☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER 17 ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER SEVENTEEN

  Zahra kuwa ta bi yayarta Amira, Warri. Da mijin da yaransu a jirgi suka tafi, yayin da aka hada Zahra da driver da kuma fagon kayansu. Daga ita sai a driver nan amma ba bu abin da ya damesu.

 Kwana suka yi suna tafiya. Tun da ga Kano take Kuka har zuwa garin. Tafiyar kusan awa ashirin a mota. Sai dai su tsaya driver ya saya musu abinci, wanda ita kam damuwa bata barta ta ci abin kirki ba.

 Idan ta tuna ba irin magiyar da ba tayi wa Momi ba akan ta barta ta je ta yi wa mutan gidansu sallam, amma sam aka hana ta. Lokacin da suka isa a galabaice ta shiga gidan. Dan kyakkyawan madaidaicin gidan bai dauki hankalinta ko kadan ba.

 Kamar jikakkun kayan wanki haka ta zube a falon. Mai kula da gidan da kuma girki wani kabila ne mai suna Ogadion. Shi ya fara kokarin taimaka mata kafin masu gidan su karaso, saboda da ga Kano sun hau jirgi zuwa Abuja, in da daga nan suka hau karamin jirgi domin karasawa Warri.

 Driver office shi yaje dauko su, wanda a matsanancin yanayi suka shigo suka tarar da ita.

“Who is she”? itace tambayar da Faruk, mijin Amira ya fara yi wa matarsa a lokacin da ya ganta.

 “Ba na ce maka Iam bringing someone from home ba”, ita ma ta amsa ma sa.

 “And kuma sai kiga dacewar ki dora karamar yarinya a mota. Me ya sa ba ki sai ticket da ita ba”?

 “Mommy ce tace kar mu bata ta. Mu jira mu ga halinta tukunna”.

 Har zai kara Magana sai kawai yayi shiru ya dauki wayarsa ya kira wani daga staff clinic dinsu. Shi yazo ya dubata ya bata ORT ya kuma basu shawarar su barta ta huta.

 Shi da kansa ya tilasta ta, ta sha tea da dan bread kadan, saboda driver ya sanar da shi bata ci abincin kirki ba a hanya.

 Ita kuwa Amira har ta fara sukewa da halin Zahra. Ita da ta samu ta dauko mai taimaka mata, kuma ita zata bige da kula da ita.

 Allah dai ya taimaki Zahra, saboda kwananta biyu ta murmure sai  dai kewar gida da ke damunta.

 To amma fa iya hutun da ta samu tayi ke nan, saboda tun daga nan renon Amal da sadik ya koma kanta. Hatta bacci da su take kwana. Tsakaninsu da uwar sai dan lokaci ta dan dauke su tayi wasa da su, saboda Zahra ba ta dade da zuwa gidan ba ta yaye su gaba daya.

 Komai Zahra ce take yi musu. Sai da aka fara daukar sabbin dalibai, Faruk ya nuna sha’awar sa ka Zahra a makaranta, nan fa Amira tace ba ta san zancen ba, saboda ita daukota tayi ta taimaka mata.

 Da kyar ya lallabata ta bari aka samo mata lesson teacher, tana lesson na awa daya kullum saboda shine tsawon lokacin da za ta iya barinta ba tare da tana mata hidima ba.

 Da Ogadion mai aikin gidan ya tafi gida bai dawo ba, sai ta ki daukar wani. Zahra ta wadatar da ita.

 Itace girki, ita ce share share da goge goge. Ga kuma rainon ‘yan biyu. Tun da suka tafi ko hutu ba su zo kano ba. Saboda yanzu Mommy ta fi zama a Abuja. Ita ma kuwa iyakarta nan din.

 Ko aiki mijinta zai tafi kasar waje tare da shi za su je ta bar Zahra da yara a gida sai mai gadi kawai. Dan lesson din da take yi ya na taimaka mata kwarai da gaske.

 Amma fa aiki take ba hutu a gidan nan. Ko yaushe ka ganta tana da abin yi. Faruk bai taba sanin dangantakar Zahra da Amira matarsa ba. Domin wani zuwa da yayi gida, Hajiyarsa take tambayarsa ‘yan biyu.

 Nan yake shaida mata akan cewa Amira ta samo wata yarinya mai kwazo kuma da ga nan Kano ta tafi da ita. Ko da ta tambayi Mommy labarin yarinyar da ta samowa Amira sai tace mata daga can gida cikin ‘yan uwa aka samo mata ita. Bata yarda, ta barta ta gane kusancin dangantakar Zahra da Amira ba.

 Amma duk da haka, Faruk yana mamaki yadda Amira ke yiwa Zahra rikon sakainar kashi. Saboda ya lura ko alkhairi ya nuna son a yiwa Zahra, sai Amira ta nuna masa ba komai ba sai an yi ba.  

 Shi kuma kokarin yarinyar yake yabawa akan gidansa da ahalin gidan baki daya. Ko shi duk abin da yake so ita za a saka ta yi masa.

