☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* 33 & 34☘️☘️☘️☘️☘️

 

           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/


TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09



CHAPTER THIRTY THREE

 Baffa ya so ko washe gari ne a daura aurensa, amma su Ba wuro da Ba Jauro su ka kwantar masa da hankalin cewa, waliyyacin auren Hamida na wajensu su kuwa sun amsa sun bashi.

 A niyyarsa ya zauna har sai  an daura auren, amma da sassafe ya samu kiran gaggawa daga wajen ogansa daga can Japan akan lallai ya yanke duk abin da ya ke a Nigeria ya nufi can Japan din saboda su na bukatar sa da wuri.

 Allah ya taimake shi ma iznin shiga kasar na tsawon shekaru biyar ya ke da shi. Hakan ya sanya, ya na da damar shiga kasar ko yaushe ta kama a  tsakanin wan nan shekaru biyar din da hukumar kasar ta bashi iznin yin hakan.

 Bayan yayi sallama da jama’ar Mayo Lofe ya shirya Walid ya ajiye shi a junction din Mambila. Daga nan ya dau shatar mota zuwa Jalingo.

 San nan ya hau jirgi zuwa Lagos.  Sai a lokacin ya kira Abbansa yake sanar da shi Japan ya tafi domin kiran gaggawa da ya samu.

 Kamar ko yaushe fatan alkhairi ya yi masa. Yadda Abban bai nuna masa abin da ya kudirta zai yi da Hamida ba, shi ma bai nuna masa ya san abin da yayi niyyar yi din ba.

 A Mayo Lofe kuwa ‘yan uwan Mallam Jibo da kuma Baffansa da kuma Chibbu sun yanke shawara Hamida ta ci gaba da zama a nan har sai an daura auren ta.

 Ba wanda yayi mata zancen karatun da ta rasa, ita ma kuwa ta hakura da shi saboda a tunaninta karatun ma ya kare, tun da a nan kauyen zata yi aure.

 Su Chibbu sun dauka ita da Baffa suka hada bakin su zo nan. Saboda haka ba wanda ya sanar da ita waye mijin da suka zaba mata.

 Ita ma kuwa ba so take ta sani ba. A tunaninta ta rasa Ya Baffanta, saboda haka ba ta jin akwai wani abu a rayuwa da zata rasa ya daga mata hankali.

 Koma waye su bata bai dameta ba. Amma ta hakikance ita da samun sukuni da farin cikin rayuwa har abada tun da ta rasa ruhin zuciyarta.

 Sai da ya isa Tokyo, san nan ya kira Ibu ya ke ba shi labarin dramar da aka kwasa shi da Abbansa da kuma Baffanin ita Hamidan.

 “But this is not fair. Sama da shekara ina binka ka daura min nawa auren kaki, amma shine kai kaje za ka daura naka in three weeks time”, Ibu yace da shi cikin wasa.

 Shima Baffa cikin wasa ya masa da cewar “Mama Barrister ce mai baka auren Humaira. Kuma tace sai ‘yarta ta shiga final year, saboda haka kara jiran wata shida”.

 “Idan ban je na ballo maka ruwa a wajen Abba ba”.

 “Yi hakuri abokina. Ban shiryar tarbar Abba ba. Bari in ga na mallaki Hamida a hannu, sai in je in yi ta rarrashi. Yanzu abin da nake so, before in taho nan, na yi convincing su Baffa Petal, auren will take place nan da sati uku.

 So please kayi gayyar ‘yan daurin aure ka yi arranging transport na zuwa da dawowa, amma ba na son a ya’da maganar da yawa. Just na kusa kawai”, Baffa ya zayyana masa.

 Cike da dariyar zolaya, Ibu ya ce “ka ce ka gama shirya komai. Amma ya za a yi da Sofi”.

 Kafadarsa ya daga kamar Ibu na ganinsa ya ce “wan nan ba damuwata ba ce. Su karata ita da iyayenta”.

 Nan dai suka dau lokaci suna tsara yadda za su gudanar da hidimar daurin auren.

 Ya kan kira kowa a Mayo Lofe ya gaisa da shi, amma ban da Hamida. Hakan ya dada sa ta sarewa da ta rasa Ya Baffanta. Ita kuwa Chibbu ta dage shirya amarya.

