☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER 18 ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER EIGHTEEN

 A cikin shekara uku abubuwa da dama sun faru. Ciki kuwa har da kammala karatun Baffa a degree sa na uku. Yayin da Zahra da Humaira suka kammala karatun secondary.

 Humaira da Zahra kamarsu daya. Duk wanda ya san mahaifiyarsu ya san kyawunta suka daukko. Mafiya yawan Fulani falgore bakake ne, amma kyawawan gaske da kuma gashinsu yalo yalo. To suma haka suka kasance, sai kuma suka daukko farin mahaifinsu. Haka ya sanya kalarsu ta zama wata irin creamy.

 Suna da matsaikacin tsawo da kuma dirarren jiki mai daukar hankali. Ga kuma gashinsu wanda akewa lakabi da ‘saloon huta’. Baki sidik ga tsawo ga laushi.

 Zahra ce ta shiga tashin hankali saboda tun da Saddam ya kyallara ido ya ganta a wani hutu da suka je Abuja ita da Amira ya shiga takura mata.

 Tana kokarin goce masa amma shi har ya sanar da Mommy ya samu matar aure. Yana fada kuwa ta rufe shi da masifa akan mai zai yi da wan nan matsiyaciyar yarinyar mai kashin tsiya.

 Dariya yayi, san nan yace “kaji mommy da wani zance. Ina fatan ba irin auren da kika lallaba ki ka yi ma Amir nima irinsa za ki yi min ba”?

 “Kai ba na son rashin kunya. Wanne irin auren aka yi ma Amir din”?

 “Mommy da kiga ruwan kudi za a kawo miki kayan daki da gara mai yawan gaske ki ka mika shi, aka baki yarinya ashe drug addict ce. Ba ki samu kin kankaro naki yaron ba ta sake dulmiyar da shi”.

 Kwashewa su ka yi da dariya shi da Amira. Sofi ce tace “see the kettle calling the pot black. Da Amir da yarinyar duk ba abu daya ba ne”.

 Su dama haka suke hira a tsakaninsu ba respect ko kadan. Duk abin da yaran suka ga dama haka zasu kwaba wa iyayen wai su wayayyu. Ga wata dabi’ar banza da suka dauka. Ana zaune kalau sai kaga sun hada party a cikin gidan a gaban iyayensu. Kowa ya gayyato jinsinsa a cashe da suturun da suka ga damar sawa.

 In ban da Amira ba wani mai karatun kirki a gidan. Amma abu kadan kaji sunce maka ‘bakauye’.

 Ran nan wata mai tuwonsu da ta ga sun hada party da sunan wai Sofi ta shekara sha bakawai. Ta sha wato yaloluwar riga da da kadan ta haura gwiwarta. Su kuma yayyun maza kowa da three quarter da armless.

 Aka dauko DJ, musamman ta gayyato kawayenta suma suka gayyato abokansu. Mommy ta shiga cikinsu ana ta sharholiya ita ala dole ga wayayyayiyar mace da ta ke son ‘ya’yanta.

 Mai aikin nasu mai suna Talai ta kalle su takaici ya ishe ta sai kace ba ‘ya’yan musulmi ba ta kalli mai gadin su tace “wadan nan da a arna Allah ya hallito su, ban san iya badalar da za suyi ba”.

 To su haka rayuwarsu take. Amir ya taba yin aure irin na nunawa sa’a. Aka kashe makudan kudi wajen lefe da kayan daki. Ita ma yarinyar ‘yar masu kudi ce. Ashe ‘yar kwaya ce ba su sani ba.

 Ita Mommy tana murna ta samu gidan masu kudi zata dau danta da ba shi da takarda ko ta tsire ta caka musu. Ashe suma haka ne abin a wajensu. Yarinyar ta gagare su. Suka dau dukiya suka lafta suka maka musu.

 Aure bai yi sati ba aka fara samun matsala. Sun hadu a club amma shi Amir so yake ita ta koyi zaman gida shi kuma ya ci gaba da chilling a club din. Kafin dai wata uku an yi sakin farko. Duka duka auren watansa takwas ya kare gaba daya. Ta na fargawa taga tana da ciki wata uku taje ta zubar da shi ta koma harkarta, shi ma ya koma tasa.

 Kuma a hakan ba su rabu da juna ba. Aure ya kare amma sun ci gaba da mu’amala. Haka suke cikin wan nan jagwalgwalon rayuwa. Kuma duk su biyun ba wanda ya isa da su. Shedancin su suke bugawa.

