☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER 20 ☘️☘️☘️☘️☘️

           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/


CHAPTER TWENTY

 Tun da Zahra ta doshi gidan su tarinka jin wanin irin shauki a zuciyarta. Bayan motar Hajiyan Faruk ta faka a kofar gidan, ta dauki kimanin minti biyu zaune a cikin motar saboda ta na kokarin tsagaita kukan da ya tunkodo ma ta.

 Ba ta sanar da kowa zuwanta ba, saboda ita kanta ba ta da yakinin Hajiyar Faruk za ta barta ta kaiwa gidansu ziyara

 Gidan ya na nan kamar yadda ta barshi. Ko fenti ba a canza masa ba. Ta kalli makotan gidan na su in da Wabili ta gaya musu cewar a nan iyayenta suka zauna kafin su koma ga mahaliccinsu.

 Daurewa tayi ta fito ta nufi soron dan tsukakken gidan nasu, wanda take jin ya fiye mata fadar shugaban kasa a cikin zuciyarta.

 Da sallama ta shiga. Wabili na daki tana walaha, yayin da ta ga ‘yan mata guda biyu a tsakar gidan sun juya mata baya suna aikin awara.

 Juyowar da suka yi domin amsa sallamar ita ta saka su dukkansu uku suka saki ihu. Wabili ta yi sallama ta na addu’a ta ji ihunsu. Ba shiri ta yanke addu’ar ta fito daga daki a firgice.

 Amma abin da ta tarar a tsakar gidan ya sa ta kasa cewa komai. Humaira ta zo jiya da daddare. Yau kuma sai ga Zahran ta Allah ya kawo mata ita. Take ta fuskanci gabas ta sunkuya domin sujudar godiya ga Allah da ya nuna mata wan nan lokaci.

 Ta na dagowa daga sujudar, Zahra na fadawa jikinta domin tsananin murna. Gaba daya a nan tsakar gidan suka zube.

Dukkansu kuka suke ba uwar ba, ba ‘ya’yan ba. Wabilin ce ta yi saurin share hawayenta, san nan ta fara rarrashin yaran daga kukan da ita kanta ta san na farin ciki ne. 

 “Sannu Zahra zarar ‘ya’ya.

 “Gidan da duk ba zara.

 “Gidan ba zai zarra ba”, Wabili ce ta yi mata kirarin da ta kanyi mata lokacin suna gidan kafin Honourable ya tarwatsa su. Dada rungume ta ta yi wani hawaye na sake kwaranyowa daga idanunta.

 “To kuma kukan ai ya isa haka”

 Ta daure ta tsagaita kukan nata, san nan ta kalli Humaira ta ce “ashe kema kin zo”?

 “Nima jiya da daddare na zo”.

 “Amma ba ki ce zaki zo ba da ki ka kirani a waya last week”.

 Sai da Humaira ta share hawayen da ya sake zubo mata, san nan tace “the last time da na gaya miki zan zo in ga su Gwaggo, I can sense bacin ranki, shi yasa na ki fada miki”.

 Rungume juna suka dada yi.  Murna duk ta hana su maganar kirki. Gwaggo ce ta ce “ Hamida kira Abbanku a waya, ki ce masa yazo yau ‘ya’yansa sun hallara a gidansa kamar yadda ya dade ya na buri”.

 Da sauri ta shiga daki ta dauko wayar da Ibu abokin yayanta ya saya mata kwananki, saboda yanzu kusan kullum sai Baffa ya kirata su sha hirarsu. Idan a wayar Abban ya kirata, ba sa barinsu suyi hira sosai, sai Abban ya yi ta fada yana cewa “barnar kudi yake yi a wayar da suke yi ta shirme. Waya dai in an gaisa kaji lafiyar wanda ka kira ba shi ke nan ba, amma ai ba a mayar da ita ta hirar gari ba da zancen shirme”.

 Shi Abban bai san cewa ko tension din karatu ne ya yi wa Baffa yawa, idan ya kira Hamidansa suka dan yi hira sai yaji kansa ya washe.

 Wayar ta dauko ta kira Abban nasu. Sallama kawai ta iya yi, san nan ciki hanzari ta ce “Abbanmu ga Zahra itama tazo”.

