☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER 16 ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER SIXTEEN

 A washe garine, da barrister ta mayar da Humaira gidansu hankalinta ya dada tashi. Honourable ba shi da masaniyar abin da ya faru saboda a mota ta bar Humaira, ta shiga gidan domin kokarin fahimtar da su abin da ya faru.

 Amma a yadda lamarin ya kaya da su sai taji tausayin ta ya karu a akan yarinyar. Ta tambayi Honourable da matarsa ko sun san Senator na da HIV. Nan kuwa suka nuna ma ta suna sane.

 Tace “amma shine ku ka aura ma sa ‘yarku”?

 Mommy na budar baki ta ce “Ai kowa ma Allah ke kare shi ba dabarar mu bace. Kuma wan nan ciwo ai yanzu ya zama ruwan dare. Idan ba shi din ba ta san wa zata aura nan gaba”.

 Nan da nan ta fara fahimtar wani abu. Sun dauki yarinya sun ba ta ba tare da sun san dangantarsu da Senator ba. Yauma kuma da ta zo ba wanda ya tamabayi ya suke da shi, saboda haka sai ta fasa gaya musu abin da ya kawota.

 Ga wani abu da ta lura da Humaira. Tun da suka karyo kwanar gidan ta kasa tsai da kukan da ta ke faman yi. Duk da alkawarin da kuma rarrashin da ta ke mata da kuma kokarin nuna ma ta cewar zata yi wa iyayenta bayanin da za su fahimta. Saboda ita a tunaninta tsoron gamuwa da iyayen ta ke kar su zarge ta da kashe auren ta da gangan.

 Hakan ya sa ta fasa sanar da su mutuwar auren na Humaira. Ta yi musu sallama ta tafi. Don ma kar su zargi wani abu, ta ciro dala dubu da ga Jakarta tace “ga shi nan Senator ya ce a kawo musu”.

 Mommy sai dashare baki take ta fara diban dashin da bata taba zubi ba. Sai bayan Barrister ta koma mota har sun fita daga gidan, san nan take tambayar Humaira, shine mahaifinta? Tana kuka ta ke sanar da ita rasuwar iyayenta duk su biyun. Ta kuma sanar da ita cewa nan gidan wan babansu ne.

 Da ta sake tambayarta ko tana da wasu dangin anan kusa ban da shi, Humaira tace “dama a gidan Abban na ke da zama da za a kaini gidanki ne aka dawo da ni nan gidan”.

 Gidan Mallam Jibo suka rankaya, inda suna tafe a hanya ita kuma tana bugar cikinta domin neman Karin bayani dangane da wan babanta kamar yadda ta sanar da ita dangantakarsu.

 A wajen Wabili ta samu cikakken bayanin matsayin Humaira da su. A nan kuma ta dada fahimtar cewar Honourable auren jari ya yi da diyar da bai san ciwonta ba.

 Tunani daya tayi. Idan har ta dawo da Humaira gidan Mallam Jibo ba ta tsira ba, saboda ko a yau Honourable ya samu labarin ta koma wajen iyayen goyonta, yana da damar da zai dauketa ya sake abin da ya ga dama da ita, saboda sanin karfin Mallam Jibo a akan rikonsu kadan  ne.

 Ga kuma karancin wayewa da rashin abin duniya da ta fuskanci suna fama da shi. Wanda ta tabbatar da sun san ‘yancin kan su da Honourable bai isa ya nuna musu mulkin mallaka akan yaran da kaninsa ya mutu ya bari ba.

 Take ta yanke shawara da in har Mallam Jibo ya yadda ya bar mata Humaira a wajenta, tayi alkawarin rike ta amana. Kuma lokaci lokaci zata ringa zuwa duba su. Haka suka hakura saboda sanin zamanta a wajensu bata tsira ba.

  A haka suka yi matsaya. Amma duk da haka sai da sukaje da Barrister har gidan su, su ka ga muhallinta ta kuma kaisu gidan hajiyar Senator saboda su dada sakin jiki da ita.  San nan ta dauki Humaira suka koma wajenta.

 Duk wan nan badakala da ake yi Baffa bai da masaniya, amma sun rabu da Barrister bayan sun amshi lambar wayarta akan zasu hada ta da wanta saboda ya san matakin da suka dauka. A haka suka yi sallama Humaira ta koma wajen Barrister Amina da zama

 Mommy kuwa da ta ga la’asar tayi ta dauki hanya ta nufi gidan da suka kai amarya saboda ta je ta lode abin arzikin da ta san yanzu Senator ya mallakawa Humaira. Amma tana zuwa mai gadi ya sanar da ita cewa ba kowa a gidan sun yi tafiya, wanda shine abin da Barrister ta sa shi ya fada idan Momi ta zo.

   Bayan an yi haka ma, sai aka mai da ita aiki Abuja, ba tare da ta sanar da mommy da kuma Honourable komai ba, ta shaidawa Mallam Jibo da mai dakinsa Wabili. Dalilinta na yin haka ta na son ta dada nisanta Humaira da wan mahaifinta saboda sanin kudurin da yake da shi akan ta.

