☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER ELEVEN ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER ELEVEN

  Yanzu su Baffa sun samu kimanin wata biyu a kasar Japan. Kuma sosai ba laifi harshensu ya dan dada murjewar da yaren kasar. Sabo da haka sai hukumar makaranta ta basu damar fara daukar darussan karatun da ya kawo su.

 Nan ma kuma sun fara a sa’a. Karatu ake koyarwa a aikace watau kusan komai practical ake gwada musu shi. Idan aka zayyana musu karatun watau theory dinsa, sai kuma a nuna musu yadda aka aiwatar da shi a Zahiri.

 Hakan ya saka su fahimtar karatun a saukake. Baffa shi kadai ne a department din da yake karatu a nan Faculty of Engineering inda yake karanta course din MechaTronics wanda ya kasance ilmin mechanical da electrical Engineering ne a hade.

 Shi kadai ne bakar fata. Sai daga baya wani yaro dan Nigeria ya shiga. Ajin su daya. Gashi dai dan masu kudi ne, amma karatun da ya kawo shi ya sa a gaba. Ganin ya samu abokin yi, Baffa ya jone da Ibrahim Salisu Awwal. Shi dan jihar Gombe ne. Da farko Baffa ya fara dari dari da shi, ganin shi dan mai kudi ne. Amma shine ma yake jan sa a jiki.

 Daga baya ma ya bar gidan da mahaifinsa ya kama masa a wajen makaranta ya dawo cikin makaranta, ya kuma yi sa’a daya daga cikin mutum uku da ke cikin dakin ya gama bana. Sai kawai ya samu hukumar makaranta ta bashi dakin da Baffa ke zaune.

 Daya rommmate dinsu dan China ne. Amma kowa ya san su ba sa shiga harkar da ba ruwansu. Ko sallah ya ga Baffa da Ibarhim suna yi sai dai yayi ta kallonsu. Shi kuma computer science yake karantawa. A wajensa suke koyon yadda za su sarrafa na’urar.

 A bin sai ya zamar musu kamar degree biyu suke yi, saboda room mate din su Wang Lee da suka nacewa ya ke koyar da su nasa course din. Duk dan sararin da suka samu suna tare da shi yana koyar dasu abin da ya koyo. Shi ma sai ya dage saboda fahimtar da yayi duk lokacin da ya bata domin koyar da su wani abu sai ya zamanto kamar yana bitar karatun sa ne

 A wan nan rana su Baffa sun shirya domin zuwa sallar jumma inda suke zuwa a wani masallacin ‘yan turkiya mai suna Tokyo Camii wanda ke unguwar Oyama Cho a yankin Shibuya.

 Basu da nisa daga nan saboda kimanin kilometer 14 ce daga makarantarsu zuwa masallacin. Hakan ya sanya ba sa iya zuwa sai jumma’a kawai. Sauran salloli kuwa tun kan zuwansu, suka tarar musulmin sauran kasashe sun roka an basu wani store a makarantar. A nan suke haduwa da sauran musulmi na wasu kasashe suyi khamsa salawat.

 Suna cikin shiryawa, sai Baffa yaji kamar takarda a aljihun rigarsa, ya sa hannu domin ganin komeye sai ga dubu biyun da mommy ta bashi ranar da yaje domin Honourable ya saka masa hannu a takardar scholarship din sa.

 Ya jima da kudin a hannunsa yana kallonsu yana tunano wulakanci da suka yi masa ranar da yaje gidan. Ba su ko saurare shi su ji abin arzikin da ya zo da shi ba, su ka yi masa abin da suka saba yi masa.

 Ya tuna ko sanda yaje gidan domin yi musu sallama wanda shi ma Abbansa ne ya matsa masa akan ba zai tafi har wata kasa ba tare da sanin wan mahaifinsa ba.

 A harabar gidan ya tarar da su da sunan an yi musu feshin maganin kwari da sauro saboda haka akan kujerun gidan na zaman waje ya samesu.

 Kafin ma yayi Magana Mommy ta rufe maigadi da masifar ba ta hana a bar kowa ya shigo ba yau saboda ta fada hutawa ta ke son yi ita da yaranta, saboda washegari za ta mayar da Amir da Saddam da kumaAmira data shiga bana makaranta a England.

 Yana kokarin yi mata bayani abin da ya kawo shi, ita kuwa sai masifa take yi. Shi dai kamewa kawai yayi a wajen.

 “Ina Magana kayi min shiru. Watau ga mahaukaciya ka samu ko?” ta fada a hasale.