 To shi kuma Saddam ya ga nutsattsiyar kanwarsa ya nuna yana so, Mommy ta nuna ita yarinyar ba ta kai mizanin auren danta ba.

 Ta manta ko ba komai yarinyar ta fishi, tunda ta samu ta rubuta jarrabawar secondary jiran sakamako take yi. A Qur’ani ma kuwa ta kusa sauka, amma ita ce a  raine saboda ba ta da uba mai kudi.

 Nata ‘ya’yan da ma ba’a dora su a tsanin karatun addini ba. Da suna Kano suna dan tsakura, amma tun da suka dawo Abuja sai suka zubar suka rungumi boko. To shi din ma gashi ya ki samuwa. Gasu nan ganda gandan samari, amma ba mai aikin tasi. Sai dai kullum abin da uban ya rarumo a gararumar siyasa ya basu.

 Ga kuma rayuwa ta karya da suka daukarwa kansu.

 Zahra idan taga tabarar da Sofi take yi har mamaki take bata. Ta fita girman jiki ta girme ta da kusan wata uku, amma inda ka san ‘yar shekara takwas haka take tabara. Tun da dai har a wan nan lokaci ba ta daina kuka da shure shure ba.

 Ita kuwa Zahra ba duka matar aure ce za ta iya rabin abin da take yi ba. Kuma in ma Abujan suka zo hutun dorawa take daga inda ta bari a gidansu.

 A wan nan rana ma tana kitchen saboda mutan gidan yau duk sun ce sakwara zasu ci da edaka ekong. Haka kuwa ta kuge. Bayan ta gama hada miyar ta shiga daka sakwarar. Ta na yi ta na nade ta a leda tana jerawa a cikin food flask.

 Ita da ‘ya’yanta ne a kitchen din, saboda ba su saba da kowa ba sama da ita. Duk inda tayi suna biye da ita. Tana aikin ta suna biya karatun su na Qur’ani. Haka ta sabar musu. Duk sanda su kayi tafiya ta kan samu lokaci su yi muraja’a saboda kar hadda ta zube.

 Ta na tsaye gefen turmi da take daka, ba ta yi aune ba taji an rungumeta ta baya. A firgice ta juyo domin ganin wane marar hankalin ne ke mata wan nan tabargaza.

 “Hello sweet heart. Me kike dafa min ne”?

 Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta hade fuskarta kamar ba ita ce ke karatu cikin fara’a da su Amal ba.

 Zama yayi akan worktop na kitchen din. Ya bude flask din miyar. Wani daddadn kamshi ya bugi hancinsa. “Kai yasin na more da mace. Ga kyau ga iya girki ga tsafta”.

 Ita dai ba ta ce masa kala ba sai ma dada gintse fuska da tayi ta na mai kokarin ci gaba da goge wajen da tayi aiki.

 Dan zaman da tayi da Ogadion watau kukun Amira na Warri, ta koyi dabarun gyaran gida da yawa. Misali in dai tana girki to kuwa bata taba bari wanke wanke ya taru. Duk abin da tayi amfani dashi a take za ta wanke.

 Haka zalika idan zata dafa kamar nama, bata lafta masa ruwa. Amma da ya tafaso za ta rage wutar ta barshi ya dahu a hankali. Yin hakan kuma zai bata damar yin wani aiki kamar shara ko mopping ko wankin ban daki ba tare da dahuwarta ta kone ba.

 Hakan ma sai yake karawa girkinta armashi, saboda zai dahu  a hankali duk kayan hadin da ta zuba su shiga cikin dahuwar sosai.

 Sanin yadda zata tsara ayyukan gidan kuma ta samarwa kanta lokacin karatu shi ya ke bata damar yin ayyuka da dama a lokaci guda.

  Banza Zahra ta yi da shi ta ci gaba da tattare wajen da ta dan bata. Plate ya dauko ya dinga bin ta daf da daf a kan lallai shi sai ta zuba masa abinci.

 Kin kula shi tayi. Ba tayi aune ba sai jinsa kawai tayi yana kokarin rungomata a jikinsa. Ba tare da wani dogon tunani ba ta daga hannuta, ta wanka mishi mari.

 Saukar marin a fuskarsa yayi dai dai da shigowar Sofi kitchen din. Wacce itama shigowa tayi ta gani ko abincin ya hadu.

 “kan uban can! Saddam din ki ka mara. Ai kuwa zaki gane kurenki”.

 A guje ta fice da ga kitchen din tana kwallawa Mommy kira. Ita ma a zafafe ta fito saboda taji kiran ba na lafiya bane.

 “Mommy kizo wan nan Zahran ce ta mari Saddam”.

