☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER EIGHT ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/





CHAPTER EIGHT

 Baffa ya samu ya shiga FGC dake kano. Da farkon Abbansa ya so ya sa shi ta kwana saboda yana so ya mai da hankalinsa kan karatunsa amma shi yaron da kansa yaki. Ba kuwa wani abu bane ya hana shi tun da in don karatun islamiyya ne yayi sauka gab da tafiyar sa secondary.

 Saboda karatun nasa hawa biyu ne. Ya yi a makaranta. Idan ya dawo gida Abbansa ya dora masa. Sai karatun makaranta ya zamar masa mai mai.

 Dalili sa na kin zuwa makarantar kwana yawan kudin da yaga an rubuta za’a kashe . Ya san kuwa idan ya gaya wa Abbansa sai ya ganganda ya nemo su. Duk da yaro ne shi, amma yana da zurfin tunani. Haka zalika ya san halin da suke cike.

  Sai yayi wa Abban nasa karya da cewar ta jeka ka dawo aka dauke shi. Shi ma kuwa sai da aka ji jiki aka samu aka hada kudin litaffi da na uniform da kuma kudin makaranta.

 Cike da sa’a kuwa ya fara zuwa makarantar. Kullum da kafa yake takawa tun daga unguwa uku wajen masallacin Faruku har FGC Kano. Ko Abban ya bashi kudin bus sai yaki karba.

 Kuma tun karin safe da zai yi a gida ba zai sake cin komai ba har sai ya dawo gida, saboda kawai baya son Abbansa ya wahala.

 Ga wadan nan ‘yan lukutayen na Gwaggo kamar yadda yake kiran su Zahra da Humaira. Da an saya musu kaya kwana kadan sun cika su. Kamar ana hura su. Ga Gwaggon ta bata su.

 Indomie pakitin guda idan an dafa tsaf zasu tashi da ita. Haka idan awara ce suka samu yanka hudu manya, ita ma sai dai labari. Abban su kuwa da ya lura suna son indomie ko za a zauna ba ci abinci a gidan ba sai ya sayo musu ita.

 Haka ya dada sanya Baffa daurewa wasu abubuwa na rayuwa. Shi bai cika surutu ba, gwanda ma da Gwaggonsa tun da ita mace ce mai harka.

 A makarantar ma da yake zuwa kafin term biyu malamai sun fara sanin sa saboda kwazonsa. Term din farko ne kawai da yaje a makare ya yi na biyar. Ana biyu kuwa ya dauko kambunsa  na daya.

 Yana term na uku ya dawo gida ya tarar da Gwaggonsa bata da lafiya. Amma ya rasa gane dalilin da Abbansa yake ta murna da ciwon nata. Sai da aka dauki watanni san nan ya gane ashe cike ne Gwaggonsa take da shi.

 Gwaggonsa na tashe da tsohon cikinta lokacin haihuwa ko yau ko gobe, Allah ya jarabci Humaira da Zarah da cutar kyanda.

Hankalin Gwaggo ba karamin tashi ya yi ba. Ga matsin rayuwa da ake ciki. A kan yaran nan ta salwanta da duk wata kadara da take da ita.

 Sun kwashe sama da sati uku a asibitin Hasiya Bayero. Dan kiwonta da dan kayan dakinta duk haka ta tattara su ta sayar a karye saboda ta samu nasayen magani.

 A wannan lokaci duk gidan sai da su ka jigata. Mallam Jibo kullum ya na zarya daga gidansa nan unguwa uku zuwa gidan sarki. Ga sana’a ta kullum fita ake a nemo abin da za a ci.

 To, ba shi da natsuwar da zai ma zauna ya yi sana’ar ta sa. Ita kanta uwar yaran ga halin da ta ke ciki. Ciwon nan kuwa da ya kama su Humaira sai da aka fid da rai da su.

 Mallam Jibo sai kuka yake ya na fadin “Allah kar ka dauki ahalin Mallam Musa a hannuna.

 Ganin halin da suke ciki ya sanya shi garzayawa gidan Honourable domin ya sanar da shi. Shi ba kudin magani ya ke nema ba, amma dai wani shakikinsu ya san halin da suke ciki.

 Baima samu ganinsa ba sai , Mommy ya samu. Yana ga ma gaya mata halin da su ke ciki ta rufe shi da fada. Fadi take “in ban da rubar tsiya me ye na kai su asibiti. Abin da man kifi a ake bayarwa da kuma bommi, amma shi ne kai saboda ka san akwai mai kudin banza ka dauko tsawo kamar bishiyar turare ka taho a ba ka kudin magani.