 Da ta ga dai ba shi da niyyar motsawa sai ta kalli Saddam tace da shi “kunto min Bingo yayi min maganinsa”.

 Bai gane me ta ke nufi ba, sai da ya ga ya nufi kejin da suke kulle wani durwan kare wanda abin cinsa nama ne kawai. Kullum haka za a bashi danyen nama mai yawan gaske ya cinye.

 Da ganin karen ka san ba wahala zai yi masa ya yagalgala dan Adam ba. To shi mommy da ‘ya’yanta suka sakarwa Baffa. Safiyya kuwa tana rike da wani dikeken teddy bear wanda ko bacci zata yi sai da shi a jikinta.

 Karen nan kuwa haikan ya nufi Baffa. Mai gadi ganin idan karen nan ya damki Baffa to kuwa sai buzunsa, ya nufi igiyar da ke wuyan karen ya ja ya rike da karfinsa.

 Su kuwa su Amir da Saddam sai ihu suke suna fadin “get him bingo! Tear him!”.

 Mai gadin yana rike da karen da ke hankoron cafko Baffa yana fadin “yaro fita kar ya hallaka ka”.

 Baffa takaici da bacin rai sun hana shi motsawa sai maigadin ne ya ja karen da karfin tsiya ya daure shi a kejin , san nan yazo ya ja hannun Baffa Mommy na hargowar “da ka barshi, tun da shi uban ‘yan taurine kai ne. In sa kare ya yagalgala min shi in ga uban da ya tsaya masa har da zai zo har gidana ya min rashin kunya”.

 Ita kuwa Safiya zuwa tayi wajen karen tana fadin “sorry bingo you lost a good meal. Bari inje fridge in dauko maka nama”.

 Shi dai maigadi ya fice da shi yayin da uwar ke masifa, ‘ya’yan na dariya. Sai da ya fita da shi bakin gate din gidan san nan yace masa “yaro kayi hakuri kar ka kara zuwa gidan nan. Wulakancinsu yawa ne da shi.”

 Nan dai ya tafi yana hawayen bakin ciki. Amma a yanzu da ya kalli kudin murmushi kawai yayi. Burinsa daya yayi karatu mai inganci ya tallafi kannensa da Gwaggonsa da kuma Abbansa. Sai kuma Hamidan sa. Tuna sunanta kawai ya sa shi murmushi.

 Ibrahim ne ya kada yatsunsa a fuskarsa, ganin ya kai minti uku da yin sallama amma Baffa bai ma san ya shigo ba. “Come on AMA what are you thinking about. Na dan jima ina jiranka a nan, but you seem to be lost. Tunanin me kakeyi?”

 Bai san ya a kayi ba, sai yaji bakinsa yace “Hamida”.

 “What! AMA yana tunanin yarinya”, ya fada yana tuntsira dariya.

 Murmushi yayi, san nan yace “me ye haka. She is my kid sister. Rigimarta kawai nake tunawa”.

 Zai sake maganar zolaya, Baffa yace “kaga we have to rush kar a fara huduba”.

 Haka nan su Baffa suka dukufa karatu ba kama hannun yaro. Ko dan tsayawa ya yi ya huta, idan ya tuna halin da ya baro gidansu a ciki da kuma yanayin rayuwarsu sai yaji ya kara kaimi da son cimma burinsa.

 Sukuwa su Amir sai da aka kai Amira tare da su, san nan ta gano ashe duk kansu an jima da korarsu daga makarnatar da aka kai su, amma iyayen ba su sani ba.

 Zuwanta ne ya tona asirin zaman nasu. Ga ta dai gida daya aka kama musu da yayyenta, amma ganinta bai hana su kawo ‘yan matan da suka saba ba.

Ta yi waya ta sanar da Mommy halin da suke ciki, ta ce mata kar ta sanar da babansu zata san abin yi. Ita dai ala dole ta bar musu gidan ta koma tana zama da wata kawarta.

 Baffa kuwa karatu ya ke ba kama hannun yaro. Sai dai duk karshen wata ya kan kukuta ya sa kati ya kira mutan gidansu.

 Wata rana yana zaune kawai sai ganin number Nigeria ta kira shi. Ya duba kuma ya ga ba number Abban sa ba ce. Kwarai yayi mamakin jin muryar Hamida.

 “Ina kika samu waya”? ya tambayeta bayan ta gaishe shi.

 “Mh wata amarya aka kawo nan makotanmu shine na sai kati na kawo ta sakamin a wayarta na dauko number ka a wayar Abba”.

 “Lallai Hamidan Baffa ashe ta yi wayo. To ina kika samu kudin katin wayar”? ya sake tambayarta.