 A irin tuararukan da Baffa ya ke kawo mata tsaraba ta dauki biyu ta kwaba lalle da kanunfari. Ta juye turaren kwalaba biyu ta kawo goro ta bara shi ta wurga cikin kwabin lallen.

 Kullm sai ta yi wa amarya turgeza da shi. Kafin sati kuwa sai wani irin sulbi da haske fatarta ta dada yi.

 Humaira da Zarah sun yi bakin cikin jin abin da ya faru, amma da suka kira yayansu domin su jajanta masa sai suka ga kamar bai damu da rashin da su ka dauka yayi ba.

 Saboda ko Walid da ya dawo bayan kwana uku da ya yi a Mayo Lofe ba shi da masaniyar abin da ke faruwa.

 Ibu dai aiki ya same shi. Shine gayyatar abokai zuwa Mayo Lofe daurin aure. Barrister ce ta taimaka masa da gyaran bangaren Baffa na gidan Abbansa.

 Aka wanke gida aka jera komai na gidan masu kyau da tsari. Naira dai ta sha kashi. Shi dai Mallam Jibo da mai dakinsa Wabili, Baffa ya shaida musu Ibu zai turo a gyara masa bangarensa.

 Haka zalika daga can Mayo Lofe ba wanda ya sanar da su hukuncin da suka yanke. Hatta ranar auren da suka yanke na Hamida ba wanda ya sanar da su.

 Baffa Petal dai ya sanar da su tabbas zai aurar da Hamida ga mijin da ya dace da ita. Daga haka kuwa bai kara musu bayanin komai ba.

 Addu’a kawai suka dage da ita, ta neman zabin abin da ya fi alkhairia ga shi Baffa da kuma Hamida.

 Amma duk da haka Wabili tana jinjina abin da zai faru idan Baffa ya dawo daga tafiyar gaggawa da yayi ya tarar an aurar da Hamida ga wani.

 Yayin da shi kuma Honourable ya rike wuta. Ya takura Mallam Jibo akan lallai ya tabbatar da Baffa ya dawo za a daura masa aure da Sofi. Ita ma kuma Sofi alkwarin da su ka yi mata ke nan.

 Nan kuwa mommy ta shiga shirin biki gadan gadan. Hatta Amira da take ta she da tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe, amma ita ma ta dage da shiga cikin hada hadar auren kanwarta.

 Zahra dai ido ne nata. Amma ko kadan hadin auren yayanta da Sofi bai yi ma ta ba. Musamman idan ta ga yadda ita Sofin ta dauki lamarin.

 Har wani girman kai na musamman ta kara. Abu kadan ta ce da Zahra “ki yi hankali ni matar yayanki ce. Kuma nan gaba kadan sai yadda na ga dama za a yi a gidansa. Idan kin bini a tafi dake. Idan kuma kin ki, kina ji ki na gani in yanke hulda tsakaninku”.

 Hankalinta ba ya dada tashi sai ta ji irin hudubar da mommy ta ke yi mata. Kullum hudubarta ga ‘yar  ta ta shine “ki dage da kin shiga gidan ki karbe duk takardun kadarorinsa, komai ya dawo hannunki. Duk kuma yadda zaki yi ki raba shi da mutan gidan Jibo ki tabbatar kin yi”.

 Ita kuma Sofi ta kan amsa mata da cewa “dama Mommy zama zan yi in zuba musu ido. Ai duk sai na yanke duk wata hulda da wadannan bararojin. Ke dai Momi sha kurumin ki. Kwanan nan zan zama wata classy babe. Wai nice Matar DR AMA”.

 Sai ta yi Shewa ta murnar jin dadi yadda abubuwa suka zo mata. Hatta diplomar da take yi a Management ta zubar da ita ta mai da hankalinta kan auran Dr AMA.

 Abin da Zahra ta kasa ganewa Ya Baffa ta ke so ko kuma matsayin Ya baffa da kuma kudinsa. Saboda ta lura daukakarsa ta fi birgeta akan shi karan kansa. Kuma ko labari ta ke bawa kawayenta tafi bada muhimmanci wajen basu labarin irin daukakar da Allah yayi masa.

