☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* 39 & 40 ☘️☘️☘️☘️☘️

 


           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/


TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09



CHAPTER THIRTY NINE

 A gidan Honourable kuwa an sayar da gida miliyan hamsin da bakwai, amma ba su cika kudin diyya ba sai da Mommy ta hada da duk wata ajiya ta ta.

 Tashin hankali dai sun gan shi a wan nan lokaci. Gaba daya daga ita har mijin nata sun yi wata irin zubewa ta farat daya. Amma ita kuwa shalele Sofi ba abin da ya dameta.

 Harkokin ta na social media ba wanda ta fasa. Kullum ta na kan waya. Ku san ma mu ce ta manta da rasuwar yayarta da kuma bawan Allah da ta taka da mota ya mutu.

 Ba bu alamun nadama na abubuwan da ta aikata a dan kwana biyun nan. Ita yanzu kulla yadda zata fitar da kanta ta ke yi. Saboda ba ta hango yadda za ta iya rayuwar talauci da ta hango iyayenta na kokarin zunduma a ciki ba.

 Shawara suka yanke da Saddam akan ta yi wa Mommy magana su tuntubi Faruk da ya aureta a makwafin yayarta. Da ta nuna masa ita ba zata iya dawainiyar yaran ‘yar uwarta ba. Shi ya ce da ita “ki share da ma ba Zahra ke kula da su ba. kin ga ni ba wani aiki zan samu ba. Idan kin auri Faruk tun da shima Don ne sai mu zauna a wajenki, ta ci gaba da kula da yaran”.

 Da wan nan shawara kuwa suka tunkari Mommy. Ita ma kuwa ta amince da wan nan shawara. Ba tare da wani dogon bayani ba ta umarci Honourable da ya je gidan su Faruk yayi musu albishir da cewa an basu kanwar marigayiya ta maye gurbin yayarta.

 Da kuwa murna Hajiyan Faruk ta karbi wan nan shawara, saboda ita da suka ce kanwar marigayiya ta dauka suna nufin Zahra.

 Duk da Faruk yana cikin shaukin rashin matarsa, amma yayi na’am da wan nan shawara. Saboda ko don yaransa bai ga wanda zai rike masa su sama da Zahra ba.

 Zahran ce ma ana tunkarar ta da zancen sai kuka. Saboda har yanzu ta kasa sabawa da rashin yayarta watau Amira.

 Kusan ko yaushe ta kalli yaran musamman jariri da ya ci sunan Muhammad Hafiz, sai Zahra ta yi masa lakabi da Amir saboda yayarta. Duk lokacin da ta kalle su  sai ta yi kuka. Ba ta yarda kowa ya taba yaran idonta na kansu. Su ma kuwa ko yaushe suna makale da ita.

 Ga hutun makaranta ya kare ya kamata su koma Warri, amma alhinin mutuwar da ta same su shi ya hana Abbansu nuna sha’awar tafiya da su. Shi kadai ya koma wajen aiki.

 Amma fa yana can din ma bini bini ya bugawa Zahra waya “ina kaza yake”? ko a ji yana tamabayar “ya ya ku ke kaza”.

 Hajiyarsa na hankalce da shi. Hakan ya dada sa ta yi na’am da shawarar Mommy na bawa Faruk kanwar matarsa. Ita a  lissafin ta Zahra su ke nufi. Ita kuma Mommy tata shagwababbiyar ‘yar ta ke nufi.

 Wata rana Hajiyar su Faruk ta yi bakuwa kanwarta ta zo, ta ke sanar da ita alkhairin da Mommy ta yi musu, ta kuma sanar da ita, ta rasa yadda zasu sa Zahra ta amince da zancen.

 Dariya Inna Shatu ta yi san na ta ce  “bar ni da ita. Kira ta ki ga yadda zamu yi da ita”.

 Zahra ta zo Inna ta ke tambayarta yaranta, ta na murmushi ta ke amsa mata. Ana haka sai ga su sun shi go. Ba su nufi ko ina ba sai wajen Anti Lalan su.

 Inna Shatu ta kalle su tayi dariya ta ce “’ya’yan Anti Lala, na ga yanda za a yi ranar da za ta tafi na ta gidan mijin”.

 Jijjiga Amir da ke kokarin yin bacci ta ci gaba da yi san nan ta ce “ai ni Inna ba inda zani. A nan zamu zauna a wajen Hajiya ni da su Amal”.