 Hatta abubuwan da suka shafe shi kamar gyaran dakin da su wankin bandakinsa ko na kananan kayansa, duka Zahra ce ke yi. Matar gidan sai dai tayi kwance kwance ta dau wanka. Kullum ka ganta kamar zata zaben sarauniyar kyau.

    Zahra dai na samun cima mai kyau. Sutura ma ba laifi, duk da dai ba wani abin azo a gani yayar tata  ta ke mata ba. Sai mafi muhimmanci a rayuwarta dan karatun da ta ke samu daga lesson dinta.

 Duk yawan aikin nan ba shi ke damun Zahra ba, sai kewar ‘yan uwanta da kuma Abbanta da Gwaggonta. Ko lambar wayarsu ba ta da ita balle ita ta samu ta kirasu. Balle kuma ta yayanta da ke wata uwa duniya.

 Ga kanwarta da aka yiwa auren dole ita ma ba ta san halin da take ciki ba, saboda gidan Honourable gaba daya ba su da masaniyar ina Humaira take

 Tayi zaman kusan shekara biyu a Warri kafin Faruk ya dage da lallai dole ta shiga makaranta. Matar gidan ta so ta ki amma ya nuna mata cewar ko yarinya ta shiga makaranta domin ta samu nasarar zana jarrabawar SSCE ko kuma ta mayar da ita  

Gaban iyayenta.

 Cikin kunkunni tace “in tana da su ba”.

 “Ban gane in tana dasu ba? Kin taba ganin mutumin da ba  shi da iyaye”?

Cikin subutar baki tace “sun mutu”.

 “Ko sun mutu ai tana da wasu ‘yan uwan. Zan kuma mayar da ita wajensu”.

 Dariya tayi san nan ta ce “mu din dai ke nan. Bata da kowa sai mu”.

 “Ban gane me kike fada ba”? ya fada kansa a daure.

 Kin ba shi amsa tayi. Sai bayan kwana biyu ya samu Zahra ita kadai yake tambayarta dangantakarsu da Amira. Ba karamin mamaki ya ji ba da ya gane ashe kanwa ce ga mai dakin nasa.

 Tun daga lokacin kuwa ya dauki aniyar kula da ita sama da yadda ya ke yi a baya. A wata ziyara da ya kawo wajen Hajiyarsa yake shaida mata matsayin Zahra a wajen matarsa. Ba karamin mamaki ne ya kamata ba.

 Ita ta sa ka shi ya dada bincikar Zahran har ya samu labarin gidan Baffanta da kuma sauran ‘yan uwanta. Hajiyan ta san su, saboda haka ita ta bincika masa inda suke. Ta kuma samu lokaci ta kai musu ziyara.

 A ranar ba karamin farin ciki Wabili tayi ba da ta jin labarin ‘yan biyun ta. Nan dai suka yi musayar lambar waya da Hajiyan inda ta ba wa Faruk shi kuma ya ba wa Zahra.

 Tun da yake da ita bai taba ganin farin ciki a fuskarta irin na ranar da ya bata lambar Abbanta ba. Kuka da dariya ta ringa yi a lokaci daya saboda murna.

 Da wayarsa ya kira Mallam Jibo. Sai da kwalla ta zubo masa na ganin yadda duk suka kagu da sukaji muryar juna. To wan nan shi ya kulla mata zaren da Mommy ta so datse mata da ‘yan uwanta.

 Bayan nan kuma shi da kansa ya kira wayar Baffa a can Japan, ya kuma kwantar masa da hankali da nuna masa cewar kar yaji komai zai rike Zahra kamar yadda zai kula da kanwarsa.

 Da aka zo saka Amal da Sadik a makaranta ya hada ya sakasu tare. Ita ta samu shiga senior secondary aji biyu, yayin da ‘yan biyunta suke nursery.

Shabiyu ya kamata su tashi ita kuma daya da rabi, amma sai uwar ta saka su a lesson saboda ba zata iya kula da su ba na awa da rabi kafin Zahra ta taso. 

 Kafin asuba ta ke tashi. Ta gyara gidan ta hada abin Karin kumallon kowa, san nan ta shirya yara su tafi makaranta. Tana tasowa daya da rabi ta dora na rana. Karfe hudu su shiga islamiyya a nan estate din su. San nan ta dora na dare. Hatta home work din yaran ita za ta yi musu.

 Yadda uwar ba ta damu da su ba, suma haka ba su damu da ita ba. Su dai in Anti Lala ta na nan shi ke nan. Rashin iya fadin sunanta ya sa suke ce mata Anti Lala. Kuma har bakin nasu ya washe haka suka ci gaba da kiranta. Hatta babansu shima haka yake kiranta.

 Ko abu ne a wardrobe dinta ko na mijinta in dai Zahra bata nan sai dai a jira ta sai ta dawo, saboda ba ta san komai na harkar gidanta ba. Tana cikin group na chatting sun fi hamsin. Mijin na tafiya nema, ita kuwa ta dauki waya, sai kuma kallo da ta aura.

 Ko shigowa yaran suka yi zata korasu akan sun zo suna damunta. Da mijin da gidan da ‘ya’yan ta dauka ta dankawa Zahra. Ita kuwa tana shakatawar ta.

Comments

Popular Posts