☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER 19 ☘️☘️☘️☘️☘️

           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER NINETEEN

 Kamar yadda Zahra ta gama secondary haka ma Humaira ta gama a makarantar Inspire da ke garin Abuja. Tabbas Barrister ta rike amana kamar yadda ta fada zatayi da farko.

 Ko da Dr Farida ta tsokane ta da cewar “ta rike Humaira kamar ‘yarta ta cikinta”, sai ta amsa mata da cewar “dangantaka a zuci take ba a jini ba. Jinta nake yi kamar ni na haifeta. Yarinyar abar tausayi ce. Ga maraici ga zaluncin wadanda ya kamata su kula da ita”.

 Bayan sun gama jarrabawa, Barrister ta saka ta a wata makaranta ta tsawon wata shida inda ake koyar da girke girke, gyaran gida da kuma na jiki, mai suna ‘Home Management Training Institute.

 In da kasan masu aiki haka ake koyar da su. Saboda a fadar Barrister ta ce “kuskuren da iyayen yanzu ke yi shine koyawa yara mata yanda zasu rike kansu ko da miji ya gaza, amma basa koyar dasu yadda zasu rike mijin da gidan har su hana shi gazawa”.

 Tun da ta tafi zuwanta Kano bai fi sau uku ba, saboda Barrister ta tsagaita zuwan na ta saboda kar a samu akasi su hadu da Baffanta Honourable.

 Karatun kam ta kwaso iya dibanta. Da Arabin da bokon. Ga kuma wayewa da ta dada yi. Duk da yaran Barrister na debe mata kewa, amma hakan bai sa taji ta daina kewar kannenta watau Zahra, Hamida, Walida da kuma Abbanta da Gwaggon ta ba.

 Sa’ar ta ma daya kusan duk sati sai sun yi waya da su. Haka nan yayanta da ke Japan shi ma ya kan kirata lokaci lokaci su gaisa.

 Kamarsu daya da Zahra, sai dai murjewar jiki da kuma daukan kwalliya da ta fi Zahran. Don ma dai Zahran kyakkayawa ce da wahalar da take sha a wajen yayarta da ya dusassar da ita.

 Saboda ko kwance kayanta ba ta iya dauka ta bata, saboda wai a ganinta ba ta kai matsayin saka suturar da ita ta sa ta cire ba.

 Za ta iya sayawa Amal da Sadik riga kwaya dai dai ta naira dubu ashirin, amma Zahra ba ta kai matsayin daurar atamfar dubu biyar ba.

 Kuma ko Faruk ne da kansa ya saya ya bayar a bata, sai dai ta aikawa Sofi ko wani daga cikin ‘ya’yan kanwar mamanta, amma ba mai wahala mata ba.

 A bangaren Hamida ita ma ma sha Allah. Ita kam duk ta kere su ma saboda ita kuma wata irin black beuty ce. Ta fi su dan duhu, amma fa kyakkaywa ce ta nunawa sa’a.

 Tun tana karama idan sun tsokane ta da cewar ‘yar baka, sai Ya Baffa yace ita African Queen ce. Tana da wani irin kyau that last for a long time. Irin su ne matan da ake yi wa lakabi da’ beni ba kya tsufa’.

 Gashin da suke takama itama tana da irin sa. Ita da Walid suna shekararsu ta karshe inda kullum Ya Baffan ta ke jaddada ma ta da ta dage ta ci jarrabawa da kyau saboda lokacin da zai tafi da ita in da yake da zama ya yi.

 Dariya kawai ta kan yi saboda sanin tsokanarta ya ke yi. Dariya kawai tayi san nan ta ce “Ya Baffa na fa girma da wan nan wayon”.

 “Iye kai ashe Hamidana ta girma, sai aure ke nan”?

 Kunya ce ta kamata kamar ya na kallonta. Ta ce “kai Ya Baffa. Ga su Yaya twins nan. Ni me na isa”.

 “Su ai ba su ce min sun girma ba. Ke ce ki ka fadi da kanki kin girma. Na dauka kuma a addinin mu idan yarinya ta girma sai aure”?

 Cikin son bagarar da zancen ta ce “yaushe zaka dawo ne? duk mun kagara mu ganka”.

 “Its going to be a surprise. Ku ci gaba da zuba ido. Amma very soon za ku ganni”.

 Haka rayuwarsu take tafiya. Kusan shekaru goma, Honourable bai sa Baffa a idonsa ba, bai kuma san in da ya ke ba, amma bai taba tambayar yaji ko a ina yake ba.

 In da kasan ma ya manta da shi a danginsa haka ya yi. Sai Humaira ya ke bibiya saboda a tunaninsa da na matarsa ta samu duniya tayi fatali da su.

 Har biya ya yi da a sa masa ido ko za a ga ta zo gidan, tun da shi ba a gari yake ba.

 Amma cikin hukuncin Ubangiji saidawan nasa bai taba ganin zuwanta ba.

 Baffa kuwa ya kammala karatunsa cikin nasara. Haka zalika binciken da yayi karatun nasa a kai, kamfanin Hitachi ta sayi binciken a makudan kudi, san nan suka bashi hanun jari a sabbin jiragen da zasu kera wanda za suyi amfani da binciken da Baffan yayi, domin karawa jiragen yawan taragu san nan kuma su ci gaba da tafiya a gudunsu na asali, ba tare da jirgen ya tintsire ba.

 Abokinsa kuwa Ibarahim Salisu Awwal wanda suka yi karatu tare, shi tun kammala degreen sa na biyu ya dawo gida. Kuma shi ya kan tura domin ya kula masa da mutan gidansu.