 Dariya Innan ta sake yi san nan ta ce “Ina! Haka ba za ta sabu ba. Ki na diyar musulmi ki ce ba zaki yi aure ba. Ai aure dole ne Zahra”.

 Hajiyan itama ta ce “ai ni ma kuwa ba zan zauna da ita ba aure ba”.

 “Tab ai kuwa sai dai ya tafi da mu

dukkanmu”.

 Hajiyar su Faruk ta sake cewa “ai kuwa Zahra ba wanda zai yadda ya aureki da yara uku”.

 Wani irin tsoro ne ya bayyana a fuskarta domin tabbas ta hararo kalubalen da ke kokarin fuskantarsu ita da su Amal. Ta tuno Hamida da ke kanwarta an aurar da ita. Humaira da ta ke sa’arta jira ake ta karasa karatu itama a aura mata Ibu abokin yayansu.

 In kuwa haka ne tabbas ita ma ba zata tsira ba.

 Ba ta gama da wan nan tunani ba sai taji muryar Innan Shatu na cewa Hajiya “kin ji labarin matar da ta kona ‘yar mijinta da tafasasshen markade”?

 “Naji jiya ana fada a inda ranka. Wai uwar yarinyar ta rasu ya kara aure shine matar uban ta kwara mata markade”.

 Inna Shatu ta sake cewa “sai ma kin ga hoton yarinyar da kyar ta rayu”.

 Hajiya ta sake cewa kin ga wanda ita kuma mijin ne ya murde wuyan yaron saboda ba dan sa bane dan matar da ya aura ne”.

 Inna Shatu ta sake cewa “ai yanzu duniya ta lalace. In dai yaro ba a gaban iyayensa su biyu ya ke ba yana cikin hatsari”.

 Duk su biyun suka kalli Zahra a sace. Tabbas tsoronta ya bayyana karara. Ganin haka sai suka kyaleta suka ci gaba da hirar. Suna dada kuranta yadda matan uba ko mazan iyaye mata ke zaluntar yaran da ba nasu ba.

 Jikinta a sanyaye ta tashi ta shiga dakinsu. Tabbas ba za ta iya zuba idanu tana ji ta na gani a raba ta da su Amal a je kuma ana muzgunuwar rayuwarsu ba.

 Hawaye ta share lokacin da ta tuno mahaifiyarsu ta na ce mata ga amanarsu nan ta ba ta. Amal ce ta fuskanci kuka take yi. Sai ta kwanta a jikinta tana share mata hawaye. San nan tace “Anti Lala ba Abba ya ce mu daina yi wa Mommy kuka ba mu dinga yi ma ta addu’a”.

 Rungumota ta yi jikinta ta kasa ce mata komai.

 Shi kuwa Faruk Abokinsa ne ya bashi shawara da ya dinga kiran Zahra su na dan gaisawa saboda ta sake da shi yadda idan ma zancen auren ya bullo zai samu hadin kanta.

 Da misalin tara na dare ya kirata. A lokacin tana goye da Amir bayan ta bashi madara ya sha tana kokarin rirriga shi ya yi bacci. Su Amal suna wajen Hajiya suna karatun islamiyya kamar yadda ta ke yi musu duk sanda su ka zo hutu wajenta.

 Wayar Abban ce ta katse ta daga tunanin da ta wuni ta na yi, wan da ya danganci tattaunawar da Inna Shatu da Hajiya suka yi dazu.

 Bayan sun gaisa ya dan tambayeta wasu abubuwa da suka dangancin yaran. Har kamar zai ajiye sai ta ce “MH Abba, yanzu tunda Anti ta rasu zaka kara aure”?

 “Me zai hana Anti Lala. Duka duka shekarata arba’in da biyu. Kin ga kuwa ai ban tsufa ba”.

  “Mh kuma Abba idan ka yi aure zaka bawa matar taka su Amal”?

 Take kuwa kwakwalwarsa ta hasko masa tsoron Zahra. Ba ta son rabuwa da su Amal.

Shima sai ya samu gangara na yadda zai karkato da hankalin Zahra kansa.

 Sai ya kama tashar da su Hajiyansa suka fara dora Zahra a kai.

 “Zan ba ta Zahra”

 “Kuma ko zata dake su ko kuma za ta ci zalinsu ba zaka hana ta ba”.

 “Wai! Anti Lala ina na sa in hana ta. Haka zan hakura in barta ta yi musu duk abin da ta ga dama. Tun da haka Allah ya kadarto mana”.