 Sai ka san nayi baitulmalin naka ba ya nan”.

A haka cike da bakin cikin abin da ta gaya ma sa, ya bar gidan. Asibitin ya dosa saboda ya san ya barsu tsakanin rayuwa da mutuwa.

Shi bai taba sanin kyanda idan ta yi mugun kamu har dayewa jikin yara yake ba kamar sun kone sai a kan su Humaira.

 Shugabar asibitin ya samu a tare da su watau DR Binta Jibir tana duba su, ta ke ta canza masu wasu alluran. Yaje wajen biya aka yanka masa makudan kudi.

 Ya dawo yake sanar da Wabili. Tace “Mallam yi sauri gida akwai ragowar rago guda daya da aka barshi domin hakika a sayar da shi kawai”.

 “Gaskiyar ki Wabili. Ga na gaban mu yaushe za a tsaya yi wa wanda bai zo duniya ba. Bari in yi sauri in je gidan. Bai fi awa daya da tafiya ba, ya dawo da kudi ya karyar da ragon.

 CMD Binta Jibir tana gefe taji ya na yiwa pharmacist din bayani ya taimaka ya karbi kudin da ya ke da su, shi kuma ya yi alkawarin ko zai kwana  ya wuni ya na sana’arsa zai hado masa sauran kudinsa. Shi dai bukatarsa ya ba shi alluran complete a fara yi wa yaran.

 “Mallam sana’ar me kakeyi” CMDn ta tambaye shi.

 “Likita wanki da guga nake yi a unguwarmu”. Ya amsa mata cikin ladabi.

 Ta mai da hankalinta wajen pharmacist din. San nan tace “give him all the drugs as well as the injection and send me the bill”. San nan ta juya wajen Mallam Musa tace “kayi hakuri zai ba ka magungunan. Allah ya basu lafiya”.

 “Amin amin likita na gode”, ya fada yana mai rissinawa. Kafin ma ya ci gaba da godiyar  ta yi gaba abinta ta barshi a nan. Ya juya wajen pharmacist din yana kokarin mika masa kudin da ke wajensa.

 “Barshi Mallan ai Dr ta biya duka”.

  Sujudu shukur ya tsugunna yayi saboda murna. Cikin hukunci Allah ana fara amfani da sabbin magungunan nan sauki ya dinga samuwa. Kafin kwana hudu kamar ba su ba. Har sun fara karbar abinci. Kafin sati har ramarsu ta fara tafiya.

 Sai bayan sati biyu da faruwar haka san nan aka sallame su. Har ofis din CMD su ka je su ka yi mata godiyar alkhairin da ta yi musu.

   Baffa ya na form two second term, Allah ya sauke Gwaggonsa lafiya ta samu ‘ya mace. Tun da aka wanke yarinya aka mika masa ya rike ta tam a hannunsa ya kasa dauke idonsa da ga kanta.

 Wata makociyar su ce data shigo barka tace “Baffa ka kama yarinya ka rike gam ka hana kowa”.

 Duk dakin aka sa dariya. Shi dai murmushi yayi. Ya juya ya kali Gwaggon sa, ya ce “Gwaggo ta na da kyau. Ta fi kowa kyau a gidan nan. ki bani ita”.

 “Ai dama taka ce Baffa”.

 Tun daga lokaci kuwa ya dauki aniyar ba ta kulawa. Ranar suna ma shi ya zaba mata suna, in da ya sa Abbansa ya rada mata Hamida. Yarinyar nan haka akayi sunanta ba tare da hakika ba, saboda kudin rago ya tafi a hidimar asibitin su Humaira.

 Ranar suna Baffa ya na ta jira ya ga an yanka rago ya ga shiru. “Abba sai yaushe za a yanka ragon suna”? Ya tambayi Abbansu.

 Sai da ya shafa kansa, san nan ya ce “Baffa yankan suna sai mutum ya na da halin yinsa yake yi. Idan babu ba wajibi ba ne”.

 “Ke nan ita Hamida ba za a yanka mata ragon suna ba”?

 “Kayi hakuri Baffa ko a gaba na samu dama sai in yanka mata. Ai na so ma ko da dan akuya aka samu a yanka ta bai samu bane”.

