☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* 37 &38 ☘️☘️☘️☘️☘️



           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/


TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09



CHAPTER THIRTY SEVEN

 Baffa dai ya na can Abuja a hotel shi da Hamida. Saboda yawan ayyukan da suka tunkaro shi wanda kamfaninsu ya wakilta shi, ya sanya shi zabar Abuja a matsayin garin da zai yi hutun amarcinsa.

 Duka duka ba su fi sati a garin ba, amma daga shi har Hamida sun yi kyau na ban mamaki. Duk wanda ya gansu ya san su na cikin farin ciki.

 A bangaren Honourable kuwa ganin takurar matarsa da kuma ta Sofi ta yi yawa, ya sanya shi yanke hukuncin daura auren Baffa da Sofi duk da rashin sanin inda Baffa yake.

 Mommy ce ta ba shi karfin gwiwar yin hakan, saboda ta ce malamin da ta je wajensa ya sanar da ita cewar daura auren shine makarin asirin da Mallam Jibo ya yiwa Baffa.

 Nan take kuwa ya dau wan nan shawara ta ta. Ya buga kati ya kuma gayyaci jama’unsa, Mallam Jibo da Baffa ba su da labari. Saboda shima Mallam Jibon Mommy ta ce a boye kar a sanar da shi sai bayan an daura, saboda kar ya yi wani surkullen ya bata musu shiri.

 Shigowar Baffa ke nan daga wajen aiki, ya shiga wanka. Wayarsa da ta dauki karar da ya ja hankalin Hamida. Ganin Zahra ce sai ta yi saurin daukar wayar.

 Da sallama ta amsa wayar. Zahra cikin tsokana ta ce “amarya mai gudun hijira”.

 Dariya kawai tayi ba tare da ta amsa tsokanar ta ta ba.

 Bayan sun gama gaisawa da dan tsokane tsokanensu. Sai Zahra ta dan kaurara murya alamar zancen ta mai muhimmanci ne.

 “Ina Ya Baffa” tace da ita.

 Kafin ta amsa mata ya fito daga bayin. Mika ma sa wayar ta yi tana fading “ga Zahra ta bugo maka waya”.

 Wayar ya karba. Amma bayan gaisuwa sai Hamida taji shi cikin tashin murya yana fadin “What”?

 “Yaushe”?

 “OK gani nan zuwa”.

 Wayar ya ajiye cike da sauri ya juya ya kalli Hamida cikin tashin hankali yace “yi mana packing kaya. Yanzu za mu tafi Kano”.

 Itama cikin tashin hanakali ta ce “ya Baffa lafiya? Me ke faruwa”?

 Har zai yi banza da ita, amma ga nin tashin hankalin data shiga har ta fara zubar da hawaye, sai ya yi murmushi ya  ce “Hey come on African Queen. Ba abin da ya faru, wani abu ne ke shirin faruwa a gidan Honourable, amma ba abin da ya faru da mutan gidanmu”.

 Tun da suka shiga motar da zata kai su airport ya ke ta bugen bugen waya domin samun jirgi zuwa kano.

 Allah ya taimaka kafin su isa filin jirgin saman ya samu jirgin zuwa kano. Su na isa ya sake daukar taxi zuwa unguwarsu. Ko gida bai shiga ba, ya sauke Hamida tare da umarnin kar ta sanar wa da kowa komai. Ta nuna musu dawowa kawai suka yi. Shi  kuma ya wuce wani waje. Bai tsaya ko in  ba, sai bakin ATM. Sai da yayi amfani da katin banki hudu kafin ya dau kudin da yake jin za su ishe shi.

 Tabbas taro ne babba, saboda ga mutane nan gungu gungu alamar taron ya dau harami. Amir ne ya fara hango shi. Duk ya dafe yayi bakikkirin da shi alamun wiwi da sauran kayan maye sun dafar da shi.

 Da hanzari ya nufi wajensa. Har kasa ya durkusa ya gai da shi kamar ba shi ne babba ba. Nan kuma ya ci gaba da ladabinsa na ‘yan shaye shaye. Fadi yake “babban Engineer. So nake ka bani kudin form in saya. Makaranta na ke son komawa, saboda ni ma in zama injiniya kamar ka”.

