☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* CHAPTER 14 ☘️☘️☘️☘️☘️

           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/






CHAPTER FOURTEEN

 Motar taxi ta airport ce ta tsaya a bakin gate din wani tangamemen gida. Horn din da mai motar yayi bai sanya mai gadin bude kofar ba, sai dai yayi hanzarin leko da kansa ta ’yar tagar da ke jikin dakinsa domin ganin waye ya kawo musu ziyara.

 Sauke gilashin tayi yayin da fuskarta ta bayyana. Kyakkyawar fuskarta wadda hijabin da ta sanya bai hana ganin kyawun matar ba, ta bayyana.

 Cike da farin ciki mai gadin ya yi hanzarin fitowa daga dakin. Yana kokarin bude gate din matar da ba za ta haura shekaru arba’in ba, ta fito daga cikin motar tana fadin “Hakimi, bari ba sai ka bude gate din ba, dauko min kayana a bayan motar”.

 Cike da murna ya ke mata sannu da zuwa yayin da yake kokarin jan dan madaidaici da kuma babban akwati domin shiga gidan. Bayan ta sallami mai motar ta rufawa maigadin baya domin karasawa cikin gidan.

 Yadda gate din ya ke wawakeke, haka gidan ya ke tangameme. Irin gidan da ake yiwa lakabi da aljannar duniya. Shuken shuken da  ke kewaye da harabar gidan kadai sun isa mutum ya dau sama da awa yana kallonsu.

 Ga kuma rantsattsun motoci har guda biyar masu numfashi a rumfar ajiye motocin gidan. Wargajejiyar kofar falon ta nufa, inda kafin ma ta karasa wata ‘yar matashiyar yarinya mai shekaru sha biyu zuwa sha uku ta fito a guje da kuma wani dan saurayi da ya gazata  da shekaru biyu ko uku. A guje suka karaso wajenta suna rige rigen isa wajenta. Kowanne su na fadin “Ummi oyoyo!”. Kama su tayi ta rungume cike da farin ciki tana fadin “ga yaran Ummi. Yara masu albarka”.

 Uwargidan Senator kenan angon Humaira. Macece mai tsananin wayewa, amma irin wayewar da addini yake so. Duk wanda ya san barrister Amina Alkasim Bala ya san ta da kyawawan dabi’u. Wala a wajen aiki ko cikin dangi ko kuma a mu’amala da mutane. Hatta masu aikinta mutunci ne tsakanin ta dasu.

 Saboda kamar misali Iya mai kula da yaranta tun haihuwar Fadila ‘yarta ta fari take tare da ita. Ita tayi mata rainon Fadila da kaninta  Fadil. Tana da wasu masu aikin inda ta kan dauki kananan ‘yan mata wadanda sukan taimaka wa Iya da ayyukan cikin gida yayin da Iya na sa musu ido. Amma duk mai aikin da ta dauka sai ta sanya ta makarantar boko ta kuma hada ta da nata yaran suyi karatun islmiyya a wajen malamin da yake zuwa domin koyar da nata yaran.

 Kafin su koma ga iyayensu kuwa har ‘yar sana’a sai ta tabbatar sun koya ta kuma yi musu hidimar aure. To wan nan babbar lawayer itace ta kasance kishiyar da Allah ya hada Humaira da ita.

Ta na aiki da babban bankin Nigeria watau CBN a matsayin  babbar lawayer bankin. Tana kuma shiga ayyukan kungiyoyin sa kai domin tallafawa wadanda aka zalinta domin kwato musu hakkinsu, musamman mata da kananan yara.

 Ko yanzu daga wani taron karawa juna ilmi da ta halarta a kasar Britania ta ke.

 “Ummi kin sayo min Xbox din da kika yi min alkawari”?

 “Na sayo amma sai naji idan Iya tace you behaved well when I was not around”.

 Kafin ma ya bata amsa wata dattijuwa ta fito daga cikin gidan. Duk da itace uwar dakinta amma matar nan sai da ta dan rusuna kafin ta amsa gaisuwar da mai kula da yaran nata ke kokarin yi mata.

 Cike da murnar ganin juna suka shiga gidan kowa a yaran na kokarin bata labarin abin da ya wakana bayan bata nan.

 Da kyar suka kyaleta ta shiga ciki ta samu tayi sallah tayi wanka, san na ta dawo cikin dakinta inda ta same su duk sun kosa ta zo ta bude akwati ta basu tsaraba.

 Mai aikin ce tace “ranki ya dade sallame su saboda ni da Isa driver muna bukatar son ganinki”.