 Baffa bashi da masaniyar damalmalin da ake damawa da kannensa, sai bayan kusan sati uku. Ya samu shiga gari da ga site din da suke aiki.

 Ba a yarda suyi waya a wajen aiki saboda kampanin suna son sirranta aikin da suke yi. Wan nan dalili ne ya sanya ba a yarda su Baffa su yi waya a wajen aiki ba saboda gudun kar sirrin binciken da suke yi ya fita.

 A wan nan rana da Baffa ya samu shiga gari abu na farko da ya fara yi, shine kiran Abbansa a waya.

 Ba karamin tashin hankali ya shiga ba da ya ji zaluncin da wan mahaifinsa ya kulla a kan kannensa. Da kyar Abban nasa ya rarrashe shi saboda niyyar da ya yi ta ya yanke duk abin da ke gabansa domin zuwa ya daidaita kowa.

 Niyyarsa ya kwato Zahra ya kuma shigar da kara a kashe auren Humaira. Abba yace masa “ba ma sai ka wahalar da kanka ba, mai babbar kotu ya kareta. Ita ma kuma Zahra kayi hakuri na san Allah zai jibanci lamarin ta kamar yadda ya jibanci na ‘yar uwarta.

 Amma yanzu ka bar aikin da kai da kanka ka gaya min cewar in har aka ci nasara saboda kana cikin wadanda suka kirkirin binciken ba karamar daukaka zaka samu ba.

 Ina son ka gane sai ka tsaya da kafafunka san nan zaka zama bango da wadanda ka ke son taimaka zasu dafa su iya tsayawa. In ba haka ba kuwa sai a hadu gaba daya a ruguje”.

 Ajiyar zuciya ya saki. San nan ya ce “na gode Abba. Zan tura maka kudi ta WAPA. Akwai wasu lambobi da zan tura maka. Idan kaje ka nuna musu lambar zasu tura maka kudin cikin akawun dinka. Ina son a canzawa Hamida da Walid makaranata”.

 Godiya kawai Abban nasa yayi, saboda na da ma da yake turowa tara masa su yake yi. Saboda idan ya tuna yadda aiki ke wahalar samu a kasar nan musamman ga ‘ya’yan talakawa, sai yaga gwara ya ringa tara masa kudin da yake turowa yadda idan ya dawo ya kasa samun aiki yi sai ya ja jari da su.

 Shi dai abin da yake samu a shagon wanki da gugarsa ya ishe shi. Bayan nan Abban ya sanar da shi niyyar Barrister na son komawa da Humaira Abuja.

 Shi da kansa ya nemi Barrister a lambar da Abban ya bashi. Ya samu ya tattauna da Humaira. Ita kuma ta dada bashi kwarin gwiwar barinta a wajen Barrister saboda kyawawan halayenta da ta karanta ma sa na ita Barrister din.

 Nan kuwa Humaira ta samu shiga hadaddiyar makarantar ‘ya’yan gata a Abuja. Duk da sai da ta maimaita aji daya amma ba a dade ba ta mike. Boardinga take yi. Kuma ko hutu akayi, Barrister ta nema mata wata makarantar a nan dai Abuja ta yin tahafeez wadda ita ma din ta kwana ce in har mutum ya na son hakan.

 Wan nan shi ya karanta mata lokacin kaiwa Abbanta ziyara da kuma dada nisanta ta da ahalin gidan Honourable.

 A kuma wan nan lokaci ne aka samu baraka a jam’iyar su Senator Alkasim da Honourable inda aka dare gida biyu. Sai kuma aka yi dace kowanne su da bangaren da ya fada. Hakan ya kawo babban sabani a tsakaninsu.

 Hakan ya dada zamowa Katanga ga Humaira, saboda Honourable ya samu ganin Senator, hakan ma ya gagara. Gidan da suka kaita kuma sun je an ce sun koma Abuja.

 Har wajen Wabili Mommy taje neman lambar wayar da za su samu Humaira, ita kuwa ta nuna mata ita ma ba ta san yadda zata samu Humairan ba. Amma fa a Zahiri kusan kullum sai Humaira ta kira iyayen nata da Walid da kuma Hamida sun sha hira.

 Sai da ta shiga makaranta ne san nan ta sanar da su sai karshen mako za ta dinga samun damar kiransu a waya, saboda dokar makarantar ke nan.

 Duk da haka, Wabili dai ta daukar Mommy alkawarin karya na cewar idan ta kirasu zasu sakata ta kira Honourable da kuma ita kanta Momi.

 Hatta shima yayan nata da ke kasar Japan ta kan samu sukunin Magana da shi, idan ya baro site ya shigo gari. Idan ya kira Abbansa da mutan gidan zai kuma kira Humaira. Yanzu damuwarsu daya ce. Rashin sanin halin da Zahra ke ciki a Warri.

Comments

Popular Posts