yi ta bata ruwa da saka mata taki tsawon shekara amma ko tsiro ba zai fito ba.

 Haka shekara ta biyu. Ta uku ma haka. Ya hudu ma shiru. Ta biyar ma ba komai da zai bulla daga cikin kasa. Amma a shekara ta shida zata fara tsira, amma kafin wata shida da fara tsiro zatayi tsawon kimanin meter shida.

 Da ga nan haka zatayi ta tsawo ana yankan ta ba tare da ta mutu ba tsawon shekaru masu yawan gaske”. Ya yi dan tsai ya kalli sauran dalibai saboda ya tabbatar da su na fahimtar sakon sa.

 San nan ya ci gaba da cewa “’yan uwana dalibai. Inason mu saka kanmu a matsayin wan nan bishiya da iyayen suka dau tsawon lokaci suna hidimta mata ba tare da ta fid da tsiro ba.

 ‘Yan uwana dalibai wan nan ce damar mu ta mu tashi mu yi girma da yado kamar Chinese bamboo tree”.

 Gabadaya hall din aka dau tafi. Mallam Jibo kuwa da bai ji bayanin da Baffa ya ke rattabowa ba, amma sai dariya da farin cikin yake, jin yadda Baffa ya ke tsaro turanci. Duk da bai fahimci abin da ake fada ba, amma tabbas ya san daukaka ce ta zo wa dan nasa ganin irin mazaunin da aka bashi a matsayin sa na mahaifin Baffa.

Da aka zo ba da kyaututtuka ga hazikan dalibai sai da AMA watau Ahmad Musa Ahmad ya karbi sama da dozzin.

 Babban bako ne ya tambayeshi me yake son karantawa a university ya amsa da yana son karanta MECHATRONICS. Ya sake tambayarsa dalilin da ya sa yake son wan nan course din.

 Yace “duniya yanzu tana tafiya ne da injinnan da kirkira ta zamani ta zo da su, wadanda suke aiki ninkin ba ninkin din da dan Adam zai yi da karfinsa. Mu da muke ‘ya’yan talakawa mu muka fi sanin bukatar iyayenmu da kuma abin da za su iya saya.

 Sanin hakan da kuma samun ilmin kirkira zai taimaka mu wadata su da abin da suke bukata wanda zai kasance dai dai da nauyin aljihunsu.

 Yin hakan zai taimakawa tattalin arzikinsu”.

Bayanin da Baffa yayi ya tsaya a zukatan mutane da yawa. Lokacin da aka bashi kyautarsa kuwa ta karshe wacce ta kasance kyauta ga dalibin da ya fi kowanne hazaka.

Har gaban Abbansa yaje ya durkusa yace “Abba am, wan nan naka ne. duk abin da zan samu kai ne tsani”. mallam Jibo hawaye ne ya balle masa. Sai shafa kansa kawai yak e yana hawayen murya.

 Manayan baki da dalibai sai jan Baffa su ke yi domin su yi hoto da shi. A haka taron ya waste. A gida ma Mallam Jibo y adage sai bawa Wabili labara yake yi.

 Fadi ya ke “ke kin ji turanci wajen yban masu gida. Sai rararara yake rattabo shi kamar a turai ka haife shi”.

 

 Bayan Baffa ya dan natsa ya dukufa karatun litattafan addini saboda da mafarkin da yake da shi na zuwa university. Ya  san kuma idan ya tafi ba zai dinga samun lokacin karatun addini sosai ba.

 Tun kafin su gama zana jarrabawar SSCE JAMB din su ta fito inda ya samu maki dari uku da hudu. Shi dai ya zabi jami’ar Lagos saboda ita ce take course din da yake burin karanta.

Yana shagon Abbansa yana taya shi da harkokin cinikinsa, daya daga cikin customers din su ya zo. Cikin da’a da girmamawa Baffa ya gai da shi. Shi kansa yadda Baffa yake tafiyar da shagon wankin ya birge shi.

Lamarin bai kara birge shiba sai da wani mutum da ba ya jin hausa yazo shagon. Tas yaji Baffa ya turance shi. Da farko ganin da yayi yana rubutu ya dauka ko makarantar yaki da jahilci ya ke zuwa. Amma yadda ya ji turancin nan na fita daga bakin yaron sai ya sa ya kasa daurewa yace “wacce makaranta kake zuwa”? 