 “Kar ka damu zan san abin yi. Yanzu nuna min inda su Daddy suke”.

 Cikin hanzari yayi masa jagora zuwa inda suke zaune shida manyan bakinsa. A ladabce ya gaisa da kowa. Shi kuwa Honourable sai nuna shi ya ke a matsayin dansa.

 Nan dai aka ci gaba da hidimar daura aure, saboda yanzu ya dada yarda da maganar malamin mommy. Ko ba komai daga maganar auren ga yaron ya zo har gida da kansa.

 Aka yi siga. Daddy ya tsaya a matsayin waliyyin ango. Yayin da wani abokinsa ya zama waliyyin amarya.

 Baffa da kansa ya mika ambulan mai kudi naira dubu dari biyar, a matsayin sadakin Sofi. Ana daura aure, Saddam ya shiga cikin gidan da albishir din Baffa da kansa ya kawo kansa aka daura auren da shi.

 Mommy fadi take yi “Malam ba ya karya. Ai   na san ba a banza yaron nan ya kewa babansa haka ba. Shiga tsakani ne”.

 Sofi kuwa sai murna ta ke rabin burinta ya cika. Saura kawai korar Hamida da iyayenta daga rayuwar Baffa shine daya burin na ta.

 Cike da murna Honourable ya shigo gida. Ga dai gidan a cike ba laifi, amma haka ya ratsa ya shigo. Ya kira Mommy. Sofi na ganin shigewarta ta mike ta bi bayanta.

 Daddy na zaune akan doguwar kujera, Sofi ta fada jikinsa cikin murna. “Daddy na gode da ka kawo min DR AMA cikin rayuwata”.

 “Kar ki damu auta ta. Zan iya baki koma menene ki ka nema a rayuwarki”.

 Mommy ta karaso ta zauna kusa da shi. “Yanzu ka yarda da abin da nake gaya maka”.

 “Kwarai na yarda. Ga zahiri kuwa na gani. Yaron nan fa da shi aka daura auren nan”.

 Ya karkace ya fito da ambulan din kudi daga aljihunsa ya mikawa mommy ya na fadin “ga sadakin ta shi ya biya da kansa”.

 Amira da su Amal da kuma Zahra suma suka shigo domin kakabin abin da suka ji ana fada akan an daura auren Sofi da Baffa.

 Kowa yana taya ta murna, amma Zahra ba ta ce komai ba. Sofi ta kalle ta a yatisne ta ce “OK har yanzu ba ki saki ba ke nan. Na ga kanki yana rawa. To ki kiyayeni. Gidan Baffa da duk dukiyarsa ta dawo karkashi na. Idan kin bi ni ki ci arziki, idan kin ki kuwa ba wani babban aiki ba ne in yi waje da ke da ga lamuransa baki daya”.

 Mommy ma sai da ta tabe baki. San nan ta ce “ai ni Daddy nama so da ka hada daurin auren da na Zahra da Saddam tun da dai ya nace ita ya ke so”.

 “Shima mai sauki ne” Honourable ya fada wa Mommy. Ya mika mata ambulan din sadakin Sofi, Mommy ta ce ni me zan yi da shi. Mika mata tun da nata ne.

 Yana mikawa Sofi kudin yana fadin “ai da kike gaya min asiri Jibo ya yi ya raba ni da Baffa ban yarda ba sai yau din nan da na ga zahiri. A she kuwa yadda malamin nan ya fada auren ne makarin asirin”.

 Ai na gaya maka” Mommy ta amsa masa. San nan ta juya inda Sofi ke rungume da ambulan din kudin a kirjinta ta na fadin “to bude mu ga nawa ne mana kin karbi ambulan kin rike”.

 Sofi na budewa ta zaro ‘yan dubu dubu wrapper biyar. Ai kuwa ba shiri Mommy ta saki wata uwar guda kamar ba ita ce uwar amarya ba.

 Sofi ta rungume ta ta na cewa Mommy “So yanzu DR AMA nawa ne ke nan ko”?

 “Na ki ne auta ta” Mommy ta amsa mata tana mai shafa kanta.

 Amira ma ta ce “Mh su Sofi yau buri ya cika, an auri Baffa”.

