☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER 15 ☘️☘️☘️☘️☘️

           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/



CHAPTER FIFTEEN

 Duk da dokar da Barrister ta bawa Iya na karta fito daga dakinta komai za ta ji, amma duk da haka sai da tayi karambanin labewa daga bakin kofa.

 Saboda ta san damben aradun da aka kwasa da maigidan da uwar dakinta a wancan auren da ya yi.

 “Ina kike marar mutunci”, muryar Senator Alkasim ta daki kunnuwansu dukan su su biyu. Ita da Iya da ke makale a bayan kofar dakinta tana kallonsu saboda ita dai hankalinta bai kwanta ta bar uwar dakinta da mai gidan shi kadai ba, saboda ta na tsoron kar ya illata ta.

 Kamar yadda Iya ta zata daga Barrister, hakan ne ya faru, saboda daga ido kawai tayi ta kalli mai gidan, san nan cikin sansanyar muryar mai nuna ba abin da ya ke damunta tace “wa alaikassalam”.

 “Ban nemi amincin komai daga gareki ba, ina ki ka kai min matata”? ya fada cikin hasala.

 Result din RVC screening da Dr Farida ta aiko driver ta da shi ya kawo mata, ta tura masa gabansa. San nan ta dauki jotter da biro ta dora a kai ta tura masa.

 Wurgi yayi da takardun ya ci gaba da Magana cikin hargagi yana fadin “takardunki na banza za ki miko min. Na rantse da Allah idan baki fito da yarinyar mutane ba, yau sai na lahira ya fi ki jin dadi”.

 Sai da ta kurbi madarar da ya tarar da ita tana sha, san nan tace “ka san halin da na lahirar yake cikine da har ka ke ganin zaka iya kwatanta shi da ni”?

 Hannu ya daga ya sharara mata mari, wanda hakan ya dada firgita Iya, saboda haka ba shiri ta dauko wayarta takira mahaifiyar Senator. Jin yanayinta da kuma yadda ta nuna mata rikici ake da Senator da mai dakinsa ya sanya dattijuwar shiga tashin hankali. Ba shiri ta sa driver ya dauko mota suka taho ita da kanwata wacce ta kasance suruka a wajenta, saboda danta ne ke auren daya daga cikin ‘ya’yanta, watau kanwar Senator.

 Abin da kowa ya sani da Senator Alkasim, shine ba ya hada mahaifiyarsa da kowa. Mutum ne mai tsananin biyayya ga mahaifansa. Har mahaifinsa ya koma ga ubangiji Kalmar “Allah ya yi maka albarka” ce tsakaninsu.

 Duk abin da mutum ya ke nema in dai ya bi ta kan Hajiyarsa sai dai in ba rabonsa bane, amma ya samu ya gama. Mutane da yawa na alakanta daukakarsa da biyayyar da ya ke yiwa iyayensa.

 Duk abin da ya sa a gaba sai yaga haskensa. Ba boka ba Mallam amma kullum cikin sa’a ya ke. Ita ma kuwa matarsa barrister tana take masa sawu wajen kyautatawa iyayensa da kuma danginsa baki daya.

 Sau biyu yana aure ta na kokarin raba shi da matan. Duk da Yaya Lami na kokarin nuna wa hajiyar Senatora ita ke korar matan, amma sam Hajiyan ta ki yarda da ita. Sai dai ta ce “halinsa ne ya ke korar su, saboda rashin hakurinsa”.

 

 Mu dawo asalin labarin. Amma ita wadda aka mara ba ta gigita ba ko kadan. Murmushi kawai tayi san na ta ce “ina ga wan nan shine horo mafi tsananin da za ka iya yi min saboda hanaka amaryarka da zan yi. Amma rabuwa kam ka sa a ranka kun rabu har abada”.

 Muryar Yaya Lami ce ta katse ta, inda ita ma ta shigo cike da fushi ta fara zazzaga mata nata irin kalar masifar.

 Barrister ta dago ta kalleta sai a lokacin taji hawayen bakin ciki sun gangaro idanuwanta. San nan tace “ai Yaya nayi alkawari daga waccan auren da ki ka sa shi ya yi, in sha Allahu ba zan sake bari ya yi wani auren ba”.

 Hannu ya sake dagawa ya sake gaura mata wani zazzafan marin, amma ko a jikinta, saboda zuciyarta ta tsike da abin da take da niyyar yi.

 “Ke har kin isa ki hana ni abin da nayi niyya. Aure kamar an yi an gama. Ki fito min da yarinyar mutane kafin in babbalaki a nan”.