 “Wacce Zahran”?

 “Abban Zahran gidan nan”.

 “Allahu Akbar”! shine abin da Mallam Jibo ya sake cewa.

 Ai kuwa da hanzarinsa ya nufo gidan na sa. Ya na yin sallama, Zahra ta nufe shi da gudu, ta zube a gabansa ta rike kafafunsa, sai kuka take yi.

 Dafa kanta kawai yana jera hamdala ga Ubangiji. “To kuma kukan na menene Zahra”?

 Muryarta na rawa, ta yi kokarin ta tsagaita kukan. Shi ya kama kafadarta ya dago ta daga durkuson da tayi.

 Har ga Allah bai taba jin kaunar Hamida sama da ta su Humaira ba. Shi a ganinsa ma kaunar da ya nuna musu ita Allah ya duba ya bashi nasa yaran har biyu bayan ya yanke kauna da samun da a rayuwarsa.

 Hannuwansa ta kama ta rike gam, kamar ance in ta sake shi guduwa zai yi. Sai da ta zauna a gefen tabarmara da ta tarar da su Hamida shi kuma ya zauna a kan turmin dake tsakar gidan, san nan ta samu sukunin gaishe shi.

 Tace “Abba na same ku lafiya”?

  “Lafiya kalau Zahra. Sai kewa da ki ka barmu da ita”.

 Wani hawayen ne ya sake kwaranyowa da ga idanun ta. Shine ya sake karfin hali yana cewa “to kuma ba shi ke nan ba. Tun da gamu mun hadu ai kuka kuma ya kare”.

 “Abba ji na ke kamar a mafarki. Wai yau gani ga ku na dawo gidanmu”.

 Wabili ce ta ce “ba ke kadai ba nima gani nake kamar mafarkin wai yau gani ga ‘yan biyu na. Allah ya kawo min uban masu gida lafiya, shi ma ya zo in ganshi”.

 Abba ne ya yi Magana yace “shi ma din kwantar da hankalinki. Yace mu zuba ido ko yaushe zai iya shigowa”.

 “Allah ya kawo shi lafiya”.

Duk kansu suka amsa da amin. Nan kuma Mallam Jibo ya shiga hidima. Su kuwa duk inda Wabili ta sa kafa suna biye da ita. Har rige rigen ba da labarai su ke yi.

 In ban da sallah ba a bin da ke raba su. Gwara Humaira tana zuwa lokaci lokaci, amma ita Zahra tun da ta bar gidan yau ne zuwanta na farko. Ita da kanta sai kallon yadda Humaira ta koma ta ke yi. Duk ta fi su wayewa. Zahra ta kasa daurewa ta ce “Humaira kalar ki irin ta ‘yan gayu ce”.

  Hamida ta ce “ni ma tun da ta shigo jiya na ke gaya mata ta zama ‘yar gayu. Sai kace baturiya”.

 “Ai ba za ku gane yadda Mama Barrister take kula da ni ba. Inda kika san ‘yarta haka ta mai da ni. Duk abin da za tayi wa su Fadil nima shi za tayi min. kuma ko tambayarta aka yi sai tace wai ni cousin dinsu ce.

 Mama Barrister is simply wonderful. Irinsu ba su da yawa a duniyar mu. Su dauki mutum ba dan uwansu ba, amma su mai da shi more like their own child. She is amazing”.

 “Shi ya sa na ce Ya Humaira kin zama ‘yar gayu. Magana daya biyu sai kin sa turanci”, in ji Hamida.

 “Ke ma I will work on your English. Daga yau da turanci nake son ki dinga min Magana, saboda kin kusa zama ‘yar university” in ji Humaira.

 “Ai nima din ba laifi. Sai dai ba zan kai ki ba. Amma kin sa Ya Baffa ya samo min wani site da yasa nake enhancing reading and writing skills dina. Yanzu idan ki ka shiga school din mu ba wanda ya kaini jin turanci”.

 “Zahra ce tace “confidence ne ba ki da shi sosai, saboda ba wanda zaku dinga yi a kai a kai. Mu kuwa can da yake kowa kabila ne dole sai turancin.