 “Ina fatan lafiya Iya”?

 “Lafiya amma ba lau ba. Isa da ya dauko ki bai gaya miki komai ba”?

 Da alamun damuwa tace “ba shi ya dauko ni ba, saboda sai gobe ya kamata mu gama, da daddare jirginmu ya taso. To kuma sai  na gama aikin da ya kaini da wuri. Ganin na samu jirgi kawai sai na taho. Me ke faruwa Iya”?

 “Ai Ummin Fadila wani yakin ne ya dada tunkaro ki. Abban su Fadila ya daura aure yau din nan. Na kuma ji yana sanar da yayarsa akan suje da Isa direba su dauko amarya”.

 “InnaLillahi wa inna Ilaihi raji’un”. Shine abin da ta furta a bakinta. “Kiramin Isan”, shine abin da ta sake fada.

 Da hanzari Iya ta sauka domin kiran Isa wanda ta samu a falon kasa shima yana jiran sakkowar uwardakin na su.

 Sai da ta ta bude akwatin ta sallami yaran san nan ta sakko kasa da wasu manyan ledojin guda biyu. Bayan sun gaisa da Isa ta mika masa ledojin guda biyu, wanda shi kansa ya san na meye.

Al’adarta ce duk sanda tayi tafiya ko nan da Kura ne sai ta samu abin data sayawa ma’aikatan gidan kuma har da iyalansu take hadawa. Ga tsayuwa da take a kan lamuransu ko nakudi kona taimakawa da wasu lamuran. 

 “Ranki dade ai inda kika san inyi tsinstuwa inje garin da kika tafi haka naji. Na rasa yadda zan sanar dake. Iya kuma ta buga waya tace bata sameki ba”.

“ Ina ganin ina jirgin shi yasa ta kasa samuna. Ashe maigidan ka ya kara aure da bana nan”. Ta fada ba alamar tashin hankali a tattareda ita 

“To wallahi Hajiya kin san halin yallabai. Duk da neman auren da daura shi a cikin kwana goma akayi komai. Ranar da kika tafi a washegari yaje neman auren”.

 “Yar gidan waye”? ta sake tambaya.

 “Babanta wani dan siyasa ne. Ya je wajensa ya ganta shine a wajen aka hada maganar auren”.

 “Shike nan Isa. Kar kayi nisa zan nemeka. Iya dan bani wani abu in sa a cikina”.

 Iya ta mike ta shiga kitchen yayin da Isa yayi mata sallama ya fita tare da godiya. Wayarta ta dauka ta kira wata lamba. Sai da aka amsa daga daya bangaren san nan ta ce “an gai da likita  bokan turai”.

 Daga daya bangaren kawarta mai suna Dr Rufaida ta amsa tana fadin “ashe Barrister ta sauka kice in karya doka san rai na”.

 “Ai kuwa yanzu zaki karyata, domin kuwa Senator ya yo abin da ya saba”.

 Cike da mamaki tace “ba dai wani auren ya dauko ba”?

 “Shi ya dauko mana, saboda haka ki shirya dana huta zan shigo mu san abin yi ki zama cikin shiri”.

 “Ai abin yi daya ne. Yadda aka saba haka za ayi wan nan din ma”.

 “Kar ki damu yanzun nan zan shigo gidan naki”.

 Nan dai suka yi sallama suka ajiye wayar.

 A gidan Honourable kuwa ana ta shiryen shiryen kai amarya. A kokarin Senator Alkasim Bala, akai masa amarya guest house din sa kafin uwar gida tankarin gida ta dawo daga tafiyar da tayi. Baya tsammanin dawowar ta sai wajen jibi. To sai kuma tayi masa dirar ba zata.

 Bayan an sallaci isha, sai ga Barrister Amina da jama’unta sun kai mota biyar da sunan sun zo daukar amarya.

 Ganin hadaddun matan da Senator ya turo, ya sanya Mommy dada rudewa. Nan da nan aka shiga haba haba da su. Duk da sun yi mamakin ganin gidan bikin a watse, alamar babu mutane da yawa, amma ba su nuna hakan ba.

 Babu wasu ‘yan rakiyar amarya daga Mommy sai ‘ya’yanta mata guda biyu watau Amira da tabararriya Sofy da ke makale da wani katon dodon kare. Ita ala dole ga aje butter.

 Ba su wani bata lokaci ba suka shiga motocin suka nufi gidan Amarya. Sai da Barrister taga sun isa gida san nan ta daga waya  ta kira Isa driver gidan su, ba wata doguwar Magana tayi ba illa tace masa “ka iya zuwa dauko Yaya Lami yanzu”.