 “FGC kano. But na gama this year”.

 “Kai masha Allah. Ka rubuta Jamb”

 Kafin ma ya ba da amsa mallam Jibo da kansa yace “ya rubuta. Kuma Alhamdu Lillah ya ci sosai”.

 “Kai amma nayi murna. Ina son ganin yara masu kwazo. Points nawa ka samu”? mutumin ya sake tambaya.

 “304 na samu”.

 “interesting. Gaskiya kana da kwazo da hazaka. Yanzu abin da za a yi, akwai wani shiri da gwamanatin jiha ta ke da shi na niyyar daukar nauyin karatu zuwa kasar waje. Ina daya daga cikin ‘yan kwamitin da Gwamna ya nada domin binciko yara masu hazaka wadanda ake son su ci gajiyar wan nan shiri. Ina fatan makarantar gwamnati kayi primary da secondary”?

 Eh yallabai nan unguwa uku nayi primary da ga nan na samu zuwa FGC Kano”.

 “Very good. In sha Allah idan zan dawo karbar wankin zan taho maka da form din”.

 “Kai madalla Alhaji na gode. Allah ya kara arziki” inji Mallam Jibo.

Ba yadda mutumin nan bai yi ba Mallam Jibo ya gaya masa kudin wankin, ya ki. Ya ce “idan kayi min haka baka kyauta min ba. Cin hanci ke nan zaka bani”.

 “Ba haka bane Alhaji. Ai an yarda da bada tukwucin abin alkhairi”.

 Ba yadda ba su yi ba amma mutumin na yaki sai da ya biya kudin wankin saboda yace aikin sa nemo hazikan yara. Domin kuwa ya ci karo da daya, saukaka masa aiki aka yi ba shi ya yi musu alfarma ba.

 Kwana biyu kuwa da zai zo karbar wankinsa ya tahowa da Baffa form din da yayi alkawari.

Mallam Jibo yaji dadin wan nan lamari, amma fa bai ga yadda zai tura Baffa ko da wani gari karatu ba tare da sanin wan mahaifinsa ba.

 A masallaci ya samu labarin zuwa honourable saboda in dai yana gari gidan baya rabo da ‘yan siyasa. Yaso zuwa da kansa amma Baffa ya nuna masa ba komai ya barshi zai je da kanshi.

 Shi kadai ya doshi gidan Honourable. Ya fi awa biyu yana jira kafin ya samu shiga gidan. A nan falo kuwa ya same su duk da sauran yaran gidan. Duk da ya kai kusan shekaru takwas rabon da su hadu, amma kamarsa da mahaifinsa da take kamar kwabo da kwabo ta sanya farat daya ya gane shi.

 Daya bayan daya ya gai da su, har da Amira da take sa’arsa. Ita ce ma  ta gane shi kai tsaye. Sai Saddam da ya kalle shi yace “Ok na tuna shi yaron nan mai kama da Musa mai wanki”.

 Shi kuwa Amir ko Magana bai yi masa ba, yana ta harkar wayarsa. Ga wani uban gashi da ya side gefe da gefe ya bar tsakiyar kamar kurege. Hannuwansa daure da wasu awarwaraye na dutse da roba, ya cika su a hannu.

 Shi dai yana tsugunne sai ji yayi wani abu mai sanyi ya daki jikinsa tare da jin wata uwar kara data saka shi dagowa a razane. A shagwabe Sopy tace “Mommy vanilla nake so me yasa aka zubo min strawberry”?

 Nan kuwa Mommy ta jawo ta jikinta ta na rarrashin ta. Ita kuma sai wani turje turje ta ke yi tana kuka tana zumboro baki. Uwar ta kai minti biyar tana rarrashi kafin ta yadda tayi shiru. Shi ma kuwa hakan bai samu ba, sai da aka sa mai aiki ta kawo mata wani icecream din ta kuma russuna ta bata hakuri, san nan uwar ta karba ta na bata a baki.

 Shikuwa da yarinyar ta kifa masa ice cream din a jikinsa ba wan da ya bi ta kansa. In da kasan ba a jikin dan Adam tayi wan nan ta’adin ba.