 Murmushi ta sake yi kamar ba ita ta sha maruka har guda biyu ba. San nan ta kalle shi ta ce “anya kuwa ka fahimci zancena? Ai aure babu shi a tsakaninku”.

 Yaya Lami ce ta taso da zafin ta kamar za ta sake faskamata wani mari, tace “amma ke wallahi an yi tambadaddiyar mace. Ke ba a aure aka aure ki. Idan an ganki kamar mutuniyar kirki, amma ba ki iya komai ba sai datse sunnar Manzo SAW”.

 “A’aYaya, Tsakani na dake a samu mai datse sunnar amma tabbasa ba ni bace” ta fada cikin bacin rai.

 Humaira na cikin bacci ta dinga jin Magana sama sama. A dan firgice ta yaye bargon da ta rufa da shi. Inda ta ke jin sautin murya nan ta dosa, amma ita ma bata fita ba, daga bakin kofar dakin ta tsaya.

 Yaya Lami ta juya wajen Senator ta ce “ni wai wan nan shegiyar yarinyar me ya sa ba zaka iya sakinta ba ne. Ta na zaune in banda rashin mutunci ba abin da take shuka maka”.

 Ta juya wajenta ta ci gaba da cewa “shegiya an dauko ki daga gidan baba na zaure, amma kin zo kin ci jar miya kina nema ki gagari mutane. Ka saketa ka huta da wan nan tashin hankali”

 “Kwarai ya na iya saki na kamar yadda kika fada, amma kafin ki saka shi ya sakeni sai ki ba shi lokaci yayi nazarin abin da sakin nawa zai haifar masa. Shin ya taba fada miki cewa duk wata dukiya tasa a sunana ta ke, saboda ya na tsoron kar ta bare bincike ya zo kansa? Ko ya taba fada miki cewar na sanar da shi duk ranar da ya yi gangancin sakina, ni kuma na yi alkawarin sai na dagargaza duk wani buri da yake da shi a duniyar siyasa.

 Ina son ki fahimce ni, ba wani abu na nema mai yawa ba, aurensa kawai zai saki ni kuwa nayi alkawarin komai zai daidaita a tsakaninmu”.

 Yaya Lami ta sake harzuka da jin kalaman Barrister. Watau ashe shegiyar yarinyar nan ita ke da mukullin taskar Senator da take harin ta shiga ta wawuri rabonta.

 “Amma dai ke kam wallahi anyi majanuniyar mace. Allah wadaran hada iri da ke”.

 Jin wan na kalami ya sanya zuciyar Barrister dada tunkudowa. Ba ta san sanda ta fara fadawa Yaya Lami maganaganu masu zafi ba.

 “Ai in ba ai Allah wadai da hada iri da ke ba, ni kuwa ba ni da abin Allah wadai. Kiyi duk abin da zakiyi amma yau sai ya saki yarinyar nan”.

 “Idan an ki sakinta din me zakiyi”?

 Kallon takaici tayi masa san nan tace “kafi kowa sanin abin da zan yi. One simple phone call and a press confrence is all what it will take and you will be done for”.

 Wan nan kalamai su suka sa ka Humaira ta gane takaddamar da ake yi duk a kanta ne. murmushin takaici ta yi san nan a cikin zuciyarta tace “dama duk wan nan hakilon na kar ta barni in zauna  gidan nan ne? ni da za ta taimaka in samu ya sallame ni in koma gidan mu da ya fiye min. Dan ni wan nan daular da suke ganin su na da ita, dan tsukakken gidan Abban mu ya fiye min ita sau dubu”.

 Tuno mutan gidansu ya saka ta jin hawaye ya na zuba a fuskarta. Har ta juya zata yi komawarta cikin dakin, amma abin da ta sake ji shi ya sanya ta tsayuwa cikin sabon tashin hankali.

 Muryar Barrister taji tana fadin “na dade da sanar maka cutar da kake yi wa yaran mutane tayi yawa nakuma rantse ba zan sake barinka ka saka wata mace cikin larura ba”.

 “Da kike maganar larura, shi ma ba Allah ne ya dora masa ita ba”?

 “Eh ai dama abin da muka iya ke nan. Mu jawa kanmu bala’I san nan mu ce Allah ne ya dora mana. Yaya da ke da shi ku ku ka saka mu a cikin wan nan tashin hankali.

 Muna zaman mu lafiya kina ganin ya fara samun abin duniya kika kanannaaye shi kika shiga gabansa, saboda kin san yana martaba ki a matsayin ki na yayarsa. Amma tabbas ba kya masa son Allah da Annabi. Son abin duniya kike masa.

