☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* 41 ☘️☘️☘️☘️☘️

 


           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/


TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=0



CHAPTER FORTY ONE

  Rana ba ta karya, sai dai uwar diya ta ji kunya. A nan masallacin Faruku aka yi wa Amira addu’ar arbain. Ga Baffa ga Mallam Jibo ga Honourable ga kuma Saddam. Duk sun halarta.

 Bayan kuwa an gama addu’oin sai a aka sanar da mutane cewar su dan dakata akwai daurin aure. Lokacin da honourable ya ji an shafa fatihar auren Zahra da Faruk sumewa ne kawai bai yi ba.

 Bai samu sararin tsayawa a daura na Humaira ba, ya fice ya nufi gidansa. A hargitse ya shiga gidan, saboda tashin hankali da kuma bacin rai.

 Saddam ne yayi kokari ya sanarwa da Mommy inda yace “wan nan dashin ma fa ba dauka. ‘Yarki kowa ba ya sonta”.

 “Ban gane abin da ka ke fada ba”, Mommy ta katse shi da hanzarinta.

 A sakarce kamar yadda ya saba Magana ya ce “ai ta kife gaba daya. Ni na rasa Zahra ita ta rasa Faruk”.

“Ban fahimci zancenka ba”? Momy ta fada cikin tashin hankali.

 “Me ye ba ki gane ba a ciki. Na ce miki Zahra an daura mata aure Faruk”.

 Wani zagi ta mulmulo ta dankara masa. San nan ta kai dubanta inda Sofi ta ke kwance tana bacci ko sallar asuba ba ta tashi ta yi ba, saboda kwana da tayi akan waya tsakanin youtube da chatting.

 Wannan ita ce al’adarta saboda haka tashin asuba ke mata wuya. Lokacin sallarta wadda ta sabarwa kanta shine takwas zuwa tara na safe.

Mommy ta lura tabbas ba ta ji abin da suke fada ba.

 Ba ta dubi mummunan halin da Honourable ya ke ciki ba, saboda ko magana ya kasa yi saboda damuwa da tayi masa yawa.

 Ita cikar burin ‘ya’yanta shi ne abu mafi muhimmanci da ta fi damuwa da shi. Mayafin ta ta yayibo tana fadin “muje Saddam ka kai ni gidan Hajiyan Hadizan inji dalilin wan nan wulakanci da tozarci”.

 “Eh muje Mommy. Don gaskiya ko Sofi zata iya hakura da Faruk ni kam sai an bani Zahra ta. Kin ji yadda kirjina ya ke zafi saboda na samu labarin ta auri wani ba ni ba”, Saddam ya ci gaba da gayawa Mommy.

 Duk da sanyi safiya saboda lokacin bai wuce karfe bakwai ba, amma sun tarar da dangi sun cika gidan. Ga dukkan alamu ma a gidan suka kwana.

 Da murna Hajiya Hadiza maman Faruk ta tare ta da fadin  “sannu da zuwa uwar amarya”.

 “Ba abin da zaki ce da ni munafuka maciya amana. Ashe saboda kasa ta rufe idanun Amira zaki iya cin amanarta”, Mommy ta fada cike da zafin rai.

Ganin za su bar abin fada a gaban mutane ita da kawarta ga kuma zancen da take yi bata fahimce shi ba, Hajiyar su Faruk ta yi kokarin janta falon mai gidan.

 Bakaken maganganun da ke fita daga bakin Mommy da take fadin an ci amanr Amira. Wa ya sani ma ko tun tana raye su ke cin amanarta, su suka sanya Hajiyan Faruk ta fara gane inda ta dosa.

 Duk da haka ta kwantar da kanta tace “Maman Amir ban fahimci zancenki ba. Ke da kanki ki ka nuna amincewa da auren Zahra da kuma Abban su Amal. Me ya kawo maganar cin amana”.

 “A cikin ‘ya’yan da na Haifa kin sanni da mai suna Zahra ne. Ai kanwar marigayiya na baki ba boyi boyin ta ba”.

 “Ikon Allah Hajiyan su Faruk ta fada tana mai kama bakinta saboda mamakin wan nan Magana ta Mommy.

 Sai yanzu hasashenta ya zama gaskiya wato ashe wan nan sakaryar ‘yar tata Mommy take nufin ta bawa Faruk. To wan nan idan an aureta ace an auri me.

 Yarinyar da ko kula da kanta ba ta iyawa ta ina zata kula da miji da ‘ya’ya uku kuma ciki har da jariri danye sharaf.

 “Yanzu duk maganar ba ta zafi ba ce. Fadi ya kike son ayi”?

 Jin kalaman Hajiya Hadiza ya sanya zuciyar Momi sanyi. San nan tace “yawwa aminiyata na san zaki fahimce ni. Yanzu shi Faruk ya saki auren Zahra saboda da ma Saddam ne ya ke sonta.