 Shi abin ma dariya ya ba shi. Yarinya ‘yar shekara takwas ke wan nan tabarar. Nan ya tuno nasa kanne da ke aji uku a primary, amma hatta kayansu sun iya wankewa, amma ita wan nan har yanzu ba ta iya cin abinci da kanta ba.

 Ganin ba wanda ya kula da shi. Mai gida yana fama da jarida. Matar gida tana tarairayar shagwababbiyar ‘yarta. Sadam da Amir suna fama da bin wakoki a wayoyinsu. Amira ce kadai ta ke tambayarsa labarin karatu. Ya ce mata shi ma ya gama bana.

 “Au ka gama”? Honourable ya tamabaye shi.   “Eh na gama daddy. Batun makarantar ne ma ya kawo ni saboda na ………

 “Ka ga dakata. Wai me yasa ba ku da tunani ne”, ya katse shi daga Magana. Haka nan ya dakata da zaro form din da ya kawo masa domin ya cika bangaren da aka nemi saka hannun mahaifi ko mariki.

 Cikin fada yaci gaba da cewa “ni ba ka ganin ga nawa yaran. Idan na tsaya hidimar da bata zaman min dole ba ya ka ke son in yi da su?

 Ni ban san me yasa ku talakawan nan ba kwa ganewa ba? An gaya maka ni bani da nawa programmes din? Yanzu tun yaushe yaran nan suke son zuwa hutu Dubai, amma hakan ya gagara saboda kawai mutum yana daukar larurar da ba tasa ba. To gaskiya zan gaya maka na gaji. Ina da nawa uzirarrikan, ba kawai zan jingine su don kawai in faranta maka ba”.

 Baffa kukan zuci yake yi saboda wani dunkule da ya taso ya tsaya a wuyansa. Ya tuna Abbansa ba shi da wadata sai dai godiyar Allah, amma bai taba ganin ranar da aka tambaye shi wani abu ko kuma wani yazo neman taimako a hakan yadda yake ya nuna ko da bacin rai ne a fuskar sa ba.

 Duk randa bukata ta tashi ko ta gida ko ta yara da murmushi a fuskarsa ya ke bayarwa. Idan kuma babu ya bika da kalamai masu dadi. Ya na kuma samu ba mantawa zai yi ba ko ya tsallake. A’a sai ya dawo da karatun baya ya sauke shi tukunna.

 Amma shi wan nan ga dimbin wadatar amma abin da bai taka kara ya karya ba sai ya yi masifa. Ya tsaya ma ya saurari bayanin da ya zo da shi ya kasa. Shi ba kudi ya zo nema ba. Takarda ya kawo ya saka masa hannu. Yana kokarin sake yi masa bayani ya ji dirin muryarsa ya ci gaba da cewa “Ku kullum ba kwa tunani. Kuma ma yaushe zan bata kudina a kan wanda yayi karatu a makarantar gwamnati. An gaya maka cin jarrabawa sauki ne da shi. Kuma ma wacce makarantar kake son zuwa”?

 Muryarsa na rawa yace “University of………”

 Amir da Sadam ne suka kwashe da dariya. Nan kuma Mommy ta saka baki a cikin zancen nasu tace “kaga Baffa kar ka rudi kanka. Tun da dai karatu kake so ka nemi ko ‘yar kumbotso nan ce. Amma University ai tafi karfin ka.

 Wadan da su ka je makarantar kwarai ma ba samun shiga suke ba balle kai da karatun naka a ‘sha kurarka’ ya kare”.

 Honourable ne ya mike a fusace yana fadin “ni ba na son mutum ya dinga hankoron abin da ba  shi da shi. Ka zama yaro mai tunani da kuma tsayawa iya matsayinsa. Amma ka daina rigimowa kanka abin da ya fi karfinka”.

 Baffa bai san lokacin da kwalllar da yake rikewa ta zubo masa ba, sai da yaji dumin ta a fuskarsa san nan ya gane kuka ne ya zo masa.

 “Kaga Daddyn Amir ba haka za’a yi ba. Kai  Baffa tsaya ina zuwa”. Jakarta ta dauko ta kirgo dubu biyu ta mika masa tana fadin “karbi wan nan ka samu ka sayi form din. Allah ya ba da sa’a”.