 Bata cika samun damar waya ba sai ta je gidan Hajiyar Su Amal watau kakarsu ta wajen uba, saboda gidan Mallam Jibo, su Mommy sun hana ta zuwa.

 Ranar da ta je kuwa abu na farko da ta fara yi shine kiran Humaira domin ta sanar da ita abin da ke faruwa.

 Humaira ta tintsire da dariya tace “can you keep a secret? Because Ibu ya ce kar in gaya wa kowa”.

 Da hanzari Zahra ta ce “don Allah gaya min menene. Na ga ke hankalinki bai tashi ba a kan labarin da na gaya miki na yadda Mommy da Sofi suke son su janye Ya Baffa daga kowa”.

 “Ba wani tashin hankali” Humaira ta amsa mata.

 “Kina ji fa sun ce idan akayi aure su za su raba shi da mu baki daya” Zahra ta fada a tsorace.

 “That will happen idan har ta aure shi” in ji Humaira.

 “Ban gane ba”?

 “Well Ibu told me that Ya Baffa ya bi Hamida Mayo Lofe and su Baffa Petal sun yarda za su daura musu aure. Because mama Barrister suka sa tana kokarin gyaran section din Ya Baffa.

 But mind you kar ki sanar da kowa saboda ko Abba da ita Gwaggo ba su san da wan nan shirin ba, saboda Ya Baffa yace he cant trust them kar su rusa masa tsari”.

 Wata dariyar mugunta da Zahra ta barke da ita, san nan ta ce “tab ashe zan sha kallo ranar da zancen nan zai bullo a gidan mu”.

 Humaira tace “ke dai remember kar ki sanar da kowa. Because Ibu ma ya kasa daurewa ne ya sanar da ni”.

 A ranar ma kuwa da Zahra ta koma gida da ace mutan gidan sun lura da ita za su gane tsabar farin ciki da ta ke ciki. Amma hankalinsu na kan tsara yadda bikin zai gudana cikin tsari.

 Ga wani uban bill da aka tsara ana jiran Baffa ya dawo daga Japan ya bada kudin hidimar bikin.

 Duk kokarinsu na son suyi magana da shi ya ci tura, saboda shi kansa mallam Jibo tun wayar farko da yayi masa ya sanar da shi tafiyar gaggawa ta same shi, bai sake kiransa ba.

 Kuma da Honourable ya takura, da ya bashi lambar Baffan ya bashi. Sun gwada amma sun kasa samunsa. Kun san kwararren Engineer. Idan ka same shi a waya, to ya so ka same shi.

 Idan bai so ba, ba network din da zai sa ka same shi a  layinsa. Bugawa zaka yi ta yi wayar ta ki shiga.

 A gidan Honourable ana ta shiryen shiryen aure Baffa da Sofi, yayin da a daya bangaren Ibu ya dage a shirye shiryen auren Baffan da Hamida.

 Saboda gargadin da Baffa ya yi masa na cewar idan komai bai tafi daidai ba to kuwa zai ja aurensa da Humaira sai nan da shekara biyu. Amma idan yayi masa abin da yake so zai lallaba mama Barrister ta ba shi auren nan da wata shida.

 Shima cike da zolaya ya amsa masa da cewar “ na isa in yi disappointing surukina”.

 Ya kuwa yi kokari matuka. Saboda har dan madaidaicin jirgin mai daukan mutum dari da ashirin ya daukar musu shata daga Abuja zuwa Taraba, saboda abokansu da dama sun fantsama duniyar nema, sai aka yarda da yin mahada a Abuja.

 Sauran kwana biyu lokacin da su Baffa Petal suka yanke zasu daura auren Baffa da Hamida ya sauka a Nigeria da bakinsa ‘yan Japanese su goma.

 A safiyar jumma’r nan kuwa da aka ware domin daurin auren Hamida da Baffa, bakin ‘yan boko suka cika mayo lofe. Karfe goma sha biyu na rana bata karasa ba, sai ganin jeep jeep a kayi sama da guda ashirin suna ta shigowa garin da baki .yan daurin aure.