 “MH MH da saura Amira. Sai na fitar da wan nan Bararojin daga gidansa ya zamana ni kadai ce a cikin zuciyarsa da gidansa san nan burina zai gama cika”.

 Tana fadar haka sai suka hada ido da Zahra wacce ta ke tsaye tana kallonsu cike da mamakin abin da ke faruwa. Ta kasa yardar ma kanta wai Baffa ne ya yarda ya auri Sofi. Ba shiri taji hawaye yana zubo mata.

 Shewa Mommy tayi san nan tace “Au ashe ‘yan bakin cikin su na da yawa. Gwara ma ki dawo ki kama kafar ‘yar uwarki ko ta barki ki dan dangwalin arziki. Amma matso zaki nuna ba kya yi da ita to kuwa ganin Baffa sai ya gagare ki a kasar nan”.

 Ita ma Sofi cikin shagabwa ta ci gaba da cewa “kawai Mommy ba kin ce Saddam ne zai aureta ba. Kuma tun da ita ke kula da gidan Amira da su Amal, kawai a yi auren su tattara su tafi can Warri ta ci gaba da aikin boyi boyin da ta ke yi a gidan Amira. Ita da  da mijinta da ba ya komai su zauna a chalet din gidan”.

 Su Amal ganin tana kuka suka matsa kusa da ita suka rike ta suma suna taya ta kukan. Mommy da Amira da Sofi kuwa sai murna suke tayi.

 Sofi ta baza damin kudin da ta dauko ta yi Fanka da su sai ga wata karamar farar ambulan ta fado daga tsakiyar kudin. A jikin ambular din har da hoton zuciya da kibiya ta ratsa ta tsakiyarta alamun soyayya.

 “Mh lallai matar DR AMA watau har da wasikar soyayya ya aika miki? Bude ki karanta muji abin da yace” in ji Amira.

 Cike da zumudi kuwa ta farke wasikar ta na cewa na san hakuri zai bani saboda yadda ya nuna min da farko”

 Mommy ta ce duk da haka ba da wuri na ke son ki nuna ma sa kin huce ba, na fi son ki dan ja masa aji”.

 Sofi ta mai da hankalinta kan karanta takardar da Baffa ya aiko mata, ya yin da Daddy ya ke bawa Mommy labarin irin mutanen da suka halarci daurin auren Sofi da Baffa. Saboda abokan huldar siyasar sa da dama da suka ji wanda ‘yar Honourable za ta aura sai ga su sun dage domin halartar auren.

 Ba komai ya sanya hakan ba sai fice da sunan Baffa ya fara yi a kasar nan da kuma da dan dama daga kasashen waje.

 Ihun da Sofi ta kwalla shi ya dakatar da su daga tattaunanwar da suke, su ka juya wajenta da hanzari.

 “Ke menene”? mommy ta fada tana mai jijjaga ta. Saboda kusan a sandare ta ke.

 Hannunta na rawa ta mika mata takardar da take karantawa.

 Mommy ta fara karanta wasika kamar haka.

 “Zuwa ga masoyiyata Sofi.

 Ina tayaki farin cikin samun cikar burinki na kasancewa matata. Sai dai idan ba ki manta ba har addu;a na yi akan kar Allah ya kadarta min zama da ke a matsayin matar aure.

   Saboda haka ina mai matukar tayaki bakin ciki saboda iya yau kadai burin na ki ya cika. A yau sha daya ga watan rajab 1440 ni AHMAD MUSA AHMAD DAGUMAWA na sake ki ke matata SAFIYA ILYASU AHMAD DAGUMAWA saki uku. Duk da babu iddata a kanki na bar miki sadakin da na bawa mahaifinki.

 Ki kuma duba cikin ambulan din akwai dubu biyu da bam. Wan nan ki bawa Amir ya sayi form ‘KO ‘YAR KUMBOTSO NAN YA KOMA saboda ya tare ni ya nuna min bukatarsa na san komawa makaranta.

 Kuma kin san shiga university wuya gare shi.

 Daga wanda ba ya burin kasancewa da ke har karshen raywarsa DR AHMAD MUSA AHMAD DAGUMAWA.