 Sai a daura masa aure da Sofi ita kuma Zahran a daura mata da Saddam din. Kin ga an bawa kowa abin da ya ke so”.

 “An dai bawa ‘ya’yanki abin da suke so amma ba kowa ba. Ina kika ga an taba haka”. Hajiyan su Faruk ta bata amsa.

 Nan kuwa ran Momi ya baci ganin rainin hankalin da Hajiya Hadizan ke kokarin yi mata.

 “Kina nufin auren ya zauna ke nan “? Mommy ta tambaya.

 “Kwarai kuwa mutu ka raba takalmin kaza”.

 “Ai kuwa na rantse da Allah ba ki isa ba. Auren an raba shi an gama”, Mommy ta amsa mata.

 Dariya Hajiyan su Faruk ta yi san nan ta ce “ikon Allah. Yau naga karfin hali. To raba shi mu gani”.

 Mommy za ta kara Magana ta katse ta ce “kin ga dakata Maman Amir. Ni nan da kika ganni na san me ya dace da ni. ‘Yar da kike kira boyi boyi ita uban yaran ya ga ta dace da shi ita kuma ya nuna sha’awar aura.

 Yanzu ke wan nan ‘yar ta ki da kike Magana ta gama rike kanta ne balle ta rike wani. Yanzu haka in ba yi sa’a ba ko tashi daga baccin jiya ba tayi ba. Kuma ni da hankali na ba zan dauki yaro in tura shi cikin matsala ba”.

 A harzuke Mommy ta katse ta ta na mai cewa “ai ban san tanadin cin mutunci ki ka yi min ba. Yarinya kuma dole a sake ta saboda ba da sanin ubanta aka daura mata aure ba”.

 Murmushin takaici ta yi, saboda jahilcin da Mommy ta nuna karara. San nan ta ce “amma maman Amir kin bani mamaki. Ga babban wali nan wanta uwa daya uba daya. Ai kuwa kin san yafi wan uba matsayi’.

 Wan nan kalami na Hajiya hadiza ba karamin tunzura Mommy suka yi ba. Nan kuwa ta fara kumfar bakin in dai Faruk ba zai auri Sofi ba to kuwa ya zama lallai a bata rikon jikokinta.

 Hajiyan su Faruk kawai zaune tayi ta na kallonta ba ta tanka mata ba. Nan dai ta karaci  buyaginta ganin ba ribar da zata ci ta fice daga gidan.

 Har zata wuce gidansu sai ta fasa ta sha kwana zuwa gidan Mallam Jibo.

 A dai dai wan nan lokaci kuma su Chibbu ne da su Wabili suka taru ana ta faman bawa Zahra baki. Tun jiya da daddare ta ke kuka saboda tunowa da tayi da marigayiya Amira. Kuma wai ita ce ta kasance matar mijin Amiran.

 Da farko ganin abin ta ke yi kamar wasa, amma da taga gadangadan abin ya tunkaro sai kuma ta shiga damuwa. Ba ta tabbatar da gaske ba ne sai da taga mutanen Mayo Lofe sun iso san nan ta dada tabbatarwa aurenta da mijin Amiran da gaske ne.

 Chibbu ce da ta gaji da rarrashinta ta ce “ni ina ga akira Jibo ya zo a warwaren auren tun da bata son shi Faruk din. Amma kuma haka na nufin rabuwarta da yaran da ta ke kulafuci ke nan”.

 Jin haka ta dago da sauri ta ce “a’a Chibbu don Allah kar ki rabani da su Amal”.

 Chibbu ta sake cewa “su Amal kuwa dole ki rabu da su tun da ba kya son ubansu”.

 Nan da nan ta shiga share hawayen ta tana fadin “kinga Chibbu na daina kukan. Don Allah kar ki raba ni da su Sadik”.

 Nan dai suka shawo kanta har ta hakura zata yi wanka tayi kwalliya. Kusan Humaira ta fi kowa murna, saboda kukan ‘yar uwarta da ya hana ta sukunin murnar auren nata habibin.

 Tana kokarin tashi suka ji amon muryar Momi da ta shigo gidan ba ko sallama. Kafin su farga da abin da ke faruwa ta janyo Zahra. Nan kuwa ta rufe ta da duka hannun bibiyu.

 Duk kokarin Chibbu da Wabili sun kasa karbar Zahra a hannunta. Kirbarta ta ke ta na fadin “yadda ki ka sa bakin cikin cin amanar da ku ke yi ke da Faruk yayi sanadiyyar mutuwar ‘yata nima sai na raba ki da rayuwarki.

 A bangaren Faruk kuwa bayan an gama addu’ar daurin aure ya samu ya sallami jama’a, sai ya tunkaro gidan Mallam Jibo. Saboda tun jiya yake neman wayar Zahra ya kasa samu.