 “To ni ka barni in zauna in ci gaba da kula da su Amal. Sai kayi aurenka”.

 Ajiyar zuciya ya yi. San nan ya yi amfanin da damar da hirar ta su ta bashi. Ya ce “Anti Lala mu saukaka lamarin. Ke ki hakura ki kar be mu dukkanmu dani da yaran naki”.

 “Ai daman na ce maka ni zan zauna da su kai kuma ka zauna da matarka”.

 Dariyar kuriciyarta ya yi, san nan ya ce Anti Lala ke nan. Ai ke ma kin san ba matar da zata yarda ta zauna gida daya da kyakkyawar budurwa irin ki”.

 Kunya zancen ya bata. Sai ta kashe wayar kawai.  Amma duk da haka bai hakura ba. Sai ya dinga fakewa da sakonnin ta waya. Kuma kusan duk kalaman da zai tsarata da su sai ya yi amfani da haruffan da za su sa ta ji matukar tausayinsa.

 Ga yawan nanata mata kalaman marigayiya Amira da ya ke yi domin tunatar da ita amanar da ta ba ta.

 Duk da matarsa ba ta dade da rasuwa ba, saboda ko arba’in ba ayi ba, amma gaskiya yaji hankalinsa ya yi matukar kwaciya da hadin auren da iyaye ke son yi tsakanin sa da Zahra.

 A haka ya dan dinga jan ra’ayin ta, har ta fara sakewa da shi. Ba dai wata hirar soyayya a tsakaninsu, amma fa akwai nuna kulawa da mutuntuwa a tsakaninsu.

 Ga shi dai ba gari daya suke ba, amma ko abinci ya ci sai ya bata labari. Ba ya la’akari da shekarunta, amma hatta shawara ya kan tambayeta a kan lamuransa.

 Hajiyarsa tayi matukar murna da wan nan ci gaba da aka samu tsakanin danta Faruk da Zahra. Hakan ya sa ta aikawa da kawarta, watau Mommy akan idan sun amince ranar arba’in din Amira adaura aure.

 A bangaren su Mommy kuwa sun hakura sun koma gidan wani abokin huldar Honourable, inda ya basu sashen baki na gida da zama.

 Ita Mommy niyyarta, idan anyi auren Sopy da Faruk ta koma garin Warri da zama da sunan zata sa ido a kula da yaran Amira. Zahra ta auri Saddam ta ci gaba da kula da gidan Faruk da kuma yaransa.

 Shi kuwa Amir ba sa ta ta sa, saboda don yayi sati ba ya gida ba sabon abu bane. Amma duk lissafin na ta, ba ta lissafa yadda zata yi da mijin da ita ta taimaka ya lalata rayuwarsa ba.

 Bayan sun gama hada lissafimsu suka yarda da ranar da aka saka ta auren Faruk da a zatonsu Sofi.

 Nan kuma Sofi aka shiga wani sharafin na yada wa a duniyar social media cewar ai saboda mutuwar yayarta aka fasa aurenta da DR AMA saboda ta auri mijin yayar ta ta, ta kuma kula da yaran da ta rasu ta bari.

 Sai fadi ta ke wai DR AMA har kuka ya dinga rusawa a gidansu saboda an fasa auren sa da ita.

     ***************




CHAPTER FORTY

    A bangaren gidan Mallam Jibo kuwa, duk da dai har wan nan lokaci yana fushi da Baffa saboda abin da yayi masa na datse igiyar aure da ya yi tsakaninsa da ‘yar uwarsa watau Sofi. Datsewa kuma ta har abada. Amma hakan bai hana shi shigewa gaba wajen karbar kudin auren da iyayen Faruk watau mijin marigayiya Amira, su ka kawo ba.

 Sun kawo kudin aure sun kuma roki arzikin a daura auren ranar sadakar ar’bain din Amira. Ya amince da haka, amma duk da haka ya nuna su ba shi lokaci ya je ya yi Magana da wan mahaifin su Zahra, watau surukin shi Faruk din.

 Baffa ne da Wabili ta gaya masa zancen kawo kudin, ya bugawa Faruk waya ya sanar da shi cewar kudin da suka kai na gaisuwa ya amshe shi a matsayin sadaki.

 Dariya Faruk yayi san nan ya ce “gaskiya kanina ba zan yarda ba. Na ga alama sadaka ka ke son ba da Zahra. Ba kuwa zan lamunta a tauye mata wani hakki ko ‘yanci na ta ba. Ta fi karfin haka. Zan aure ta da da duk abun da ake auren kowacce yarinya.