 Hannunsa na rawa ya saka hannu ya karba yana yi mata godiya. Cike da bakin ciki ya mike yayi musu sallama ya fita daga gidan. Shagon wani business center ya shiga. Sai da ya samu natsuwa san nan ya zauna ya cike form din. Inda ya kamata mahaifi ko mariki ya sa hannu ya rubuta sunan Mallam Jibo.

 Yayi printing din JAMb result din sa. Mai cafe din ne ya sanar masa a kan an saki jarrabwa ta SSCE. Nan take kuwa ya sayi scratch card a wajensa ya bude.

 “ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR!” ita kawai Baffa yake jerawa ganin A1 da A2 ne suke jere reras a result din nasa. Shi kansa mai café din ganin irrin ragargazar da yayi wa SSCE ya ki karbar kudin katin yana taya shi murna.

 Take kuwa ya hada yayi printing. Da ihun murna ya shiga gidansu.

 “tsaya uban masu gida gaya min mai ya faru” Wabili ta tambaye shi.

“ Gwaggo na cinye duka”. 

 “Me ka cinye duka”?

 Sai dada maimaitawa ya ke “Gwaggo na cinye duka”.

 Abbansa ma da ya shigo haka ya tarar da su. Gasu dai cikin murna amma ya kasa fadin murnar me yake yi.  

 Da kyar suka samu ya sanar da su sakamakon jarrabawarsa. Saboda murna Mallam Jibo haka ya fita ya dinga bawa alamajirai sadaka. Sai da yaji aljihunsa ba ko kwabo san nan ya hakura.

 Sai da  aka natsa san nan ya tambayeshi ko ya samu ganin Honourable. Nan kuwa ya sharara masa karyar ai ga takardun ma ya saka hannu. Shi mallam Jibo ba karatu ya iya ba, saboda haka sai ya yarda da batun da ya tsara masa.

 Sai da aka natsa san nan ya nemi lambar wayar DR Adam Mukhtar, wan da shine wanda ya bawa Baffa form din da ya kai gidan honourable ya sa masa hannu amma bai samu komai ba sai tsarabar wulakanci.

 Ba karamin kokari yayi musu ba, na ganin takardun da duk ake nema daga Baffa sun hadu. Hatta passport shi yayi masa.

 Da VISA da takardun duk sun kammala a cikin watanni uku da fitowar jarrabawar su Baffa. Daga nan kuma aka ce su jirayi ranar da za a kira su domin tafiya.

 Tofa! Tun da aka yi haka, Mallam Jibo bai tsaya da addu’a ba. Ya yi sauka ya yi sadaka duk domin nemawa Baffa kariya da kuma sa’a a tafiyar da zai yi zuwa wata kasa.

 A kira su yau a kira su gobe shiru. Su dai sun fawwalawa Allah lamuransu. Sun san in dai rabo ne Baffa zai samu rabonsa.

 Ganin an dauki sama da wata shida ba wani bayani, sai suka fara sarewa. Ga shi sun yi zarya gidan DR Adam, amma an sanar da su yayi tafiya.

 Baffa ya maida hankalinsa kan tafiya zuwa Lagos inda nan ya cike a JAMB dinsa, saboda a tunaninsa zancen kasar waje ya sha ruwa. Abbansa kuwa ya dage da tari. Ko naman miya an daina ci a gidan sabo da ana tarin kudin tafiyar Baffa makaranta.

 A wan nan rana ta daren jumma’a, Mallam Jibo na tsaka da ibadarsa yaji ringing din wayarsa Nokia mai torchlight. A firgice ya katse zikirin da yake yi saboda tunaninsa ko daga can Mayo Lofe nan watau garinsu wani abin tashin hankali ya samu ake neman sa.

 Sai da yayi InnaLillahi san na ya amsa tare da sallama. Wanda ya amsa sallamar daga daya bangaren ya saka shi mikewa tsaye ba shiri.

 “ko ba lambar mallam Jibrin ba ce”? aka dada fada daga daya bangaren.

 Shi kansa na daya bangaren wayar ya fuskanci rudanin da Mallam Jibo ya shiga. Sai ya sake maimata masa introduction dinsa na dazu. Yace “sunana Mallam Inuwa Abubakar  Digil. Gwamna jihar Kano”.

 Muryarsa na rawa yace “yallabai ban san me zan ce bane”.