 Ko kin dauka ban san duk plan dinki a kansa ba. Aiki ya samu aka tura shi wani gari kika hana ni binsa a dalilin idan ya tafi da ni ba zai dinga zuwa gida ya na muku hidima yadda ya kamata ba.

 A dalilin haka ki ka saka shi ya samo mana tsarabar kanajamau”.

 Wan nan kalamai karaf a kunnen mahaifiyarsa da kuma sabuwar amaryarsa. Humaira na kokarin komawa dakin da aka sauketa yayin da Hajiyarsa take kokarin shigowa  cikin falon ita da kanwarta wanan mummunan bayani ya daki kunnuwansu.

 Duk da karancin shekarun Humaira da kuma tsufan Hajiyar Senator, sun san me ake nufi da wan nan ciwon. Duk kansu a wajen da suke tsaye kowa ya sandare.

 Ita kuwa Barrister da bata san da tsayiwarsu ba, taci gaba da bayaninta cikin muryar kuka tana cewa “na yadda na dau wan nan kaddara, amma ba zan zuba ido saboda wani boka da kika kaishi wajensa da sunan neman magani ya bashi shawarar ya dinga auren yara kanana marasa ciwon saboda na jikin sa, ya dinga raguwa”.

 “’Ya’yanki aka aura da zaki dinga shiga tsakanin su”?

 “a’a ba ‘ya’yana ba ne, amma na dauki amanar zan kare hakkinsu ko da ban san daga ina suke ba. Kuma da kike ikirarin ya sakeni ya huta, ko hakan ta faru, na yi alkawarin  ba zan kyale shi ya lalata rayuwar wasu yaran ba saboda takamar yana da abin duniya”.

   Muryar hajiyansa ce ta katse shi daga maganar da ya yi niyyar fada. Cikin tashin hankali ta karaso falon. Duk kansu sunyi mamakin ganinta, saboda ba wanda ya san da zuwanta.

 Gaba dayansu sun dan tsorata da ganinta, saboda zance ne wanda suke boye mata ba sa son ta san cutar da dan na ta yake dauke da ita.

 Ita ma Humaira a nata bangaren kukan kawai take rusawa a kofar dakin da aka sauketa. Abin da bata gane ba shin ita ma tana dauke da cutar ne saboda ta sha ji ana fadin mai ciwo da marar ciwon ba sa iya auren juna. Ba ta da mai bata wan nan amsa sai kawai ta ci gaba da kukanta. Tunaninta ya karkata kan cewa itama ta na da ciwon shi yasa Baffansu ya aurar da ita da gaggawa.

 Tana share hawaye take fadin cikin zuciyarta “ni gwarama in mutu in huta da wan nan bakin ciki. An rabani da Abbana da Gwaggona da kuma ‘yan uwana Hamida da Zahra”.

 Hawaye ne ya sake kwaranyo ma ta da ta tuna da dan karamin kaninsu watau Walid da ba shi da abokin da ya wuce ita. Ko a bakinsa ne sai ya boye abu idan aka bashi lokacin bai yi wayo sosai ba. Idan kuwa ya shigo ya tofo shi daga bakinsa ya bata, bata jin kyamarsa haka za ta karba ta ci.

 Jin salatin da aka zabga a falon ne ya katse mata tunaninta. Ta dan leka ta ga duk sun yi kan Hajiyar da hanzarinsu saboda kamota saboda kokarin faduwa da ta ke yi, wanda da gani tashin hankalin ne ya haddasa mata hakan.

 Yayin da su kuma a nasu bangaren da kyar suka ja kafafunsu suka karasa inda hajiyarsa da kuma kanwarta suke. Bayan sun samu sun zaunar da ita akan kujera, Yaya Lami ce ta yi karfin halin cewa “yawwa Hajiya gwara da Allah ya kawoki. Ke ce mai goyon bayan duk abin da ta yi saboda kin ce kin yarda da ita ba zata taba cutar Kasimu ba, to yanzu ga shi nan kin gani da idonki. Auren da aka daura yau take son farraka shi kamar yadda ta saba farraka sauran”.

 Hajiya kallonta kawai tayi. Sai da tayi addu’a a zuciyarta ta ji saukin radadin da ya taso mata, san nan ta kalli Barrister da ke durkushen gabanta tana gursheken kuka. Saboda Allah ya sani ko da take yiwa Senator barazanar tona masa a sirri a duniya, tana fada ne kawai, amma ba wan nan agendar a zuciyarta.