 Ba yanda Ibu kamar yadda su AMA watau Baffa suke kiransa, bai yi da Abba ba domin ya dinga amfani da kudin da yake aiko musu, amma sam yaki.

 Shi dai tari yake yiwa Baffa idan ya dawo ya samu ya sai dan gida ya kama sana’a yayi aure idan har aikin gwamnati bai samu ba.

 Bayan nan ya rokin Ibu da kar ya sanar wa da Baffa kudiransa, saboda ya san ran sa ba zai so hakan ba.

 Lallaba rayuwarsa ya ci gaba da yi. Shi bai rike Baffa don ya girma ya biya shi hidimar da ya yi masa yana yaro ba. Ya yi ne kawai saboda zumuncin Allah da kuma kaunar da yake yi wa amininsa Mallam Musa watau mahaifin Baffa.

 Ga yaransa Hamida da Walid suna shekarar su ta karshe a secondary. Humaira da Zahra sun gama. Duk da dai saduwa ta yi wuya a tsakaninsu, amma ya san duk abin da suke ciki saboda ‘yar wayar nan ta zamani mai tamakawa wajen sada zumunci.

 A wan nan hutun ne ma da Faruk da Amira za su USA, ya yi niyya akan yaransa a wajen Hajiyarsa za su yi hutu. Ita ta shirya barinsu a gida kamar yadda ta saba. Amma suna isa Lagos Airport ba tare da sanin Amira ba, ya bugawa drivensa waya akan ya kai su airport ya saya musu ticket na zuwa Abuja.

 Daga nan kuma suka hau wani zuwa Kano. In da kasan mai zuwa Hajji haka, Zahra ta dinga ji, ganin yau dai gata a kano. Ba ta da tabbacin Hajiyar Faruk za ta barta ta ziyarci gidansu, amma jinta jiha daya da su, sai take ji kamar tana tafiya zuwa wani gari mai nisa, sai kuma ta kusa isa, in da za ta.

 Hajiyan ba karamin murna tayi ba da ganin yaran da kuma uwar goyonsu watau Zahra. Kusan duk shekara sukan zo mata hutun dogon zango, amma ba sa zuwa da Zahra saboda in dai ba Amira ce za ta Abuja su je tare ba, ko kuma in tana Warri su zauna tare.

 Saboda ko allura ba za ta iya matsarwa ba idan Zahra ba ta nan. Ko kayan mai gidan Zahra ce ta ke jerawa, saboda haka shima duk abin da ya ke nema ba ya bata lokacinsa wajen tamabayar matar.

 Saboda ya san ko ya tamabayeta, Zahran dai zata tambaya. Hakan ya sa ya gwammace ya tambayi Zahran kai tsaye.

 Ko baki zai yi, ita zai kira ya sanarwa. Idan wani appointment ya ke da shi yana tsoron kar ya manta, Zahra zai fadawa ta tuna masa. Shi yasa yake tsokanarta da sunan ‘organiser’.

 Washegari kuwa Hajiyar tace ta shirya driver ya kaita ta gaisa da mutan gida da rabonta da su ta kai kusan shekara hudu.

 Ta shirya ta fito, Hajiya ganinta cikin wani yalolon material ta ce “ke kuwa zaki gida ba sai ki yi shiga mai kyau ba. Amma kya dauko wan nan kaya ba kyan gani ki saka”.

 Murmushi kawai tayi, saboda ba ta san me zata ce da Hajiyan ba, da ba ta san cewa kure adaka tayi da wan nan yadin ba.

 Wata kodaddiyar riga ta dauko ta karamar atamfa za ta saka. Hajiyan ta sake cewa “to ai gwanda na farkon da wan nan din”.

 Kafin ta sake magan ta ce “mu ga kayan naki”

 Tun da ta bude ‘yar tsumman jakar da ta zo da ita take Allah wadai da halin danta da kuma na surukarta na yanayin da suke barin yarinyar mutane a ciki..

 Kanwar faruk mai suna Zainab wacce take ganin zasuyi kai daya ta sa ta ware mata suturu masu dan dama da ga kayanta ta bata.

 Kasa daurewa tayi sai da ta bugawa Faruk waya tana masa fadan yadda suke barin Zahra ba suturar kirki, bayan su ‘ya’yansu kowa ya ga na su kayan yasan yara ne ‘yan gata.

 Hakuri ya bata. Tun da shi dai Allah ya sani duk sanda ya ba da kudi a saya wa su Amal kaya sai ya bada kwatankwacinsa na Zahra.

 Bayan nan ta sake cewa “kuma ta kwashi shekaru tana zaune daku, amma ban ga tsarabar da kuka ware ta kai gidansu ba”?

Hajiya ba ta san cewar uwar dakinta ba ma ta san ta taho Kano ba, saboda a Warri ta barta.

Hakuri ya bawa Hajiya san nan ya roke ta arzikin ta saya mata duk abin da ya dace domin ta kaiwa mutan gidansu tsaraba.

 Tafiyar dai sai daga ta a kayi zuwa washe gari. Saboda zaunar da ita Hajiyan tayi ta tambayeta adadin mutanen gidansu. Kasuwa suka je kuwa ta saki naira ta sai mata tsaraba rankatakaf, dangin sutura, abinci, kayan masarufi. da kuma ababen bukatun yau da kullum.

 Washegari kuwa cike da zumudi ta tunkari gidansu. Burinta a ce har da Humaira ma ta zo. Saboda ta samu ganin kowa.

Comments

Popular Posts