 “Ba damuwa. Ba ka san yaune ranar da yaron ka Ahmad Musa Ahmad zai tashi zuwa kasar Japan domin fara karatun digiri din sa ba”?

 “Yallabai bani da masaniya, saboda mun yi ta zuwa hukumar da aka tura mu. Wanda muka sani yayi tafiya. Kuma tun da ga lokacin ba mu sake samun wani bayani ba”.

 “Fine ba damuwa. Dauko shi da takardun nasa kuzo filin jirgin sama yanzun nan”.

 Jikin sa na rawa ya tashi Wabili ya na mata bayanin wayar da akayi masa. Shi ma Baffa nan suka taso shi. Ita dai ta basu shawara akan suje in sha Allahu ba, abin da zai faru sai alkhairi.

 A gurguje suka dauki yan tsummokaran Baffa da takardunsa suka ta da wani makocinsu mai Sharon. An yi sa’a ranar a Kano ya kwana, saboda lodin Abuja yake yi. Shi ya dauke su, suka nufi Airport. Ai kuwa kamar a mafarki sai ga su ga gwamna.

 A nan ne suka samu labarin abin da ya faru. Ashe daya daga cikin kwamishinoninsa ne ya cire sunan Baffa ya saka dansa a madadinsa. Sai yayi rashin sa’a ranar da yaran zasu tashi sai ga Gwamna da kansa yayi musu dirar mikiya. Kuma yaki amfani da list din da suka ba shi ya dauko nasa na farko da yayi approving.

 Saboda hatta kudin da ya umarta a bawa yaran wanda za su sai sutura da dan allowance kafin su bude account a can kasar ya tarar sun wawashe.  Ai kuwa sai da ya sa suka yi amon kudin nan. Shi ya dankawa kowanne yaro takardunsa da kuma kudinsa san nan ya yi musu fatan alkhairi.

 Mallam Jibo sai shi da makocinsan suka dawo bayan sunga tashin Baffa da sauran daliban.

 Kuka wurjanjan Mallam Jibo yake yi saboda kewar amininsa da kuma murnar alkhairin da shi Baffan ya samu.

 Fadi yake “ina ma Musa ya na da rai yaga daukakar da Allah ya yi wa uban masu gida”.

 Da wan nan labari suka dawo gida. To mai tafiya yayi, amma fa situation report din Hamida ba dadi. Tun da ta fuskanci Baffa tafiya yayi ya barta ta ke ta gursheken kuka. Tun Wabili na rarrashinta har ta sike. Nan kuwa ta dauko zabori ta fara zabga mata.

 A nan ma ta dada sanin Baffa yayi mata nisa. Saboda ta tuna wata rana da ta kifarwa da Gwaggon ta su mangyada. An caula mata ta daya ta zabga ihu. Daga soro Baffa ya rugo a guje. Ganin abin da ya ke faruwa yayi wajensu a guje. Yana zuwa yayi mata rumfa da jikinsa ba ta yadda Gwaggo zata iya dukanta.

 “Gwaggo kiyi hakuri. Don Allah kiyi hakuri”.

 “Ai kuwa ba zan hakura ta dinga yi min ta’adi ba gaira ba dalili ba”.

 “Gwaggo ta’adin me ta yi miki. Kiyi hakuri zan biya ki”.

 “Ai kullum dai. Komai ta bata kace za ka biya. Yau kuwa jikinta ne zai gaya mata”.

 Ganin yana ta ba ta hakuri ita kuwa ta dage sai ta zane ta ya boye ta a jikinsa ya fita da ita.

Ranar kuwa bai barta ta shigo gidan ba sai da Abbansu ya dawo san nan ya bashi ita amana kar ya bari Gwaggo ta kara dukanta.

 To a wan nan rana haka ta zanu kamar kwarya ba mai ceton ta, sai ma karin haushi su Humaira da suke mata dariya, saboda dama a wuya suke da ita. Ta bata maka kaya Ya Baffa yace mai yasa ka ajiye inda zata iya dakkowa. Tayi maka laifi ka hukunta ta ya ce baka san ita karama ba ce. Idan kuma kayanta ka taba yace kana cin zalinta.

 Haka take kamar ido kowa shayin taba ta yake saboda kawai Ya Baffa ya tsaya mata.

Comments

Popular Posts