 Suna cikin mota Dr Rufaida tace mata “ta ina za a fara”.

 “Ta inda aka saba”, daya aminiyar ta ta da ta kasance itama Lawyer ce mai suna Barrister Karima tace “ai ina ga we just follow the same process. Idan munga daya suke da ango sai a san abin yi. Idan kuma suna opposite factions sai mu san next line of action da zamu dauka”.

 Sauran biyun ma watau Muna da Zakiyya suma suka nuna amincewa da wan nan shawarar.

 Suna tattaunawa har suka isa  tafkeken gidan senator Alkasim. Daga harabar gidan kawai kyawunsa ya tafi da imanin Mommy. A zuciyarta take rayawa ba don tsoho bane kuma ga record din da ake tunanin yana da shi da ba abin da zai hana ta kai tata ‘yar gidan.

 Amma ta manta ‘yar tata har yanzu bata gama girma ba saboda dikeken karen nan dai da shi take bacci. Har a wan nan shekaru hatta kayan da zata saka sai mai aiki ta dakko mata. Amma ita da kan ta, ba zata iya yiwa kanta komai ba.

 Tana shekara goma sha biyar ko undies dinta sai mai aiki ta wanke. Ta dai iya sakawa da cirewa. Amma ko daukewa daga inda ta cire Allah bai sa ta iya ba.

 Barrister ta sauke su a wani katon dakin da ta sa aka gyara mata shi kafin su tafi dakko amarya. Duk da dare ne wajen takwas na dare amma sai da aka cika ‘yan kawo amarya da kayan abinci nau’I iri iri. Mommy ganin yawan abincin da lemukan sha ta ce “tun da dare yayi bari mu tafi dasu gida har dangi ma sai a rabawa”.

 Take kuwa Barrister ta sa su Iya suka loda musu kayan a motocin da suka dauko su. San nan ta sake dauko turamen sufa guda shida  da Hollanda shida da kudi dubu dari biyu ta basu tukwuci.

 Mommy bata santa ba, bata taba ganinta ba, amma ganin abin duniyar da ta cika su da shi ta dau ‘yar da bata san ciwonta ko zafinta ba ta mika musu.

 Tun da dama Senator ya bayar da dokar kar a kaita da komai, saboda ya tanadar mata da komai, tun daga suturara sawa har kayan amfani na gida.

 Har Mommy ta fita ta dawo ta sunkuya gefen Humaira wacce zuciyar ta ke mata zafi. Hatta ‘yar uwar tagwaitakarta, Mommy bata barta ta rako ta bakon gidan da aka sayarwa masu gidan da ita ba. Domin a ganinta sayar da ita  Baffan nata yayi.

 “Dama idan ya baki kayan lefen ki gobe ki tabbatar kin kira ni na gani, saboda dole a debewar saura ‘yan uwa daga ciki”.

 Ita dai bata bata amsa ba sai kukan da ta ci gaba da yi.

 Bayan sun yi sallam sun fita, sai ga Barrister da Dr Rufaida da Muna da kuma Zakiyya sun shigo dakin. Ita dai tana lullube cikin mayafi bata iya daga kanta ta kalle su ba.

 Muna ce ta ce “amarya sauke lullubin mana ki ga yayunki”. Shiru tayi bata motsa ba. Zakiyya ce tace “kin san tana jin kunya ba lalle ta iya bude fuskarta ba, bari ku gani” gefenta ta je ta zauna ta yaye mayafin da aka lulluba mata.

 Gaba dayansu salati suka saka na ganin karamar yaarinyar da Senator ya kwaso. Kwarai tana da kyau ba na wasa ba, amma kuruciyarta a fili take.

 Rufaida ce ta kalle su ce ta ce “she is so young. Anya ma kuwa ta san inda ta kawo kanta”?

 “Ta kawo kanta ko a ka kawota” inji Muna.

 Barrister ce ta sake cewa, yanzu dai zamu yi wan nan maganar ta ina za a fara”?

 “Ai inaga yadda aka yi da sauran haka itama za a yi da ita” Zakiyya ta amsa mata.

 Ita dai Humaira sai  raba idanu ta ke yi ta kasa gane maganar da suke yi. Tunaninta ne ya katse a lokacin da taga daya daga cikinsu ta fiddo sirinji daga Jakarta, yayin da sauran suka rike hannunta, matar nan ta kafa bakin allura ta fara zukar jininta.