 Shiru ya yi bai ba shi amsa ba. Tun daga wan nan lokaci Baffa ya koma wajen Sale mai Shayin a nan unguwarsu. Ya dinga yi masa wanke wanken kofunan da farantan indomie da aka yi amfani da su, shi kuma ya na bashi lada.

  Ga shi ya yi sa’a sun samu hutun makaranta. Kafin wata kuwa sai daya hada kudin dan akuya. Bai yi shawara da kowa ba sai ganinsa kawai aka yi ya shigo da shi wai ga shi ya kawo a yi wa kanwarsa Hakika da shi. Da kyar aka lallaba shi ya yarda a bar mata a kiwata mata shi tun da hakikar ba wajibi ba ce.

 Baffa bai taba nuna shaukinsa a kan yara ba, sai a kan Hamida. Idan Zahra da Humaira za su kwana suna kuka ba zai kula da su ba. amma ita ko yaya ya ji kukan ta yanzu zai bar abin da yake ya dauke ta.

 Kafin wata biyar kuwa ya koya mata dan lasar abubuwa, saboda komai ya samu na ci sai ya lasa mata. Balle ma da yake tana da wata shida Wabilin ta sake samun ciki inda ta haifi namiji.

 Tun yana tsumma Mallam Jibo yayi masa huduba da Musa. Shi ma suna kiransa da Walid. Zuwansa bai dakushe tauraruwar Hamida ba. Shi dai Baffa Hamida ce tasa.

 Wani lokaci har korafi Wabili take yi na halin ko in kula da yake nunwa a kan ‘yan biyunta. Ranar nan ya gaji yace mata wai sun cika kumatu basu da kyau. Ita kuwa Hamida tafi su kyau.

 Dariya tayi tace “a ga dai mai kyan a cikinsu. Amma kowa ya kalli su Humaira ai ya san kyawawa ne. kai dai kawai son kai zaka yi”.

 Murmushinsa na sabo yayi. Ko fita zai yi daga gidan sai yayi mata wayo, in ba haka ba ya tafi ya bar Wabili da aikin rarrashi. Komai kukan da take da taji muryarsa za ta yi shiru.

 Suna term na karshe aji uku na karamar sakandire aka gayyaci makarantarsu quiz har Lagos. Ba tare da doguwar shawara ba, makaranta ta zabi Baffa a matsayin daya daga cikin daliban da zai wakilci makarantarsu. In da ka san za shi wata duniya haka hankalin Mallam Jibo da Wabili ya tashi.

 Da kyar principal din ya dau lokaci yana masa bayani kafin hankalinsu ya kwanta. Ana I gobe zasu tafi kuwa, Wabili ta sha jan kunne akan Hamida. Haka ta zauna kamar ita ce uwar shi kuma dan. Baffa ya dage ya na zayyano mata abubuwan da za a kiyaye kar a yi wa Hamida da kuma wanda yake son a dinga yi mata.

 Har ya tafi ya kwanta ya sake fitowa da asusunsa ya fasa ya debo dan tarinsa duka ya mikawa Gwaggo yace ga shi nan a dinga saya mata biredi da kayan shayin da yasan ta na so. Ya kuma hada da sharadin kar su Humaira ko Walid wani ya sha mata.

 Sun isa lagos lafiya. Aka basu masauki a makarantar FGC da ke garin. Sai da suka kwana suka huta san nan washe gari aka nufi babban hall din dake makarantar inda a nan ne za a yi gasar.

 Gwamnan garin shine babban bako. A cikin jawabinsa ya yabawa yaran da nuna musu kwazon su ne ya sa aka zabo su a cikin miliyoyin dalibai. Saboda haka suyi kokari su ci gajiyar wan nan baiwa da Allah ya basu.

 Bayan nan ya yi alkawarin bawa duk dalibin da ya fi kowa yawan maki kyautar naira dubu hamsin wacce zata kasance mallakinsa ba na makarantar da ya wakilta ba.

 Kafin a fara gasar sai shugaban gasar ya bawa dalibai dama su gabatar da kansu.

Da aka zo kan Baffa ya mike cike da karfin gwuiwa saboda ba kananan adduo’I Abbansa ya sa shi ya dinga yi ba wadanda za su hana shi tsoron Magana a cikin mutane da kuma kudurtawa ransa nasara daga Allah SWT take.  

 Tun a hanya yake yi. Da suka iso ma cikin dare ya dada yi. Bayan nan yau bayan sallar asuba, bayan yayi karatun sa na izu daya da yake yi kullum ya dora da adduo’in.