 Amma Daddyn su Amal ya hana mu broken irin nasu. Yace in dai za muyi speaking we should speak correct English”.

 Ita kuwa Wabili tana da ga gefe, idan ta ji sun tsarmo turancin nan wani dadi ne yake lullube ta. ‘Ya’yanta sun zama ‘yan gayu suma sun iya turanci.

 Kusan kwana suka yi a zaune su na hira, kowa na bada labarin gidansu. Walid ma kin tafiya dakin sa da ke soro ya yi. Nan ya makale cikin yayyensa ana chapter da shi.

 Bayan sun yi sallar Asuba, suka koma bacci yayin da Wabili ta kyale su taci gaba da kaye kayenta.

 Ba su farka ba sai misalin tara da rabi. A wan nan lokaci kuwa har Gwaggonsu ta kammala hada musu abin kari.

 Dukkaninsu sun hadu har da Abbansu suna karyawa a tsakar gida. Da ganin yanda fuskokinsu ke annuri ka san duk suna cike da farin ciki.

 Walid ya yi sa’a yau ranar hutun makaranta ce, saboda haka shi ma ya samu damar zama da ‘yan uwansa. Shne ya kalli Mallam Jibo yace “Abba yau ba za ka fita shago bane”?

 “Ka ta ba ganin mutum ya yi manya baki ya fita ya barsu? Ai yau ina nan tare da ‘yan biyun Gwaggo”

 Dariya suka saka gaba dayansu. Gwaggo na shirin Magana sallama daga soron kofar gidan ya katse su. Abban ne ya amsa. Dukkaninsu murmushi ya bayyana a fuskokinsu yayin da Ibarahim Awwal Salisu yaron da suka yi karatu tare da Baffa a Japan ya shigo gidan.

 Shi ya na gama masters ya taho ya bar Baffa a can. Ya samu aiki da wani kamfanin mai a Lagos.

 Duk da sun saba lokaci lokaci ya kan zo gai she su. Kuma kusan duk sakon da Baffa yakan aiko ta hannunsa ya ke aikowa.

 Da hanzari Abba ya mike domin taro shi, amma sai wata sallamar ta dakatar da shi. In da kasan irin turawan nan ruwa biyu haka ya zama. Ya shigo, jikinsa sanye da jeans shudi mai turuwa da kuma Tshirt ta Polo fara.

 Ba wani bane illa DR Ahmad Musa Ahmad wanda kusan duk abokansa da kuma na wajen aiki ke kira da AMA.

 Mallam Jibo kawai tsaye yayi ya kasa motsi. Ba abin da kwakwalwarsa ke wassafo masa sai amininsa Mallam Musa. Ba abin da ya raba Baffa da shi. Sai dai murjewar jiki da kuma alamar hutu da ta bayyana a jikinsa.

 Duk wanda ya san Mallam Musa ya na saurayi ya san tsaf kamarsa Baffa ya debo. Kamar kwabo da kwabo haka su ke.

 Zahra ce ta waiga domin ta ga abin da ya sanya Abbn nasu shiru. amma ita ma abin da ta gani ba shiri ta daka uban tsalle tayi kansa tana fadin “Ya Baffa ya dawo!”

 Sai a lokacin hankalinsu ya kai kan bakin da ke tsaye a kofar gidan. Ai kuwa gaba dayansu suka tashi da gudu suka nufi inda yayan na su ke tsaye. Ba dan ya na da karfi ba da sai sun kayar da shi kasa saboda wawar rungumar da su ka kai masa.

 Ba za ka iya tantance wanda ya fi farin ciki ba, tsakanin bakon da kuma ‘yan gidan da ya tarar.

 Baffa ne ya mayar da hankalinsa wajen Abban sa da ke tsaye yana hawaye. Janyewa ya yi daga rikon kannensa ya nufi wajen Abban nasa da hawayen da ke kwaranya sun ki tsayawa daga idaunsa.

 Tsugunnuwa yayi a gabansa ya na kokarin gai dashi. Abban ne ya dago shi san nan suka rungume juna cike da farin ciki.