 Duk da Humaira ta sanar da shi ba komai kawai ba ta dan jin dadi ne ta sha magani ta kwanta, amma hakan bai sa ya hakura da zuwa domin ganin halin da ta ke ciki ba.

 Can masallacin ya baro Baffa da Ibu tare da abokansu da suka samu zuwa daurin auren. Duk da da sassafe aka yi shi amma mutane da dama sun samu halarta.

 Yana parking Saddam ya hango shi. Yana kokarin kiran Zahra da wayarsa sai kawai jin saukar naushi ya yi wanda zafin naman da ya ke da shi ne ya sa ya iya kaucewa bai samu fuskarsa ba.

 Ya na kokarin kai masa wani dukan ya kama hannunsa ya murde yana fadin “Saddam lafiyarka? Me ya faru da har haka zata faru tsakanina da kai. Ka manta nifa kamar yaya na ke a wajenka”.

 “Ta ina ka zama yayana maci amana. Kuma na rantse da Allah tun muna shaidar juna ka rabu da Zahra. Ni ni kadai ne mijinta”.

 Sai a lokacin ya fara fahimtar zancen Saddam. Wurgar da shi kawai yayi a kasa yana kokarin barin waje sai ga Chibbu a guje ta fito domin neman dauki saboda Mommy ga dukkan alamu kokarin kashe Zahra ta ke kamar yadda ta yi ikirari.

  A gaggauce ta gaya masa abin da ake ciki. Da gudu ya bita suka koma cikin gidan. Ya na ganin irin shakar da Mommy ta yi mata ya hankide ta ya dago Zahra da ke zaro numfashi da kyar ya rungume a jikinsa ya na kokarin rarrashinta.

 Mommy ta sake harzuka ta yi kanta zata sake dukanta. Ya sa hannunsa ya tare ta samu nasa hannun. Itama kuwa sai da taji a jikinta saboda kare dukan da ya yi.

 “Au a gabana zaku nuna min cin amanar da ku ka yi wa Amira”. Yana kokarin yi mata bayani ita kuwa sai zage zage ta ke dada surfa musu. Ganin haka sai yayi banza da ita ya mai da hankalinsa kan duba Zahran da shatin dukan da Mommy ta bar mata.

 Ganin ba ribar da zata ci a wajen sai ma bakin ciki da ta ke dada kunsa sai ta fice da niyyar turo musu sarkin yakin ta saboda ta san shi zai sama mata abin da ta ke so.

 A inda ta tafi ta barshi nan ta dawo ta same shi zaune a kujerar falon. Nan kuwa ta ci gaba da zayyane masa irin cin mutuncin da aka yi mata a gidan su Faruk da kuma wanda aka yi mata a gidan Mallam Jibo.

 Sofi jin bakin labari na ta rasa Faruk ma a wan nan karon. Ta fita a guje ‘yar motar da tayi musu saura ta dauki wani katon dutse ta kwadawa glass din motar na gaba. Nan kuwa ta tarwatse.

 Saddam ga jin haushin rashin Zahra da ya ke jin tabbas ya yi sai kawai ya fara dukan Sofi ta ko ina ya na fadin “shegiya duk ba ke ki ka ja mana wan nan talaucin ba. Banza mai kashin tsiya. Ai ko nine Faruk ba zan aure ki ba. Shi ma Baffan ai saboda ya san ke ambasadon mutuwa ce shi yasa ya guje ki. An haife ki iyayensa sun mutu. Ranar da aka sake ki shi kuma Faruk kika kashe masa mata. Kika jayo mana talaucin da mu ke ciki. ‘Yar motar da muke hawa kin nakasa ta. Ke ma yau sai na karyaki a gidan nan”.

 Da kyar Momi ta kwace ta a hannunsa, saboda Honourable yana tasowa wani jiri ya kwashe shi ya zube a wajen.

 Bayan an gama da kwatar Sofi wacce ta daku a hannunsa suka dauki Honourable su ka tafi da shi asibiti. Saboda lahanin da Sofi tayiwa motar sai a dan sahu suka tafi.

 Can kuma bayan ‘yan wasu gwaje gwaje aka tabbatar musu da cewar Honourable ya samu cutar shanyewar barin jiki.

 Nan kuma suka shiga sabon tashin hankali. Amma fa duka duka kwana biyu kawai Momi ta yi da shi a asibitin ta ce ta tafi ta nemo kudin da zata kaishi asibiti kasar waje, ta bar jinyarsa a hannun Saddam.

  Da ga haka ta bude shafin maula. Duk mutanen da Honourable ya yi mu’amala da su sai da ta rinka binsu da nacin su taimaka mata saboda larurar mijinta.

 Ta kuwa samu dan abin da ta samu amma fa shi mai jinya yana cikin lahaula wala kuwwata, saboda dan jinyarsa ba wata kula ya ke ba shi ba. Shima gidan wani abokinsa ya koma da zama can ya ke yini sai dare ya leka asibitin.  

    ***********************

Comments

Popular Posts