☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER 21 ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER TWENTY ONE

 Suna tafe a hanya ya kalli Abban nasa ya ce “Abba yaya ka ke fama da hidimar gida”?

 Sai da yayi murmushi san nan ya ce “Uban masu gida ai ba wata hidima da ta sha kaina. Shagon wanki yayi albarka. Duk dawainiyarmu da albarkar wajen mu ke yi”.

 “Abba gidan ne na ganshi yadda na tafi na barshi. Sai na ga kamar aiken da na yi bai yi tasiri ba, saboda yawan hidimar gidan”.

 Murmushi yayi, saboda ya fuskanci inda Baffan ya dosa. Watau ya na son sanin me ya sa ba suyi amfani da kudaden da yake turo musu ba, amma kuma yana kokarin kar tambayar ta zama kamar titsiye.

 “Aike ya yi tasiri sosai Uban masu gida. Ka san an ce kudi wawaye ne ba su da wuyar taruwa. Sai ka ga yadda kudin nan suka taru”.

 “Abba taruwa kamar yaya”? Baffa ya tambaya cike da mamakin kalaman Abban nasa.

 Sai da ya nisa san nan y ace “kasan harkar kasar nan. To tsoron kar ka gama karatun ka dawo gida a rasa aikin yi. Sai naga bari in tanada su. In an samu abin yi shike nan. Idan ba a samu ba sai ka kama wata sana’ar.

 Kuma Alhamdulillah, ai ba abin da ya gagara na lamuran yau da kullum. Kuma hidimar ma ai ta ragu. Kannenka duk sun samu sunyi karatu kamar yadda ka ke buri.

 Suma ‘yan biyun Gwaggo duk da yadda lamura suka so rincabewa, ai kaga da aka sa addu’a a gaba aka kuma rungumi kaddara, ai komai ya daidaita.

 Kaga ita Humaira uwar dakin nata ba karamin kula take da ita ba. Kana ganinta ma ta koma kamar wata baturiya saboda kula da ta ke samu.

 Ita ma kuma Zahran ai zaman nata ba laifi a wajen yayar ta ta. Duk da hidimar gida da take fama da ita, amma hakan bai hana ta ci gaba da karatun ta ba.

 Kuma ita Hamida makarantar da take zuwa, ai sai zakakuran yara gwamnati take dauka. Ina ga tayi jarrabawa wajen hawa uku kafin ta samu shiga makaranatar.

 Shi ma kuma aminina watau Walid ai irin ta mazan da ita Hamidan ta ke zuwa nan yake zuwa shima”.

 Shi dai Abban na sa yana bayani, amma hanakalinsa ya rabu biyu. Yana saurarensa san nan yana tunanin anya a yanzu akwai mutum mai amana irin Abbansa. San nan ya sake wani tunanin. anya Abbansa ya san matsayinsa kuwa.

 Shi yanzu idan ma kasar nan ta kasa bashi aikin yi, ai yana da akalla kasashe bakwai da ke zawarcinsa, saboda binciken da yayi ya kawo ci gaba a harkan kera jiragen kasa.

 Ya san idan ya gaya masa yawan makudan kudin da kamafani Hitachi suka sayi binciken nasa kwakwalwarsa ba zata iya dauka ba.

 Bai masa wan nan bayanin ba, sai kawai yayi murmushi, ya ce “duk da haka Abba da kayi abin da ka ke so da kudin, saboda ba nawa bane. Kai na turawa kuma kai nake bukatar kayi amfani da su”.

 “A’a kar ka damu kanka, uban masu gida. Mu kam Alhamdu Lillah, muna cikin inuwar Ubangiji. Asrin mu kuma a rufe yake.

 Abin da kudin idan ka aiko har su Mai unguwa da Mallam Liman na ke dan samma wani abu. Har nan su Saleh mai shayi duk na kan basu wani abu daga ciki”.

 “Duk da haka Abba na so ace ka yi amfani da duk abin da na aiko maka”.

 “kar ka damu. Gobe idan Allah ya kaimu, sai muje bankin tare a cire ka mai da su taka ma’ajiyar”.

 Dariya Baffa ya dan yi, san nan yace “Abba wani ai ba ya jiye kudin wani. Kowa ya ajiye nasa. Saboda haka ba ruwana da kudin ka. Ka kashe abun ka yadda kake so.

 Danka zai ci gaba da daukar dawainiyarka da yardar Allah”.

 “Ka duba ka gani Baffa ba abin da zan yi da kudin nan. Kai kuwa zaka bukace su. Ka ga dai yanzu tun da an gama karatu sai azo a nemi abokiyar rayuwa”.

 Murmushi kawai Baffa yayi bai bashi amsa ba.