CHAPTER THIRTY EIGHT

 Mommy ma yanke jiki tayi ta fada kan kujera ragwab. Sofi kuwa yi tayi kamar ta farfado daga mafarki. Ta fisge wasikar da ga hannun babarta, ta sake karantawa.

 Ba shiri ta saki wani irin mahaukacin ihu kamar hauka sabon kamu. Nan take ta fara al’adarta, watau wurgi da duk abin da ke kusa da ita idan har ranta ya baci.

 Nan ma kuwa ta fara watsi da kayan falon ta na ta na ihun “Wallahi ba ka isa ba DR AMA! Dole ne in zama matarka!”

 Ganin yanayinta ya sanya Amira kokarin tare ta saboda tana tsoron kar ta jiwa kanta ciwo saboda kayan karau na falon da ta ke farfasawa.

 Wata bangaza da ta kaiwa Amira sai gata ta fada kan teburin tsakiyar falon kuma a kan tsohon cikinta.

 Nan kuwa ita ma ta saki wata razananniyar kara. Sofi kuwa ba ta cikin hankalinta ta ci gaba da wurgi da duk abin da ke kusa da ita.

 Zahra ce ta fara lura da mawuyacin halin da Amira ke ciki. Ga glass ya yanke ta ba ta san a ina ba. Ga kuma jinin da ya ke zubowa daga jikin na ta.

 Da sauri ta nufi wajenta ta dago ta tana cewa “sannu Anti”.

 “Kai ni asibiti Zahra”, Amira ta fada a cikin mawuyacin hali.

 Daddy ma da shock ya hana shi motsawa, amma ganin yawan jinin da ke zuba daga jikin Amira sai hankalinsa ya tashi.

 “Yi sauri dauko ta muje asibiti” ya fada cikin tashin hankali.

 Suna fita suka ga inda aka ajiye motar gidan da ta yi saura wayam. Daddy ya tambayi Amir akan wa ye ya fita da mota.

 “Ni dai ai ka san mai rangwamen gata ne, a  gida nan. Mai ciakkaken gata ce ta dauka. Sai dai na ganta kamar ta sha a rungumi zaki yadda ta ke taka motar”.

 

 Honourable dafe kansa kawai ya yi ya rasa abin yi. Amal ce tayi saurin daukar wayar mamanta, ta kira lambar Abbansu.

 Faruk ya na amsawa yaji muryar Amal tana kuka. “Abba ka zo ka kai maminmu asibiti kar ta mutu”.

 “Subahanallahi! Me ya same ta”?

 “Anti Sofi ce ta tura ta kan center table ta fadi akan cikinta” Amal ta amsa ma sa.

 “Innalillahi wa Inna ialihi Raji’un. Gani nan karasowa gidan na ku dama ina kan hanya” cewar Faruk.

 Ko minti biyu ba a kara ba kuwa ya shigo gidan. Gabadaya suka dunguma zuwa asibitin, amma fa duk abin nan Amira ta ki sakin hannun Zahra.

 A asibitin ma ana kokarin shiga da ita dakin theater amma ta ki sakin hannun Zahra. Sai fadi ta ke “ku bar ta zan bata sako”.

 Ganin haka Faruk ya lallaba su da su bari Zahra ta shiga da ita tun da sun ce aiki za ayi mata saboda faduwar da tayi a kan cikinta ana zaton ko ita ko dan da ke ciki ko kuma duk su biyun sun samu lahani.

 Ana shiga da ita dakin ma sai ga nakuda ta taso mata gadangadan. Dama kuma ta dan haura lokacin ta da wajen sati biyu.

 Ganin haka likitocin suka dan dakata da yi mata allurar bacci. Ba ta haura minti goma sha biyar ba, sai kukan baby ya kauraye dakin, alamun ta haihu.

 “Zahra ki kula da su Amal da kuma sabon Baby da na Haifa. Na baki su duka”. Amira na gama fadin haka sai jikin ta ya saki. Sai a lokacin Zahra ta lura da yawan jinni da ke zuba daga jikin Amira.

 Duk da ta tsorata, amma haka ta hakura ta zauna rike da hannun Amira. Duk kokarin likitocin nan sun kasa tsayar da jinin da ke zuba daga jikinta. Da kyar su ka samu suka zare hannun Zahra daga cikin na Amira.