 Hamida bata nan, saboda takaici ya cika ta na rashin Ya Baffanta da ta yi. Tun daren jiya ta gudu kauyen su Nenne matar Baffa Petal, saboda bama ta son taga daurin auren nata.

 Ita ma Chibbu ta yi banza da ita. Saboda ta kasa gane bakin ciki me ta ke yi. Tun da ta zo garin ko abincin kirki ba ta ci sai azumin nafila da kuma sallolin nafila da take yawaita yi.

 Hakan ya san Chibbu kyaleta saboda ta kasa fuskantar matsala gareta ko farin ciki ne ya cika ta take yawaita godiya ga Allah.

 To ga baki ‘yan daurin aure har da masu jajayen kunnuwa da kananan ido sun iso. Nan kuwa su Ba wuro da ba Jauro suka shiga hidima da su.

 Tun bayan sallar asuba aka fara gasa ragunan da kuma suyar kajin ‘yan daurin aure. Ba su sa ran baki zasu zo ba. Shi kansa angon ba wanda ya sa rai da zuwansa.

 Nan kuwa a ka fito da dakkire da nono suka fara da shi. Ana idar da sallar jumma’a aka zarga wa Hamida igiyar auren Ya Baffanta ba tare da sanin ta ba da kuma sanin iyayenta.

 Su Baffa Petal dai sun sanar da su yau za su daura auren Humaira da mijin da ya basu iznin su zabar mata, amma fa ba su barshi ya san waye mijin ba. Shi ma kuma bai dage sai ya san waye ba.

 Angwaye sun dage a ranar zasu dauki amarya. Saboda haka aka tura kauyen su Nenne da ba shi da nisa da su aka daukota.

 Ba kuwa ta samu wani bayani ba. Aka fara shiryata domin daukar amarya. Nenne da Chibbu za su shiga mota daya da ita.

 Nan kuma Baffa ya dage akan Baffa Petal da Bajauro da Bawuro su je tare da su.

 Baffa Petal yana zolayarsa yace “kana tsoron haduwa da Abbanka ne”?

 “kamar ka sani. Sai yanzu nake fargabar yadda zamu kwashe da shi idan yaji abin da nayi”.

 Chibbu tana gefensu tace “oho mu dai ba ruwanmu. Wata happen wata idu wata kamburusu kayau”.

 Dariya Ibu ya tintsire yace “Chibbu har yanzu mun rasa baturen da zai fassara mana turancin nan naki”.

     ******************



CHAPTER THIRTY FOUR

   A can Kano kuwa Humaira da Mama Barrister watau matar Senator Alkasim kuma yayar abokin Baffa watau Ibu, san nan wacce ta kasance uwar dakin Humaira, su su ka tsaya tsayin daka na ganin komai ya tafi daidai.

 Sun gayyaci kawaye ba tare da sanin amarya ba. Sun raba ankon biki na tsadaddaje leshi dan dubu ashirin da atamfa ‘yar dubu bakwai ga kawayen amarya kyauta. Kuma ko wane kaya da abin daurawa a ka da kuma mayafin mahadin kayan.

 Haka zalika dinkunan amarya sun kammala ba tare da saninta ba. Ga gidan amarya ya dau harami. Hakan ya sa su Wabili daukar cewa Baffa ya yarda da hudubar da suka yi masa na yadda ya karbi auren kanwarsa Sofi.

 A bangaren Humaira da Mama Barrister hatta abincin da masaukin baki na abokan ango da zasu zo kawo amarya ya kammala.

 Sai da Mama ta tabbatar su Baffa sun baro Jalingo saboda anan suka tsaya suka hau jirgin da Baffa ya dada yin shatarsa domin daukar su Chibbu da kuma abokansa, san nan ta tura Humaira ta sanar da makotansu akwai taron biki a gidan Mallam Jibo washe gari.

 Saboda ma kar Wabili ta gane me ake yi sai ta bari sai bayan isha san nan ta shiga tsohuwar unguwarsu gayyatar ‘yan biki.

 Zahra bata samu damar taimaka mata da komai ba, saboda Amira ta hana ta motsi ko nan da can. Ba ta kaunar ta waiga ba ta ganta kusa da ita ba.