 Saboda haka ba tare da wani tsoro ba, ya karbi micro phone yana amsa tambayoyin da ake masa.

 Da farko ya gabatar da kansa in da ya amsa tambayar suna da shekaru da kuma jiha da presenter yayi masa. Cikin turanci ake gudanar da komai. Shi ma kuwa cikin turncin ya amsa “suna na Ahmad Musa Ahmad. Shekarata goma sha uku. Ina karatu a FGC Kano. Ina kuma daya daga cikin daliban da zasu wakilci jihar Kano”.

 “Da kyau” presenter ya fada. San nan ya sake cewa “banda kyautar da za a bawa jihar da ta ci, mai girma gwamna yayi alkawarin ba da kyauta ta musamman ga duk dalibi da ya zamo zakara a wan nan gasa. Idan kaci me zakayi da wadan nan kudin”?

 Baffa ya sake cewa “ni babana sana’ar sa wanki da guga. Tun ina class three ana mana subject a basic science na taba ganin hoton injin wanki. Tun a lokacin naci burin duk kudin da na fara samu a rayuwata zan tara in saya masa injin wanki saboda ya huta da wahalar wanki da yake yi da karfinsa. Saboda haka Idan har na ci wannan gasa zan saya masa injin wanki da kudin”.

 Gaba daya hall din ya dau tafi na musamman saboda a duk daliban da aka yiwa irin wan nan tambaya sai ya zamanto shine kadai dalibin da mahaifinsa ba dan boko ba, ba kuma wani dan kasuwa ba. San nan shine dalibi mafi kankantar shekaru.

 Bayan an natsa aka fara gwabza gasa. Zagayen farko jihar kano tazo ta biyu. A zagaye na biyu tazo ta farko. Sai ya rage saura jihohi hudu da za su kara a  zagaye na karshe. Da jihar Lagos da Bayelsa da Benue sai kuma ita Kanon.

 Nanfa kowanne dalibi ya dage ya ke zubo albarkar kwakwalwarsa. A kullum akan tara yawan tambayoyin da kowanne dalibi ya samu dai dai. Kullum aka tara Baffa ne gaba.

 A rana ta uku da fara gasar wacce ta kasance ita ce ranar karshe, jihar kano ta lashe gasar. Haka zalika Baffa ya cinye kyautar Gwamna ta dubu hamsin.

 Gwamna kuwa da kansa ya bashi kyautar da yayi alkawari. Ya danka masa zunzurutun kudinsa cash a hannu. Anan kuma ya dada tambayarsa me yake son saya da kudinsa yace injin wanki kamar yadda ya fada da farko.

 Gwamna ya bayar da umarnin lalle kafin su tafi a kai shi ya sai injin wankin da yake so da kudinsa.

 Malamin da ya tafi dasu shi ya raka shi kasuwa ya kuma taya shi da zaben injin da zai dace da sana’ar mahaifinsa. Sauran kudin ya raba gida hudu. Malamin su ya bawa daya shi da sauran dalibai biyu da suka zo, kowa ya dauki kashi daya.

 Nan fa duk suka shiga kasuwa kowa yayi tsaraba. Har makota ya sayawa tsaraba, amma tsarabar gimbiyarsa ta zarce ta kowa. Rabin jakar duk kayanta ne.

 Sun iso lafiya. Baffa kuma ya iso da lambar yabo na dalibin da ya fi kowa hazaka a wan nan gasar.

 Bayan ‘yan murna da sannu da zuwa sun natsa Hamida dai na makale a jikinsa, saboda tana jin muryarsa ta tattako ta karaso a soro su ka yi kiliya da juna.

Sai bayan ya huta ya ci abinci san nan ya kunce tsaraba yana basu labarin Lagos da irin gine ginen da ya gani. Ya fito da hotunan da suka dauka yana nuna musu. Kafin ya bawa kowa komai ya ware kaya da takalma da kayan wasa sama da kala goma. Kowanne ya dauko sai yace “wan nan na Hamida ne”. sai da aka kusa rabin jaka san nan Wabili tace “wai ni Baffa ita kadai ka yowa tsaraba ne”?

 “Aa Gwaggo lukutayen ki ma na sayo musu tasu”.

 Mallam Jibo ne yayi dariya yace “ai kin san Baffa da Hamida ba a shiga tsakaninsu. Amma dai ina fatan baka manta da abokina ba ko”? watau yana nufin Walid.