 “Mari a mare? Ai kuwa yau za ta ci ubanta a gidan nan”.

 Ta na isa kitchen din kuwa ba tayi wata wata ba ta dauke ta da zafafan maruka har guda uku. Take fuskarta kuwa ta tashi, shatun yatsun Mommy suka fito radau a fuskarta.

 Amal da Sadik ganin abin da aka yiwa Anti Lalan su, sai su ka yi kanta suka riketa suna kuka. Mommy kuwa ba ta damu da kukan nasu ba sai zazzaga masifa take yi. Sai fadi take “ke dan ubanki ashe har kina jin kin kai matsayin da zaki saka hannu ki daki ko da Karen gidan nan ne.

To kuwa ki tabbatar kin yi na karshe. Na rantse da Allah idan kika sake ko da gigin hararar Saddam ne, jikin ki ne zai gaya miki”.

 Ita dai bata tanka ba, sai rungome Amal da Sadik da tayi tana gursheken kuka.

 “Sakarsu dan ubanki” Mommy ta fada tana mai fisge yaran daga jikinta.

 Sautin kukan nasu shi ya fito da uwarsu daga daki. Itama nan aka taru da ita aka gama tsittsigewa Zahra.

 Ita dai ba ta ce komai ba in ban da kuka da takeyi. Bayan sun koma falo Saddam ya kalli Mommy yace “ni dai kawai ki gaya wa Daddy ya daura mana aure da ita”.

 “Banza kai in ban da ka yar da kanka har wan nan kotsin ta isa ta wulakanta ka wai har da mari, amma still ka na son ta”? Sofi ta ce da shi.

 “Da ta mare nin ba gashi ta ji a jikinta ba. Kawai ni Mommy ki sa a daura mana aure”.

 Ita kam haushi ya hana ta Magana.

 A daki kuwa Zahra tafi awa biyu tana kukan takaicin a bin da aka yi mata. Nan kuma Amal da Sadik suka zage suna rarrashinta suma sun a tayata kukan.

 Ganin haka ne ya saka ta share nata hawaye ta kamo su ta rungume a jikinta tana rarrashinsu.

 Ana gama wan nan da daddare sai ga Saddam ya shigo dakin da take. Yana kokarin kamata ta dauko fitilar gefen gado. Tace “kana sake matsowa kusa da ni na rantse da Allah sai nayi maka rotse sai dai idan kashe ni zakuyi a gidan ku taru ku kashe ni”.

 Ganin haka ya kuma kalli cikin idonta ya ga ko alamar tsoro babu, ya kuma san tabbas ba karamin abu bane ta kwada masa fitilar kamar yadda ta fada.

 “Aikin banza don ma kin yi sa’a na ce ina sonki. Shine ki ke min wulkanci. Daddy yana dawowa zan sa a daura mana aure in ga abin da zaki iya yi”.

 “Wan nan kuma daban zan kuma dau kaddarar da Allah ya dora min. Amma ba zan zauna ina kallo ka wulakanta ni ba. Ni da kai za muyi zaman yi min in maka”.

 Shi kansa ya kasa gane wane irin taurin zuciya yarinyar ta ke da shi. Tana da taurin kai fiye da tsammanin mutum. Kusan ba abin da ke firgita ta. Amma ko irin cin mutunci da Mommy ta yi mata dazu ya isa a ce ta tsorata da shi, amma sam hakan bai wani tabata ba.

 Cike da borin kunya ya juya ya fice daga dakin. Da Daddy ya dawo suka sanar da shi cewar Zahra tayiwa Saddam rashin kunya. Sofi zata dora da bayani, shi Saddam din da kansa yace “Ni daddy ba so nake ka rama min ba, kawai ka aura min ita. Ina son ta haka”.

 Amira tayi saurin cafewa tace “idan aka aura maka ita ni kuma in yi yaya? Waye zai ci gaba da yi min aikin da take yi min”?

 “Ai wan nan ba matsala. Ki bamu side a gidanki sai ta ci gaba da kula da gidanki da yaranki yadda ki ke so”.

 Sofi ce tace “wai Daddy har yanzu ba a gano inda Humairan take ba”?

 “Ina aka ganta. Shegiyar yarinya mai mugun hali. Ta samu arziki tayiwa kowa bulunbukwui. In samu in ganta ma abin ya gagara. Ga shi shi kuma Senator mun raba inuwa da shi, na san ba wata alfarma zai iya yi min ba.

 Har can Abujan inda a kace sun koma naje, amma na kasa sanin inda take. Shi gidan nasa ance ba a nan take da zama ba. Na kuma rasa wanda zai gaya min inda take”.