 “Kudin break din da Gwaggo take bani kullum nake Tarawa a wajen Anti Sa’a. Shine yanzu da suka taru na sai kati”.

 Har wata kwalla yaji tana kokarin taruwa a idonsa. Tabbas tsakanin Hamida da iyayenta bai san wa yafi kaunarsa ba. Daurewa yayi yace “daga yau ki ringa kashe kudin break dinki. Ni zan dinga kiranki. Ki daina zama da yunwa a makaranta”.

 Nan dai suka dan taba hira kafin katin nata ya kare. Haka kuwa ce ta dinga kasancewa, da ta ga dan kudinta ya taru zata sai kati ta kaiwa amaryar nan ta kira mata yayanta.

 Ba yadda bai yi da ita ba ta daina taki. Ta ce Abba ya gaya mata karatu yake yi bashi da kudin sayen katin waya.

Wata rana sun je masallacin da suke sallar jumma’a, sai yaga an manna notice ana neman wanda zai taimaka da aikin share share da goge goge da kuma wanke wanke a ranakun asabar da lahadi. 

 Nan da nan kuwa ya nemi wan nan aiki ya fara yi. Idan zai tafi sai ya tafi da littafin da ya ke bukatar yayi bita. Idan ya samu sarari aiki ya dan sarara masa sai ya taba karatu.

 Kun san mutane Turkey basa wasa da abinci kamar larabawa. Sai ya dada samun sa’a. idan ya tashi zai taho gida, abincin da mai wajen yake loda masa ya ishe shi yaci har sama da sati gudan ma.

 A dan fridge din dakinsu yake adana abincin sa, ya dinga tsakura shi da Ibrahim suna dumamawa a microwave din da suka saya. Hakan ya ba shi damar adana dan kudin allowance din da gwamnati take bashi.

 Suna haka har karshen shekara tazo. Aka basu hutun wata uku. Ibrahim yana ta shiryen shiryen zuwa hutu shi kuwa bai mayi tunanin zuwa ba. Da zai tafi kuwa ya hada dan kudin da ya tara na kusan allowance din sa na wata shida. Saboda tun da ya fara aiki ya ke tara kudin da gwamantai ta tanadar masa domin abinci da lamuran yau da kullum.

 Ya san matsayinsa ya kuma yi kokarin tsayawa iya matsayin nasa. Haka zalika ya san abin da ya kawo shi garin shi kuma ya mai da hankali yake yi. Ko gajiya yaji na neman buge shi, da ya tuno da dan tsukakken gidansu, ko ya tuno yadda Abbansu yake gwagwamarya wajen neman musu rufin asiri, sai yaji kamar an jona masa caji. Gajiyar sai ya ji duk ta bar jikinsa.

 Hakan yake dada kara masa kaimi da kwazon neman abin da aka kawo su suyi.

 Ga tarbiyya da ya tsayarwa kansa. Muraja’ar karatunsa da ya saba a gida bai daina ba. Azumin litinin da alkhamis da ya saba shi ma ya ci gaba da abinsa. Zuwansa karatu kasar waje bai sa ya mance da nasihar Abbansa inda ya yi ta gargadinsa da duk rintsi kar ya yar da koyawar addininsa.  

 Ranar da Ibrahim zai tafi ya dauko kudinsa wadan da ya canza zuwa dala. Ya kuwa samu kimanin dala dubu daya da dari uku. Dala dubun  ya dauka ya bashi sauran kuma ya sayi waya mai dan kyau ya bayar a kaiwa Abbansa.

 A cikin tsarabar tasa ba abin da ya bawa Ibrahim mamaki irin dutsen guga da ya ga ya saya har guda uku masu ingancin gaske. San nan ya dan tsintar musu yan suturu dai dai misali.

 Amma fa komai na Hamida ya nunka na su Humaira. Da ya zo dauko kudi zai bashi ne sai ga dubu biyu kudin Nigeria sun fado daga ma’ajiyar tasa.

 Ibrahim ya sunkuya ya dauka da sauri yana fadin “yawwa kaga na samu na taxi kafin in yi canji”.

Da sauri Baffa ya fisge kudin. Sai da ya dan nutsu ya kalli kudin san nan yace “sorry Ibu. I cant give you this money. Na kumayi alkawari komai talauci ba zan kashe su ba har sai na maidawa mai su”.

 “Fine! Bani wan nan sai in taho maka da wasu daga Niger” Ibrahim ya fada masa.