 Bayan sun isa gida, nan kuma suka tarad da kofar gidan cike da abokan arziki da makota da suka samu labarin dawowar Baffa suka zo masa sannu da zuwa.

 Nan kuma fa aka tsaya kofar gida ana gaisawa da kakabin canzawar Baffa. Mallam Liman yace “ba don kamarsu da marigayi ba ai ba za mu gane shi ba”.

 Shi dai murmushi kawai yake yi. Ya na nan kuwa a kofar gida har sai da aka kira azahar. Tare suka je masallaci. Bayan sun dawo ne ya samu mutane sun tsagaita ya samu shiga cikin gidan.

 A nan kuma ya tarar da gwaggonsa ta hada masa abinci kala kala. Ga kazar hausa da ta gasa masa. Ga tuwon shinkafa miyar danyar kubewa. Ga fura da nono an dama. Ga gurasa bandashe.

 Can kma gefe ga kafar sa an dora akan garwashi tana dahuwa a hankali. Shi kansa da ya kalli nau’in abincin da aka jere masa sai da ya dara. Yace “Gwaggo duk a ina zan zuba wan nan”.

 “daure kaci uban masu gida. Ba ka dawo da wuri ba balle in tamabaye ka me ka ke sha’awar ci. Sai na dafa duk abin da na san ka na so”.

 “Gwaggo bari in dan watsa ruwa sai inzo in zauna inci da kyau”. Ya na kokarin mikewa Abban ya dakatar da shi. San nan ya ce “zauna ka ci abincin sai muje in nema maka masauki. Akwai wani sabon masaukin baki da aka bude a can wajen GRA. An ce wajen na da kyau”.

 “Ko mai kyansa ba zai taba kai kyan gida mu ba”. Abban na kokarin yi masa bayani ya mike kawai ya dauki bokitin da ya gani a tsakar gidan ya nufi famfo da niyyar dibar ruwa.

 Hamida tayi sauri ta fito daga daki ta karbi bokitin ta cika da ruwa san nan ta kai bakin kofar bandakin. Ta sake dawowa ta dau wani ruwan ta shiga da shi. Ta sa tsintstiya da Dettol ta sake wanke bandakin duk da kalau yake.

 Ta shiga daki ta dauko sabon sabulu da tawul ta shiga da shi ta rataye masa a kusar bandakin. Yadda ba tayi masa Magana ba, shi ma bai tanka ma ta ba.

 Kafin ya fito kuwa ya tarar har da sabuwar katifa Mallam Jibo ya sayo ya kawo don a shimfida masa.

 Kannensa suka fito da duk kayan da yake cikin dakin sa na da in da Walida ya koma da zama. Suka dada sharo dakin, san nan suka shimfida masa sabuwar katifar.

 Shi dariya ma suke bashi sai kace wani bako na musamman. Wata karamar jaka ya dauka ya shiga ciki. Sai da ya shirya cikin kaya marasa nauyi, san nan ya fito daga dakin.  Walid na kokarin shiga da akwatunan da ya zo da su, amma ya hana shi.

 Ya nuna msa wani karamin akwati yace wan nan kawai zaka shigar min da shi, sauran bar su a nan. Gwaggon ya sa ta bude kayan san nan ya basu iznin kowa ya dauki abin da yake so.

 Fiye da rabi materials ne na mata da maza. Nan dai Abba da Gwaggo suka shiga rabawa. Abban ya ware da yawa yace “wadan nan a kaiwa mutan gidan Baffan ka Honourable”.

 Kallon Abban nasa yayi, san nan ya ce “akwai wasu kayan da za su zo sai a basu a ciki. A rabar da wadan nan kawai”

 Ai kuwa hatta da mutan unguwa sun san yaro dan albarka ya dawo daga tafiya. Honourable da iyalansa ba su shigo kano ba, saboda haka ba su da labarin dawowar Baffa.

 Kusan kwana sukayi suna hira shi da kannensa da kuma marikansu. Kowa yana kokarin bawa Baffa labarin bayan saduwa.

 Shi dai halinsa na rashin magana ya na nan. Sai dai yana biye da su. Lokaci lokaci ya kan katse su da ‘yar tambaya. Yaji dadi ganin Allah ya taimaka kannen nasa kowacce ta samu ilmi dai dai gwargwado.

 Duk da dai Zahra ba ta tona asirin zamanta gaba daya a wajen yayarta ba, amma duk kansu sun fahimci matsanancin halin da take ciki. Amma duk da haka sun yabawa tsayuwar mijin yayar ta ta akan harkar karatun ta.