 Ni ta taimka ba ni na taimake ta ba. Ta yarda da ni duk da ratar shekarun da na bata. Ta yarda ta karbe ni ba tare da la’akari da yawan ‘ya’ya da na ke da su ba.

 Kaga kuwa ya kamata in kyautata mata fiye da kowacce irin mace da zan aura”.

 Murmushi Baffa ya yi san nan ya ce “duk da haka ka lura da cewar rashin da muka yi na Amira shi ya kawo dangantakar da ke shirin kulluwa tsakaninku. Shi ya sa na ga kamar ya kamata mu kashe duk wata bidi’a, saboda alhinin rashin da muka yi”.

 Amma bayan Faruk ya sanar da Hajiyansa yadda suka yi da yayan Zahra. Sai suka yanke shawara kar a kai wani abu na al’ada gidan su Zahran.

 Amma fa ba karamin shirin tarba su ka yi mata ba. Hatta gidan da suka zauna  aWarri ya canza musu wani hade da sanya sabbabin kayan gidan a sabon gidan.

 Ya yi haka ne saboda ya ragewa Zahra tunanin Amira wanda ya san zai dinga yawaita bijiro ma ta a duk lokacin da ta ga gidan da suka yi rayuwa tare.

 Sai yake ganin canza mata muhalli zai bata damar sakewa da shi ta kuma rage damuwa da rashin yayarta da ta yi.

 Hatta da kayan lefe, Hajiyarsa da ‘yan uwansa mata sun hada mata lefen na garari, amma sun yanke shawara ya ajiye a wajensa sai ta je gidan ya bata.

 Allah ya sani daurewa zuciyarsa kawai ya ke saboda kar mutane su gane yana zumudin auren Zahra.  Tun da a ka yi masa tayin auren ta, sai yaji zuciyarsa farat daya ta fada kaunarta.

 Allah ne shahidinsa, a lokacin da ta ke zaune a  matsayin kanwar matarsa bai taba raya wani abu a kanta ba. Amma yanzu karya zai yi idan har ya ce bai fada kogin kaunarta ba.

 Amira na da kwana talatin da biyar da rasuwa ya taho Kano domin addu’ar arba’in dinta da kuma daurin aurensa da Zahra.

 A nan Kano ma kuma Sofi ta takura da lallai Mommy ta je gidan su Faruk taji ya ya batun shirye shirye. Saboda ta tama har dinner, barbeque da kuma kauyawa day za ta yi.

Jira ta ke Faruk ya shigo a yi maganar venue da kudin abinci.

 Ta riga ta sa wata fashion desingner ta yi mata dinkunan biki. Ta sa Mommy ta karbo ma ta bashin lesussuka saboda kar lokaci ya kure ba ta yi dinki ba.

 Sau biyu tana bugawa Faruk waya tana masa maganar shirye shiryen biki, amma ya sanar da ita ba komai ta bari idan ya shigo gari zai neme ta.

 A tunaninsa tanadin bikin sa da Zahra ta ke yi, wanda hakan ya sa shi jin dadi ganin kamar hakan na nuna dada amincewar Zahra da shi ke nan.

 Ya kuma ji dadin ganin yadda Sofi ta dauki al’amarin na ganin ta na kokari taimakawa Zahra da shirye shiryen bikinta.

 Mallm Jibo ganin an kawo kudi Honourable bai ce ma sa komai ba, ya san ya shi zuwa domin ya yi masa bayani.

 Da tambaya ya gano gidan da suka koma. Shima gidan da gani mai shi ya ci ya tada kai da naira. Amma abin takaici shi ba a gari yake ba. Ga kuma bangaren babban dansa wanda ke zaune a kasar waje sai ya shekara biyu bai shigo Nigeria ba.

 Amma ko nan din ba su ci arzikin a basu ba. Sai wani bangare da idan danginsa suka zo daga kauye nan ake saukarsu. Nan ya bawa Honourable da iyalisa. Wajen a kuntacce yake.

 Daki biyu ne da bandaki guda daya, sai kuma falo da dan karamin kitchen. Ko tiles ba bu a sashen saboda ita ma matar gidan irin Mommy ce. Ita ta hana shi ya saka musu tace wai ba su san shi ba lalata shi za su yi tun da ba sanin darajar sa suka yi ba.

 To wan nan bangaren shi aka ba wa Honourable da iyalinsa. Momi da Sofi a daki daya. Honourable da Saddam a daya. A dan lokutan da Amir kan shigo gidan, a falon gidan yake yada zango.