 “Ka yi hakuri. I want to return the exact notes”. Zai kara Magana, Baffa yace “pls forget about that. Na tuna Hamida tana da gashi, and ba ta son kitso. Dazu a mall din nan naga colourful ribbons masu kyau. Muje in saya mata”.

 “Gaskiya kana ji da Hamidan nan. Anya zaka iya ba da aurenta kuwa”?

 Bai bashi amsa ba, sai murmushi kawai da ya yi. Ranar da Ibrahim ya sauka a Nigeria. Da ga Lagos jirgin Kano ya hau saboda ya mika sakon AMA gidansu.

 Bai san kan kano sosai ba, sai ya nemi wani abokinsa. Shi ya raka shi har unguwar da Baffa ya kwatanta masa. Sun kuwa yi sa’a, a rumfar Sale mai shayi suka tsaya domin tambaya,wanda kuma ya kasance makocin shagon Mallam Jibo ne.

 Da rawar jiki Mallam Jibo ya tare su saboda jin abokin Baffa ne da suke karatu a can kasar ya kawo musu ziyara. Barin komai yayi ya musu jagora zuwa gidansa. Cike da murna ya ke yi wa Wabili bayanin bakin nasa. Murna kamar shi su ka gani. A wan nan rana fura ta daka da hannun ta saboda ita mallam Jibo ya nuna sha’awar son sha. Nan da nan kuwa aka dire musu ita.

 Ya sake fita sai ga shi da dakwalen zakaru guda biyu ya shigo da su akan a dafawa baki. Dakin da Baffa yake zama ya yi musu jagora saboda nan ya gyara a matsayin falon baki.

 Nan yaci gaba da tambayarsu yanayin da Baffa yake ciki. Ibrahim ya na yi masa bayani, a lokaci guda kuma yana nuna masa hotunan da Baffa ya dauka ya bayar a kawo musu.

 Da sauri ya fita yana fadin “Wabili fito ki ga uban masu gida yadda ya kara girma da kyau”.

 Ita ma kuwa cike da murna take kallon hoto cike da mamakin kyan da girma da Baffa ya kara. Farinsa ya fito sosai. Kowa ya gan shi yaga mahaifinsa Mallam Musa. Sai dai kyau da kuruciya da ya fi shi.

 Fadi take yi “yanzu Mallam wan nan baturen Baffa ne”?

 Su Humaira ma nan suka dawo suka tarar da bakon gidansu. Inda ka san Baffa suka gani haka suka dinga murna. Hamida kuwa ta matsa ta ba su guri ma su ci abinci ta kasa. Ganin su take kamar Ya Baffanta ta gani.

 Tun wajen goma na safe suke gidan ba su suka samu suka bar gidan ba sai bayan azahar. Shi ma don yayi musu alkawarin in dai zai koma zai sake biyowa su gai sa ne.

 Ya bude akwatin tsarabar Baffa ya cire ledar dake dauke da sakon Hamida ya mika mata. Saboda amanar da Baffa ya bashi ke nan a kan ya bawa Hamida nata sakon da ban, saboda kar Innarsa ta hanata duka.

 Kin karabar ledar tayi ta fara kuka. Da kyar Ibrahim ya rarrashe ta yana tamabayarta dalilin kukanta. Cikin shesshekar kuka tace “yaya ya tafi ya barni. Kuma ya yi min alkawari zai dawo ya dauke ni mu tafi tare amma ya ki zuwa”.

 Shi ma ya tausayawa yarinyar. Da gani ba karamara shakuwa ce a tsakaninsu da AMA ba.  Duk da ya san dare yayi a can, amma haka ya kira Baffa a waya, saboda ya lura shi kadai ne zai iya rarrashin Hamidarsa. Sai shine kuwa ya rarrashe ta. Nan kuwa ya samu dama ya yi wa Abbansa bayanin sakon da ya aiko da shi.

 Sai da zasu tafi san nan Ibrahim ya dauko sakon kudin da Baffa ya  bashi, ya bawa Abbansa. Fada Mallam Jibo ya dinga yi yana fadin “shi da yake fama da kansa meye nasa na aike ban da kaya har da makudan kudi”.

 Ibrahim ne ya kwantar masa da hankali in da ya nuna masa, AMA ba shi da wata matsala. Nan kuma ya sanar da shi dan aikin da ya samu ya ke yi.

 Sai da ya ga kayan mutane da aka wanke aka goge a dakin soron da suka sauka, ya gane dalilin Baffa na sayen dutsen guga har guda uku. Ashe sana’ar babansa ya ke son habbakawa.

 Wan nan abokin na sa na kano ya hada da mallam Jibo saboda ya taimaka masa ya canza masa kudin, san nan ya taimaka masa da bude account a banki domin adana kudinsa.