 Ita suka mika wa jaririn bayan an goge shi da zaitun. Allah ya sa ma asibitin idan ka haihu hatta rigar farko da jariri zai saka su suke bayarwa da ba dan haka ba ko riga yaron, ba shi da ita.

 A hijabinta ta dada nade shi san nan ta nufi inda su Mommy suke tsaye duk sun yi jugum jugum.

 Sama da awa likitoci suna kokari a kanta, amma Allah ya yi ikonsa. A nan Amira ta yi shahada. Ta rasu ta bar yaranta guda uku. Amal da Sadik sai kuma sabon jaririn da ta Haifa.

 A haka su ka dawo gida da gawar Amira da kuma jinjirin da ta Haifa. Sun shiga gidan ke nan aka kira wayar Honourable akan yazo police station saboda Sofi ta na tukin ganganci ta bige wani yaro, kuma ya rasu.

 Gaba daya ji ya ke ko gani ba ya yi sosai. Sai wani jiri ne ke dibansa. Ba yadda ya iya, sai wani yayan Mommy ne ya nufi police station din shi kuma ya tsaya jana’izar Amira.

 Daga makabarta police station ya wuce can kuwa ya tarar da iyayen yaro sun kafe akan sam ba za su yafe ba saboda kuwa tukin gangancin da Sofi ta ke yi ne ya jayo rashin dansu.

 Amma tabbas da sun san tsautsayi ne za su yafe. Da kyar suka samu a aka basu belinta da sunan za a tura su kotu a washegari.

 Da Baffa aka yi zaman makoki. Kuma tabbas ya koka da rashin Amira, saboda ko ba komai ita ta dan fi sauran mutan gidan Hoourable mutunci.

 Amal da Sadik kuwa suna lafe a jikin Zahra. Duk inda ta motsa nan za su bita. Ga kuma jariri a goye a bayanta. Duk ta jeme ta fita hayyacinta. Sai Umman Faruk watau kakar su Amal ta yi da gaske ta ke samu ta dan ci abinci.

 Tun da aka yi rasuwar nan, kullum a nan iyalan Mallam Jibo kaf su ke yini suna zaman makoki. Ga kuma abinci wadattace da Wabili kan yi ta kawo.

 Sai dai a bangaren Honourable zirga zirgar kotu ta hana shi zama domin karbar gaisuwar ‘yarsa.

 A gidan Mallam Jibo Wabili ta nuna rashin jin dadin yadda mummunar kaddara ta hana Honourable zaman makoki.

 Baffa yana budar baki ya ce “to ai dama shi ba ya zaman makoki tun da ba sunna ba ce”.

 Umbola Wabili ta yi masa da hannuwanta. Ta ce “waye kuma ya sanar da kai wan nan zancen? Kai abu ba ya wucewa a wajenka a she?”

 Murmushi kawai Baffa ya yi.

 Satin Amira biyu da rasuwa aka yanke wa Sofi hukuncin ta biya iyayen yaron da ta kade diyya. Kusan duk wata kadara da Honourable da Mommy suke da ita har gidan da suke ciki sai da ya salwanta.

 Daddy sai share zufa yake duk da ba wani mashahurin zafi ake yi ba. Mommy sai kuka take lokacin da aka zo ana cinikin gidan su. Da takaici ya ishe shi bai san lokacin da ya zari takalminsa sai gidan Mallam Jibo.

 Kwata kwata Mallam jibo ba shi da masaniyar tsiyar da baffa ya shuka, saboda lokacin  da Honourable ya daura auren Sofi da Baffa ba ya nan ya je Mayo Lofe gaisuwar wani dan uwansa da ya rasu.

 Ya dawo cikin dare washegari labarin rasuwar Amira ya ruske shi. Saboda haka ko wanda zai tsegunta ma sa abin da Baffa ya yi bai samu ba.

 Zagen zagen Honourable shi ya sanya shi ya fara fahimtar me ya faru. Saboda Honourable sai fadi ya ke “sai na yi ajalin Baffa a garin nan. Yadda ya tozarta ni sai na wulakanta shi sama da haka”.