 Ita kuwa Humaira sun fahimci zamanta a makaranta ya fi ko na gidan Barrister yawa, saboda da yadda ta gaya musu jadawalin karatun nata. In bata makarantar boko tana ta islamiyya. Idan su ma an yi hutu ta tafi makarantar da ake koyar da su zamantakewa da kuma kula da gidajensu.

 Hamida dai na zaune. Ta ki Magana sai murmushi da ke susbuce mata idan har ta hada ido da Baffa. Shi ma bai kulata ba.

 Sai can ya mike yace “oya kowa yaje ya kwanta, nima na gaji”.

 Bayan sun shiga cikin dakunansu. Ya tura Walid akan ya kirawo masa Hamida. Nan ma da ta zo ta kasa Magana sai wata tsabar kunyarsa da ta ke ji.

 Sai da suka dauki sama da awa suna hira da Walid, kafin suka yi bacci. Shi ya ke tambaya abubuwan da su ka shafi Hamidan.

 Washegari kuwa abu na farko da Baffa ya fara yi shine neman fili ko gida da zai saya. Mai unguwa ne ya samo masa wani filin mai kyan gaske kato da shi a awon gwamnati.

 Abban cike da murna yake fadin “kaga amfanin tarin da nayi. Muje banki a fitar da kudin a biya”.

 “Abba wancan kudin naka ne. kayi duk abin da ka ga dama da su. Ina da isassun kudin da zan biya wan nan filin”.

Bai fi sati biyu a gidan ba, hutun Humaira ya kare. Ita ma Zahra su Amira sun dawo. Ta shirya komawa Baffa ya raka ta da gargadin kar ta kuskura ta sanar da Amira dawowarsa.

 Hunaira ma ta shirya ta koma. Bayan nan gida yayi saura da ga shi sai Hamida da kuma Walid. Yana jin dadin hutun sa sosai. Ga kuma Hamidan sa da ta dauki ragamar kula da duk lamuransa. Kunyar da take ji dai ya barta da abarta.

 Sai dai idan yana son hira da ita ya kira ta a waya. A nan kuma sosai ta kan ware. Amma shi da ita face to face sam ta kasa. Ita kanta ta rasa wacce iriyar kunyarsa ta ke ji. Shi kuwa hakan na masa dadi saboda ya fuskanci ba shi kadai yake mafarkin abin da ya hasaso shine a zuciyar Hamidan duk da watakila ita kanta ba ta san dalilin take jin kunyar da take ba.

 Ibu n ya kira shi yake sanar da shi interest dinsa na son auren Humaira. Baffa ya nuna masa farin cikinsa amma ya nuna masa akwai marikiyarta, ita kuma zai so ta yanke lamarin auren Humaira, ko ba komai ita ta bata damar da ta samu rayuwa ingantacciya,

 Bayan ya sanar da Abbansu. Shi ma ya goya bayan su nemi yardar Barrister akan duk wani abu da ya shafi harkar Humaira.

 Sun dau niyyar zuwa Abuja tun da shima Baffa ya na son zuwa ya yi mata godiya, akan taimakon da ta yiwa kanwarsa.

 Ana cikin haka kuma sai ga sakon Email da ga  kamfanin Hitachi akan suna bukatar ya shiga cikin team din da za su yi aikin kera sabbin jiragen da za su yi wanda za su yi amfani da binciken da shi Baffan ya yi.

 Ya nuna musu kudirin da ya ke da shi na son koyarwa ko da na shekara biyu ne, saboda kudirin da ya ke da shi na kokarin zama Professor a fannin da yayi karatu, watau Mechatronics.

 Ya tattauna da University of Tokyo in da su ka nu na sha’awar son ya zo ya yi koyarwa a makarantarsu . Ya tattauna da duka su biyun. Sun kuma nuna babu matsala zai iya aikin da guraren biyu. Makaranta sau biyu a sati zai dinga shiga.

 Ya san idan ya sanar da Abbansa Makudan kudin da suka nuna za su biyashi, ba fahimta zai yi ba, saboda kwakwalwarsa ba zata taba hasaso masa akwai masu irin wan nan kudi a duniya ba.

 Ko kudin da ya dinga Tarawa a banki, ba don ya hadu da mai amana ba, ba sanin yawansu yayi ba. Shi lissafi idan ya haura dubu dari to kuwa ya bace masa ke nan.

 Ya dai nuna masa ya samu aiki a can inda yayi karatu. Ya yi murna amma ya nuna za su sake kewarsa.

 Kwantar masa da hankali yayi. Ya ce “Abban yanzu ba kamar da ba ne. ba zan sake wan na dogon zaman ba tare da na zo gareku ba”.

 Ya hau jirgi zuwa Abuja inda Ibu kuma ya hau nasa shima, domin su yi mahada a can.

Comments

Popular Posts