 Jikinta ne gaba daya ya dauki rawa. Zuciyarta kuwa raya mata take “an kawo ki gidan’yan shan jini”. Kafin ta gama hadiye tsoronta da kukan da ya sake tunkudo mata, matar da ta zuki jininta cike da sirinji ta mike  tana rufe shi tana fadin “let me get the RVC screening done, zan dawo nan da rabin awa in sha Allah”.

 Ta fice daga dakin. Barrister kuma ta buga wa Iya waya ta ce mata ta kawo wa bakuwa abincinta.

 Bayan ta shigo da trayn, Muna tace “sakko kici abinci”. Kuka ta sake fashewa da shi. Barrister ce ta zauna gefenta tana fadin “ki saki jikinki. In sha Allah ba abin da zai same ki. Just trust me da iznin Allah ba zan cutar da ke ba.

 Kwarai kalaman sun yi tasirin a zuciyarta duba da yadda ta sauke wata sansanyar ajiyar zuciya, alamun ta yarda da zancen kishiyarta. Ba tare da ta san dalili ba, sai taji ta yarda da kalaman matar.

 Muna ce ta zuba ferfesun kaza a cikin wani karamin kwano ta kuma zuba mata lemon kwali a kofi, san na tce “oya sakko kici abinci bana son musu. Kowa ya ganki, ya san yinin yau baki ci komai ba”.

 Cikin shakakiyar murya da ta koshi da kuka ta ce “Anti kiyi hakuri zan ci amma banyi sallah ba”.

 “To taso muje”. Ta wuce gaba inda Humaira ta bi ta a baya, ta nuna mata toilet. A cikin toilet din ma ta dade tana kuka kafin ta iya karfin halin fitowa daga bandakin.

 Suna kallonta suka san kuka ta sake yi. Muna ce ta sake cewa wan nan kukan naki baiyi yawa ba kuwa. Ai murna zaki yi ko ba komai kin zama matar Senator”?

 Wani kukan ne ya sake fitowa ba tare da ta iya hadiye shi ba. “Come on stop teasing her” inji Barrister.

 Lokacin data zo sujjardata, ta karshe kuwa duk sai da suka tausawa mata, saboda yadda take addu’a tana kuka harda  jijjiga.

 Bayan ta idar da sallar, suka takura ta sai da ta ci abinci. Ba laifi ta ci da dan dama, amma fa hawaye bai daina zuba daga fuskarta ba. Saboda ta hango tarin matsaloli a inda aka kawo ta.

 Su dai suna kallon ta kawai suna kissima abubuwa da yawa a kan amaryar ta su. “shiga bandaki ki yi wanka ki sa kayan barci”. Ba ta yi mata musu ba ta mike ta shiga bandakin da ta fito daga ciki dazun. Nan ma dai sai da ta shaki wani kukan kafin ta yi wankan ta fito. Kayan da ta cire su ta sake maidawa.

Muna ce ta dauko doguwar rigar Fadila ta bata ta saka. Da ke Fadilan na da dan garin jiki caf ta zauna a jikinta kamar dama tata ce. Magani Muna ta sake ballowa ta bata tace “ungo ki sha”. Ba tayi mata musu ta karba. Ita kam tun da suka zuki jininta ai ta san bata da wani katabus. Duk abin da za suyi da ita ma ta yarda da kaddarar da ta hau kanta. 

 Duk da ta na dan tsorace da su, amma hakan nan ta ji ranta ya kwanta sai tana ganin kamar babu abin da zasuyi mata na cutarwa. Hakan ya hanata musawa, ta karbi maganin da ruwan da Muna ta mika mata.

 Bayan ta shanye sai ta sake miko ma ta kofin madara mai dan dumi. Shi ma ta karba ta shanye, san nan cikin dasasshiyar murya tace “Anti na gode”. Ko minti biyar ba tayi da shan maganin ba taji idanuwanta na lumshewa. Kafin kace kobo bacci mai nauyi ya dauke ta.

 Karima ce ta juya ta kalle su tace “Dr fa ta yi waya tana da aiki a asibiti ba zata samu dawowa ba, amma fa result din RVC is negative, saboda haka sai a san yadda za yi da Senator”.

 “Wan nan mai sauki ne. ku dai na gode da kokarinku ku tafi ni nasan yadda zamu kwashe da shi. Amma please ku tafi min da Fadil da Fadila, saboda bana so suyi witnessing thug of war din da za yi a gidan nan yau”, inji Barrisater Amina.

 Nan suka yi mata sallama suka wuce tare da yaranta. Ita kuma ta tsaya jiran maigida ango, saboda ta san duk inda yake yau sai ya nemeta.

Comments

Popular Posts