 Mallam Jibo na “fadin dakata yaya. Zauna mu sulhunta me kuma ya faru”?

 “Me zan sulhunta da kai bakin munafuki. Ko kuma shi yaron da ya yi sanadin ajalin ‘yata ya kuma jawo salwantar duk wani abu dana mallaka. Ai na yi alkawarin sai na sa an salwantar da shi a garin nan”, Honourable ya fada cike da zafin rai a lokaci daya kuma yana hankoron kaiwa Baffa duka.

 Shi kuwa gogan duk dramar ta shin hankalin da wan babansa ya ke yi, murmushi ne dauke a fuskarsa.

 Da kyar Mallam Jibo ya lallabi Honourable suka shiga ciki. A nan ne kuma ya samu labarin abin da Baffa ya yi wa Sofi a ranar da aka daura musu aure wanda kuma shine sanadin duk faruwar wadan nan abubuwa.

 A ranar Mallam Jibo ya zagi Baffa yayi fada irin wanda bai taba irinsa a rayuwarsa ba. Ya zage shi da fulatancin Adamawa ya zage shi da na cameroo ya kara da Hausa.

 Baffa dai na tsugunne a gabansa bai iya daga kansa ya kalli Abban nasa ba. Saboda tun da Allah ya halicce shi bai taba ganin sa cikin bacin rai irin na yau ba.

 Tun su Wabili da Hamida na ba shi hakuri har suka hakura, su ma su ka yi shiru. Ga shi su ba su san abin da ya hada su ba, har Abban ya dauki zafi da Baffa ha ka.

 Sun kasa fahimtar fadan Abban in da ya ke ta nanata Baffa bai godewa Allah da ni’imar da Allah ya yi masa da har zuciyarsa ta rika ya dage da son rama abin da Allah ne ya hukunta faruwarsa.

 Ai bayan haka ma sai Abban ya daina amsa gaisuwar Baffa gaba daya. In dai ya yi masa sallama ya amsa daga ita kuwa ba zai kara ba.

 Hamida hankalinta ya tashi saboda tashin hankalin mijinta wanda shi kuma bacin ran Mallam Jibo ne ya saka shi cikin tashin hankalin.

 Ta na kuka ta ke tambayarsa laifin da ya yi wa Abba da ya dauki zafi da shi haka.

 Murmushi ya yi san nan ya ce “wai fa don na ki yarda in yi miki kishiya, shine Abba ransa ya baci”.

 A dan firgice ta ce “ban ga ne ba”?

 “A’a kwantar da hankalinki, African Queen. Wata dunkulalliyar yarinyace Honourable ya aura min, ni kuwa a ranar na yanka ma ta receipt dinta mai gaba daya”.

 Ba ta san lokacin da wata wawiyar ajiyar zuciya ta subuce ma ta ba, jin Baffa ya ki karban auran Sofi. Saboda gaskiya a tsorace ta ke saboda furucin Abbansu na dole Baffa ya a dawo ya kara aure da Sofin.

 Ba dai ta furta kowa ba ne saboda yadda Wabili da Mallam Jibo ke nuna mata ta sadukar da wani bangaren na soyayyarta da ta Baffa, domin ya samu damar gyara dangantarsa da wan mahifinsa.

 Wanda su a ganinsu auran ‘yar wan mahifin sa shine tsani na farko da za a hau domin gyaran wan nan zumunci.

 Ai kuwa ganin jifa ya wuce kanta watau ta tsira da ga kishiyar da ta ke tsoro, sai ta dage da karfafawa Baffa gwiuwa akan fushin da mahaifinta ya ke yi da shi.

 Bayan nan duk sanda ta samu haduwa da Abban nasu sai ta ba shi hakuri da kuma kokarin rarrashinsa akan laifin da mijinta ya aikata.

 Amma fa ba ta bari da ga shi har Gwaggon ta su sun fahimci ta san abin da ya faru ba. Yayyenta kawai ta bari suka san ta san abin da ya hada Abbansu da Baffa.

 Zahra da aka yi komai akan idonta ita ta gaya musu yadda ta kaya a gidan Honourable a ranar da Baffa ya saki Sofi.

Comments

Popular Posts