 “daina kuka Amina. Gaya min gaskiya abin da naji da kunne na haka ne ke da wan nan yaron kuna dauke da wan nan cutar”?

 Kasa bata amsa tayi sai sautin kukanta da ya karu. Hakan ya bawa Hajiya amsar tambayarta.

 “Inna Lillahi wa Inna Ilaihi raji’un” shine abin da suka iya furtawa a tare ita da ‘yar uwarta da suka shigo tare.

Juyawa tayi wajen dan nata da ya sandare a tsaye tace “Kassim, da gaskene abinda matar ka ta fada”? 

 Shima shiru ya yi ya kasa bata amsa. Karfin hali tayi san na tace “shirunku shine amsar tambayarta”.

 Ta juya wajen Yaya Lami tace “tun yaushe ki ka san yana da wan nan ciwon”?

 “Hajiya mh  ba fa abin da kike tsammani bane kumama an ce irin nasa ana warkewa” ta fada cike da rudani a muryarta. Saboda ba tason abin da zai jawo Senator ya daina shawara da kuma jawota a jiki fiye da sauran kannensa da suke uwa daya. Ga shi dama ta na da burin ta faranta ma sa rai saboda ta na son ya tura mata yaranta maza guda biyu karatu kasar waje.

 “Ina ita yarinyar da ya auro din take” yayar Hajiyan ta tambaya.

 Barrister ce ta mike ta nufi dakinta domin ta kirawo Hunaira. A bakin kofar dakin ta sameta tana ta gursheken kuka.

 Sai da suka shigo san nan Barrister ta samu karfin halin yin Magana. Inda ta ce “Hajiya na rantse da Allah ba buri na in hana shi aure ba, kawai ina son raba shi da al’adar auran yaran mutane yana yada musu ciwon kuma ya sake su ba.

 Abu daya na ke so da shi ya dage da zuwa asibiti domin karbar magani da kuma shawarwarin a wajen likita. Ciwo na Allah ne. mutuwa ma, ta Allah ce. Ba wanda zai mutu kafin lokacin sa.

 Kuma na gaya masa idan auren yake so ya je kungiyar heart to heart, watau wajen da ake kula ma su wan nan ciwon. Akwai mata sai ya nemi auransa ya yi. Abu daya ne na ranste ba zanyi ba. Ya auri mai lafiya ya hada ta da ciwon. Wannan kam ko kasa da sama za su hadu ba zan zuba ido in kyale shi ba, sai inda karfina ya kare”.

 Hajiya tace ai wan nan jihadi ne kika yi. Kuma ni tun sanda Lami tace min kina raba shi da matansa nayi amanna da cewa haka kawai ba zaki hana shi aure ba. Saboda na san da ga gidan da kika fito. Na kuma san irin tarbiyar da ki ka samu.

Hakan ya sa, na hakkakewa zuciyata dole akwai abin da ke faruwa. Amma Baban Fadila ba ka kyauta min ba”.

 Ita ma cikin shehshekar kuka tace “Hajiya ki kwantar da hankalinki, idan har zai daure ya kiyaye dokokin da za a gindaya masa, tare da shan maganin akan lokacin ba wanda zai taba gane yana da wan nan ciwon.

 San nan ina rokonki da ki taya mu da addu’a, Allah ya sanya wan nan ciwo ya zama kankanrar zunubai a garemu”.

 “Allah ya kyauta. Yanzu ina su wadancan biyun da suka rabu suke”?

 “Daya tana karbar magani, saboda ta riga ta samu ciwon, dayar kuma na mai da ita makaranta, saboda ita Allah ya tsare bata kamu da shi ba”.

 A nan dai Hajiya ta saka senator ya bawa Humaira takardar sakinta, ta kuma dorawa barrister nauyin mayar da ita wajen iyayenta. Shi kuma bayan doguwar nasiha da mahaifiyarsa da kuma kanwarta suka yi masa shi ma ya rusuna ya dada gane kuskuren sa. A nan a gabansu Barrister tayi alkwarin taimaka masa suje center ya nemo macen da duk yake so ya aura, ita kuma tayi alkwarin tsaya masa.

 Amsar da ya basu ita ta dada nuna nadamarsa. In da yace shi dama ba auren ne a kansa ba, kawai lakanin da malamin ya bashi yake kokarin aiki da shi, amma yanzu ya gane gaskiya zai saki wan nan layin ya kama dahir da matarsa ta dade ta na nuna masa.

Comments

Popular Posts