 Ballantana ma da ya kasance shi da rana ya fiye shigowa saboda reverse da ya yiwa rayuwarsa. Da rana ya ke zaman gida ya yi bacci. Da daddare kuma ya fice sharholiyarsa.

 Idan kuwa ya shigo duk abin da yayi ido hudu da shi in dai zai sayu a kasuwar tsaye to kuwa ya zama nama. Hatta kwan fitila kwance shi ya ke yi ya sayar.

 Hakan ya tilasta musu, idan gari ya waye sai Honourable ya yi saurin kunce kwayayen fitilun gidan, har sai ya futa san nan su mai da su.

 Mommy kuwa da Jakarta take yawo saboda ko yaya ya laluba ya samu dan canji, kwashewa zai yi.

 Dan zaman da ya kan yi a falon kuwa haka za ka ji falon ya dumame da kaurin da kuma warin kayan mayensa.

 Ba wanda ya isa ya yi masa Magana a gidan saboda kowa shayinsa ya ke yi. Kwanaki da Sadam ya so ya lafta masa wauta ya tashi yana zazzaginsa saboda ya dauke masa waya, da kyar mai gadin gidan da yake civil defence ne ya kwace shi a hannunsa.

To a wan nan gida mallam Jibo ya same su domin ya gaya wa Honourable batun kawo kudin auren Zahra da iyayen Faruk su ka yi da kuma ranar da suka bukata a daura auren.

   Ai kuwa daga Honourable har matarsa ba wanda ya saurare shi. Sai ma cin mutunci da suka raka shi da shi. Magana daya ce ta daure masa kai in da yaji Mommy na fadin ya jira nan da ‘yan kwanaki zai ga abin mamakin da za su yi.

 Idan da yana ganin ya ci riba da raba auren Sofi da Baffa to itama Sofin ta samu miji gangariya, sai dai bakin ciki ya kashe su.

 Hakan ya sanya bai samu sukunin yi musu bayanin auren Zahra da mijin marigayiya Amira ba.

 Ana haka Ibu shima ya zo da kokon bararrsa na a hada daurin aurin Zahra da Humaira, samun amincewar mama Barrister sai Baffa ya sanya ranar daurin auren da na Zahran.

 Kamar kuma yadda ya yanke hukunci ba ya san al’ada a harkar auren Zahra haka ya yanke a kan na Humaira.

 Ibun ne ya ce “to kai wai ina ruwanka. Saboda kawai an dan yankar ma wani bangaren na girma sai ka dinga hana miji ya yiwa matarsa hidima”?

 Dariya Baffa ya yi Ya ce “idan ban zuga Mama Barrister ta mayar da auren nan da wata shekarar ba”.

 Sassuta murya Ibu ya yi duk da ya san wasa ya ke yi masa. Ya ce “yi hakura babban yaya, amma ba zaka gane tanadin da na yi na tarbar Humaira ba ne”.

 “Look at you, har ni za ka nunawa yanda ake tarbar macen da za a aura. Ni da na fara son tawa tun tana tsumman goyo. Kai kuwa da sai da ta girma ka fara naka takun kaunar”.

 Dariya Ibun ya sake yi, san nan ya ce “ai kai na san babba yaya ne har a duniyar soyayya, amma dai a taimaka min in dan yi ko da kwatar abin da na yi niyya ne”.

 Baffa ne ya ce “ ka yi hakuri kaga ‘yar uwarta da nake son a hada auren ba za ayi wata bidi’a ba saboda rasuwar Amira. And ba zan so Zahra ta ji kamar auren Humair ya fi nata daraja ba saboda kawai an yanke al’ada a nata auren”.

 Ibun ya fahimce shi kwarai da gaske.

Angwaye sun shirya. Gidajen amare ma sun shirya, saboda hatta gwajin jinin da masallatai kan bukata saboda tantance lafiyar ma’aurata sun yi suna rike da sakamakon su a hannu.

 Amma fa mutan gidan Honourable ba su san me ake ciki ba. Jira suke Faruk ya zo sadakar ar’abain a saka ranar daurin auren sa da Sofi.

 Kuma ko da mommy ta yi wa Hajiya Hadiza watau Hajiyan su Faruk waya ba abin da ta fahimta. Saboda Hajiyan godiya kawai ta dada yi mata da kuma fatan ganin ranar auren Faruk da kanwar matarsa.

Comments

Popular Posts