 Gaba daya ta yi sanyi. Sai ta kira Zahra kamar zata yi mata Magana amma sai ta yi shiru kawai ta na kallonta. Ta kan kuma takura Amal da Sadik yaranta su zauna kusa da ita.

 Wanda kowa ya san hakan ba sabon ta ba ne. amma yanzu duk kokarinta na ganin ta ja su jikinta ne. Da ga su har Zahran ba ta kaunar su matsa su barta.

 

 Hamida dai kanta ya kulle. Wa aka aura mata da har za a dau amarya a jirgi. Bata ga Baffa da Ibu ba balle ta fahimci ina aka dosa. Ko ma waye bai dameta ba. Tun da dai ba Ya Baffa ta aura ba bai dameta da ta san ko wane irin miji aka bata ba.

 Su na yin la’asar suka baro Mayo Lofe, amma ba su iso Jalingo ba sai tara na dare. Amma suna hawa titin sama iska ta kawo su Kano a awa daya tak.

 Har su Wabili sun kwanta barci baki ‘yan kawo amarya suka tada su. Tana ta kakabi da murna tana kuma kokarin hada musu dan abin sawa a bakin salati, sai ga Humaira da Mama Barrister sun sauka da kabakin abinci na ‘yan kawo amarya.

 Can karkashin zuciyarsu ita da Mallam Jibo sun yi murna da yadda Allah ya sanya Hamida matar Baffa ce, amma dukkansu suna kakabin yadda za su kwashe da Honourable.

 Saboda ko a jiya sai da ya zo ya sauke musu ashafar tsiya da kuma kora musu gargadi mai tsanani akan idan ma su suka hana Baffa zuwa inda ya ke su kuka da kansu. Ya kuma kara musu da bayanin ya ba su nan da karshen sati, idan har Baffa bai dawo ba zai daura auren sa da Sofi idan ya so idan ya dawo ya tarar da amarya.

 To sai kuma ga diyarsu ta cikinsu ta bayyana a matsayin matar Baffa. Allah ne shaidarsu. Sun yi iyakar kokarinsu su ga hakan bai faru ba, amma idan Allah ya kaddara abu dan Adam bai isa ba.

 Wabili dai ga murnar ganin ‘yan uwanta. Ga kuma tararrabin yadda za su kwashe da Honourable da Hajiyarsa. Shi ma Mallam Jibo hakan ne ya dakushe murnar ganin dangin nasu.

 Su Chibbu kuwa da suka zo da amarya ba abin da ya dame su. Balle da yake da ma ita macece da bata daukar rainin hankali. Ta dade da dawowa daga rakiyar Honourable da iyalinsa. Saboda haka hidimar biki ta ci gaba da yi ba tare da tayi la’akari da sanyin jikin da ke damun Mallam Jibo da Wabili ba.

 Ga Mama Barrister da ta dau ragamar kula da baki. Suna sauka ta wadata su da abinci. Sai bayan sun natsa, san nan Baffa Petal ya kalli Mallam Jibo wanda da gani jikinsa a sanyaye ya ke.

 Cikin harshen fulatanci yace da shi “Jibo na ga alama kamar ba ka yi murna da zabin miji da muka yiwa Hamida ba. Duk da dai umarnin ka mu ka bi na mu zaba mata mijin da ya dace da ita.

 Mu kuma sai muka ga ba wanda ya dace da ita sai naka dan, wanda kuma shi ya taka da kafarsa ya nuna ra’ayinsa na san auran Hamida.

 Saboda haka”. Ya dan karkace ya dauko daurin kudi ‘yan dari biyar dunkule daya watau dubu dari biyar ke nan, ya mika masa.

 “ungu wan nan sadakinta ne” ya fada ya na mai mika masa.

 Mallam Jibo bai karba ba, amma ya dada lankwasa muryarsa alamun ladabi ga kanin mahaifin nasa. San nan yace “a’a Baffa barshi a wajenka sai ka kira ta ka bata. Amma ni Baffa ba wai na ki auren su bane kawai yadda duniya zata kalle ni na ke kakabi.

 Mutane za su ga saboda abin duniya na dauki Hamida na ba wa Baffa. Shi kansa Yaya ba zai taba yarda da cewar na yi iyakar kokarina in ga na barshi ya aurawa Baffa ‘yar sa ba. Kuma….”