 Ya juya ya kalli Mommy, yace “ke baki samu bayanin komai ba a wajen matar Jibon”?

 “Wan nan bafullatanar ce za a samu wani bayani a wajenta. Har tsorata ta na yi amma ko gezau. Hasalima ta dage ita tun ranar da na dau yarinya ba ta kara ganinta ba.

 Da na tsorata ta da nuna mata cewar zan daukko mata police har sai ta bayyana ta ta kalle ni cikin idona tace ‘wacce na sa police suka kama da farko saboda kala mata satar sarka da nayi an gano dana ne ya saci kayan. Itama wan nan idan na kai kara allura zata tono garma, saboda za a gano mu muka sace ta”.

 “Ashe ita ma taurine rai ne da ita irin na mijinta. Ba abin da ke tsorata su”

 “To ko dai shi Senator Alkassim din zaka yi kararsa ya fito maka da ‘yarka”?

 “Ashe baki da hankali ban sani ba. Mutumin da nake lallaba shi ya taimaka min da harkar siyasa ta shine zaki ce in yi kararsa”?

 “Wai da na ga ba jamiyar ku daya ba yanzu”?

 “A wajenku ba masu zabe. Mu kuwa a can sama duk jam’iyar mu daya. Ku akewa yiwa wasa da hankali, amma mu duk daya muke”.

 Saddam ne ya sake cewa “wai dama yanzu Daddy da gaske duk wanda kake zagi a media kawai bula ce”?

 “Babbar bula ma kuwa. Kana biya na gobe zan canza kalmomi na a kan ka” Daddy ya fada yana mai mikewa da nufin shiga dakinsa.

 “Wai Amir bai dawo bane” ya tambayi Mommy.

 Sofi ce ta ce “amma dai Daddy akwai ka da wauta. Kai ma ka san Amir ba zai dawo ba har sai dollars din da ya diba a dakinka sun kare. Kuma ina ga wan nan karon he is lucky don ya diba da dan dama”.

 Dariya kawai suka kwashe da ita na maganar da Sofi ta yaba wa mahaifinta. Haka nan suke rayuwarsu ba wanda ke respecting wani. Duk maganar da kowa yaga dama haka zai gaya wa dan uwansa.

 Idan kuwa fada ya shiga tsakaninsu. In da kasan ‘yan daba haka su ke yinsa. Zage zage da doke doke musamman tsakanin Saddam da Amir ba a Magana.

 Ita dai Sofi ba ta dukan yayyenta, amma fa masu aiki komai girmanka, ka bata mata rai ba wani abu bane ta daga hannu ta shararawa mutum mari. Ba kuma abin da iyayen za su ce mata.

 Kuma su duk nan wayewa ce ta kawo haka. Ga wayayyu nan a Abuja da suka dage wajen bawa ‘ya’yansu ilmin Arabi da na boko, amma su sai bankaura kawai suke yi kuma a dole ganinsu sune suke ‘yan gayu.

 Amir dai halinsa sai godiyar Allah. Saboda lalacewar tasa kullum dada gaba take yi. Da farko clubs din masu dan aji yake zuwa, amma yanzu shine local settings irin su marrabar jos.

 Ga su dama su tashin da aka yi musu komai su ka ga dama shi sukeyi ba wanda ya isa ya kwabe su.

 To a cikin wan nan kwamacala Zahra ta samu kanta. Amma furgaginsu bai tsorata ta ba. Ta shawa kanta alwashi za ta yi duk iya kokarinta ta ga kwatar wa kanta ‘yanci.

 Shi kuwa Saddam ya dai ci gaba da bibiyarta, amma tun threat din da tayi masa ya ke shayin kai hannunsa jikinta. Burinsa Daddy ya dawo daga rallyn da suka tafi da shugaban kasa kawai a aura masa ita.

 Yayin da a daya bangaren ita kuma Amira ba ta son ya aureta, saboda kwata kwata ba ta tsara zata barta tayi aure kwana kusa ba saboda hidimar gidanta da ta daukar mata.

   Shi ne ma dalilin da ta barta take karatu, saboda ko da Faruk zai takura ta aurar da ita zata nuna masa ta na burin ta yi karatu mai kyau. A lissafinta ba tayi niyyar rabuwa da ita ba sai yaranta sun tafi secondary.

 Shi ma din in so samu ne ta samu ko da driver gidanta tun da bahaushe ne ya aure ta ko da a matarsa ta biyu. Hakan zai bata damar ci gaba da morar Zahra.

Comments

Popular Posts