 Kowa dai ya samu rabonsa. Sai da ya gama da wan nan san na ya mike ya farke dirkiken kwalin da ya zo da shi

  Mallam Jibo yana kallon ikon Allah. Ga dai wani farin sunduki nan. Shi ba akwati ba shi ba fridge ba.

 Da hanzari Baffa ya nufi socket din da ke tsakar gida. Su dai su na kallon ikon Allah. Ya kai minti talatin ya jona wan nan ya daura wancan har ya samu ya hada injin kamar yadda mai sayarwar ya nuna masa.

 “Abba akwai kayan wanki”?

  “Akwai. Amma ina fatan ba wankin zaka yi ba daga dawowarka”? Abban ya amsa masa.

 “Abba kai dai bari kaga ikon Allah”.

 Ya shiga dakin ya debo kayan da ya san na wanki ne. Ya ware farare da kuma wadanda yake tsammanin masu zuba ne daban. Ya debi kayan da dan dama ya zuba a ciki.

 Mallam jibo ya dan razana, sai fadi yake “Baffa kar ka ka nikewa Alhaji Sammani kaya. Kaga kayansa masu daraja ne sosai”.

 Dariya ya yi san nan ya ce “Abba kwantar da hankali ka ba abin da zai same su”.

 Ya debo ruwa ya zuba san nan ya dauki gudan sabulu ya wurga. Yana murza ‘yar wata roba. Sai inji ya fara kuku ‘gurum gurum’. Ya na yi yana juya kayan nan.

 Wabili fadi take “ikon Allah yau zan ga abin da za a yi da kayannan”.

 Ai kuwa suna tsaye suna kallon ikon Allah sai gani sukayi ruwa ya fara kumfa. Bayan kamar minti goma sha biyar, injin yayi shiru ya daina motsawa. Baffa ya dada murda wani waje  sai su ka ga ruwan kumfa na malallowa, har sai da ruwan nan ya kwaranwe gaba daya. Baffa ya debo wani ruwan na dauraya ya zuba ya sake murda robar farko. Nan take kuwa injin nan ya ci gaba da juyawa. Bayan kamar minti biyar ya sake murda daya robar ya zubar da ruwan daurayar.

 Mamaki bai kara kamasu ba, sai da suka ga ya debi kayan ya zuba a daya bangaren sundukin ya kunna shi. Shima ya dauki wata kara wuu wuu kamar iska ta taso. Bayan kamar wata minti biyar din ya fito da kayan nan kal da su har wani kyalli suke tsabar wankuwa, gasu kuma kyamas ba ruwa ko kadan a jiki.

 “Ikon Allah”, Mallam Jibo ya fada da tsananin mamaki. “shi kuma wan nan injin wanki yake yi”?

 “Ai ni na ma rasa bakin Magana”, inji Wabili yayin data daga kayan tana dada dubawa.

 Murmushi ya yi ya kalli Abban nasa yace “tun mu na class three na ga hotonsa an rubuta shi a cikin injun nan zamani da ake amfani da su. Tun a lokacin na yi alkawarin duk kudin da na fara samu a rayuwa Abbana zan sayawa injin wanki ya daina wahalar wanki da karfin sa”.

 Wani hawayen ne ya zubo masa, wan da ya kasance na dadi da kuma na tunawa da marigayin abokinsa. Ina ma ya na raye yaga dan albarkar da Allah ya bashi.

 Shafa kansa yayi yana shi masa albarka. Sannu a hankali Mallam jibo ya gane yadda zai sarrafa injin wankinsa. Nan da nan kuwa sana’ar sa ta dada habaka. Saboda wankin da zai yi a sati a yini daya injin sa zai masa shi.

 Da abin ya bunkasa ma sai shi Baffa ya hana shi guga ya sa suka samo almajirai suna gugar su kuma suna biyansu.

 Akwai wani course da ke yi musu a makaranta mai suna entrepreneurship watau koyar da kananan sana’oi. Nan kuwa ya maida hankalinsa ya koyi subject din da kyau. A nan ya koyi dabarar tafiyar da business din Abbansa.  

 Har register ya bude masa ta yadda za a dinga rubuta sunan customers da kuma ranar da zasu dauki kayansu.

 A hankali ma sai wani gida ya kama haya saboda soron sa yayi kadan. Alamjiran da suke masa guga su su ke kwana a daki dayan na gidan

           *****************

Comments

Popular Posts