 Haka zalika da zai tafi ya sake biyowa ta Kano saboda nanatawar da mallam Jibo ya dinga yi masa akan lallai ya dawo ya karbar masa sako.

 Ganin yadda iyayen Baffa ke ji da shi ya sa, ya ware kilo goma domin daukar sakon Baffa kawai. Saboda ya san ba su san ana kayyade iya adadin nauyin kayan da kowanne fasinja zai iya dauka a jirgi ba.

 Aikuwa zatonsa ya tabbata gaskiya. Mallam Jibo ya laftowa Baffa kilishi. Ga danbun nama da Innarsa tayi masa mai yawan gaske. Ga su busasshiyar fura da yaji kala-kala.

 Kannensa kuwa har da su gullisuwa da alawar madara. Shi kansa kaunar da suke nunawa junansu tana birgeshi. Su biyu ne kawai shi da yayarsa ita kuwa tayi aure, saboda haka ba kowa a gidansu sai ‘yan uwa idan sun zo.

 Abu daya ne ya daurewa Ibrahim kai. Ya san sunan Baffa Ahmad Musa Ahmad wanda shine dalilin da tun a FGC ake kiransa da AMA. Ga kuma sunan Abban sa Jibrin. Ya daukar masa hotunan kannensa kamar yadda ya bukata ya tafi masa da shi, a wayarsa.

 Bayan ya isa Tokyo ana ta murnar haduwa da juna, Ibarahim ya kasa daurewa yace “AMA sorry, kar ka ga kamar ina pocknosing. Amma me yasa baka amfani da sunan babanka as your surname”?

 “I am” ya fada da murya mai nuna alamun damuwa.

 “No you are not. Your surname is Musa, and naji sunan Abbanka Jibrin. Ka san a musulunci ba a son using sunan wani as surname in ba na mahaifi ba”.

 “Da gaske nake maka sunan babana Musa. Abbana abokin baba na ne”.

 “Allahu kabar!. And so much care and attention daga wajen abokin baba. Gaskiya yana sonka sosai. You need to see the glow on their faces da na ce musu ni abokinka ne”.

 Nan Baffa ya bashi dan takaitaccen tarihinsa, amma ya yanke labarin wan mahaifinsa. Ibarahim ya jajanta ma sa rashin iyayensa da kuma nuna jinjinawarsa ga Mallam Jibo yadda ya dauki nauyin yara har uku wanda ba shi da alaka ta jini da su.

 Cike da tsokana yace “and Hamida. Ke nan ita ba blood sister din ka bace”?

 Gyada masa kai kawai yayi.

 Dariya ya sake tuntsirewa yace “ashe ita zaka iya aurenta ke nan”?

 Filo kawai ya maka masa bai bashi amsa ba. Shekara hudu cur su Baffa suka kwashe suna diban karatu. A jarrabawarsu ta karshe ma kuwa, abin da Baffa ya saba samu shi ya samu. Shi ya fita da sakamakon da makarantar ba ta taba fitar da dalibi mai irin wan nan sakamakon ba.

 Take kuwa hukumar makarantar ta dauki nauyin karatun sa  na degree na biyu. Bai samu zuwa gida ba sai waya da yayi ya sanar da su alkhairin da ya same shi.

 Su ma a nan gida, Alhamdu Lillah. Komai na tafiya daidai. Sana’ar dai da kowa ya san mallam Jibo da ita, to ita din ya ke yi sai dai ya dada samun sauki saboda dutsen guga na lantarki da Baffa ya saya masa, wanda hakan ya dada saukaka da kuma habaka sana’ar tasa.

 Sai dai kun san samun talaka, duk abin da aka samu a larurar yau da kullum take karewa. Lokaci lokaci Baffa ya kan aika musu da sakon kudi wanda in dai yazo to kuwa har makota sai sun san Baffa yayi aike, saboda sai ya ficincinawa kowa. Sauran kuma ya adana.

 Sau daya ya taba zuwa gidan honourable da sunan ya sanar da shi me Baffa ya ke ciki ya kuma samma masa dan abin arzikin da yake aiko musu a matsayinsa na shakikin dan uwansa. Amma ko saurarensa bai yi ba ya rufe shi da masifa ya kuma sake kora masa bayanin kar ya sake zuwa masa gida tun da shi ba abin da suka hada da shi.

 Wan nan dalili ya sanya ya fita sabgar honourable gaba daya. Ya kuma hakura da kokarin da yake yi domin yaran dan uwansa su saba da shi.

     *******************

Comments

Popular Posts