 Wabili ma tana daga gefe fadi ta ke “Allah mun gode maka da ka dawo da uban masu gida lafiya”. Sakin Abban nasa ya yi ya nufe ta da sauri. Hannuwanta ya kama ya rike a cikin nasa yana fadin “Gwaggo na same ku lafiya”?

 “Lafiya kalau uban masu gida. Ka gan ka yadda ka koma bature. Wan nan ba domin hoton da kake turawa Hamida ta waya ba, ai da ba zamu gane ka ba”?

 Sai a lokacin ya lura da cewar bai ga Hamidan ba. Dube dube ya fara yi domin kokarin gano favourite kanwarsa. A bayan kyauren dakin Gwaggo ya hango ta, ta na lekensa.

 Murmushi kawai ya yi, ya yi kamar bai ganta ba. Ya mai da hanakalinsa wajen Mallam Jibo da ke tsaye har a wan nan lokacin yana share hawayen da ke malalowa a fuskarsa.

 “Gwaggo ina ga kamar Abba bai yi murna da zuwana ba, ko kuma na yi masa laifi”.

 Sai da ya share hawayen da ya kwaranyo ma sa san nan yace “Baffa murnar ce ta yi min yawa. Ka na ga murnar ganinka ta sa ko Magana na kasa yi”. Dariya kawai suka saka dukkansu.

 Humaira ce ta mai da hankalinta wajen da Ibrahim abokin yayansu ke tsaye. Ga dukkan alamu kowa na gidan ya manta da shi a wajen. Karamar kujera ta dauko ta ajiye masa, san na ta ce “yi hakuri murnar ganin Ya Baffa ta sa mun kasa yi wa bako abin da ya kamata”.

 Murmushi ya yi. Sai da ya zauna a kujerar san nan ya amsa mata da cewar”kar ki damu ni ba bako ba ne. kuma duk da ba ku yi min abin da ya kamata a yiwa bako ba. Bakon ya yi wa kansa abin da ya kamata”.

 Gyada kanta tayi alamar ya daure mata kai da kalamansa. San nan tace “I don’t get you”.

 “Kar ki damu you will understand”, shi ma ya amsa mata.

 Wabili ce ta hada musu abinci a nan kan tabarmar da suka tashi, ya yin da yaran suka shimfida wata a kofar dakin Abbansu.

 Wani katon kofi Baffa ya dauka ya cika da koka, wanda da jin kamshinsa kasan da sabuwar gasara aka yi shi. Ga kuma kamshin yaji ya na tashi. Da ya kafa kai sai da ya shanye tas san nan ya ajiye.

 Duk dariya suke masa ganin irin shan da ya yi wa kokon. Su dai kannensa sai indomie suka dafa, saboda sai da Baffa da Ibu suka tashi da kosan da Gwaggonsu ta zuba musu.

 Ita kuwa Hamida tana makale a bayan kofa tana leken Baffa. Ba ta san mai ya sanya ta kasa hada ido da shi ba. Tun da yayi sallama taji wata irin faduwar gaba da bata taba jin irinta ba.

 Hakan ya sa ta boye ta kasa isa inda Baffa ya ke. Idan ba ta manta ba, ko wancan satin sun dade suna waya, amma bai sanar da ita zai dawo ba.

 Lekowa ta sake yi ta kalle shi. Take taji bugun zuciyarta ya karu. Ya kan aiko da hotunansa, amma kyansa ya bata mamaki. Mutum sai ka ce bature.

 Shi ma dan fisgar ido ya yi sai yaga har yanzu ta na lekensa. Murmushi ya sake yi ya yi kamar bai ganta ba. Ya maida hankalinsa kan hirar da suke yi shi da Ibu da kuma Abbansa.

 Shi da Ibu da kuma Abbansa suka koma filin jirgin sama domin debo kayansa, wanda ya kasa hakura saboda an ce kofar cargon jirgin ta samu matsala, kuma zai dau awa kafin a iya bude ta. Hakan ya sa ya kasa hakura ya taho gida.

 Ibu ya hau jirgi domin zuwa Abuja yayin da shi kuma da Abban suka kamo hanyar gida.

Comments

Popular Posts