 Ba wuro ne shima cikin fulatanci ya katse shi da cewar “Jibo ai kace mutane za su zargi wani abu a kan auren Hamida da Baffa, ko. To ka barsu su yi ta zargin.

 Idan dai kai saboda Allah kayi to ka bar mutum da ra’ayinsa da kuma zarginsa”.

 “Gaskiyarka Hamma” Ba Jauro ya amsa masa. San nan ya mai da hankalinsa wajen Mallam Jibo yace “ka kyale mutum ka kama Allah. Duk abin da zaka yi ka duba Allah kar ka damu da abin da mutum zai ce”.

 Ajiyar zuciya Mallam Jibo ya saki san nan ya ce “gaskiyar ku Hamma Jauro amma akwai abu daya da na ke dubawa kuma shine dalilin da ya sa na takura na ke hakuri da halin Yaya.

 Ba wani abu bane illa na san Musa ya mutu da burin gyara zumuntarsu da yayansa. Da na ga yanda ya dawo shi da kansa ya ke son gyara zumuncin su da iyalan Musan shi ya sa ni ma na so auren ya kullu tsakaninsu”.

 Ba Wuro ne ya ce “sai yanzu ya ke son gyara zumuncin da shi ya yi sanadin lalacewarsa? Sai yanzu da ya ga Baffa ya zama mutum san nan ya ke so ya kalle shi a matsayin dansa?

 Sai yanzu ne ya san su din ‘ya’yan dan uwan sa ne? sai yanzu da ya ga sun isa moro ya lallabo ya ke son mayar da su ‘ya’yansa”?

     “Zancen ka haka ne” Ba Jauro ya amsa masa.

 Duk da rashin samun goyon bayansu Mallam Jibo ya roke su da su lallaba Baffa ya karbi auran Sofi sai ya hada su da Hamida, tun da musulunci ya ba shi damar hakan.

 Sun amsa masa za su shawarcin Baffa, amma fa sun nuna masa ba zasu matsa masa ba. Idan yana da ra’ayin yin hakan shi ke nan.

 Hamida ba ta gama tantancen waye mijinta ba sai washegari da safe da Baffa Petal ya kira ta ya danka mata sadakinta.

 A nan dai ta daure bata nuna murnar ta ba. Amma kusan da gudu ta fada dakin da aka sauki Nenne da Chibbu. Kansu ta fada cike da murna.

 Sai a lokacin Chibbu ta san ashe ba ta san Baffa ne mijin da iyayenta suka aura ma ta ba, bayan ta gama shaida musu yadda Baffa ya tsayar da su a hanya ranar da za su je Mayo Lofe ya dauke su suka karasa tare.

 Bayan nan ta dauko wayarta domin kiran mijin nata. Da farko da ta buga bai dauka ba, sai ta dauka ko yana wani uziri ne da ya hana shi daukan.

 Amma daga baya sai ta gane da kansa ma yake katse kiran. Ta kira ya kai sau ashirin yana katsewa, har ta hakura da kiran saboda ta gane fushi yake da ita na kin dagewa a aurensu.

 Murmushi ta yi cikin zuciyarta san nan ta ce “ba damuwa tun da aikin gama ya gama.

 Zuwan Zahra wacce ta sato jiki daga gidansu ta zo gidan Mallam Jibo da kuma Humaira shi ya dada rage mata damuwar da Ya Baffa ya dora mata.

 Nan kuma suka fara tsara maganar su kwalliya da kayan da zata saka na biki. Sai a lokacin Humaira ta gaya mata ai duk an gama da wan nan. Mai make up zata zo gida ga kuma dinkunnanta ta karbo mata.

 Kafin karfe goma na safe kawayenta duk sun hallara a gidan da ankon atamfa da Baffa ya bayar a raba musu, tare da leshin da za su saka na dinner.

 A can kuma inda angwaye suke, Ibu ne ya lura da wayar da Baffa yake yawan yankewa. Fakar idonsa ya yi ya dauke wayar domin ganin ko waye mai kiran.

 “What! African Queen ce ta yi mis calls har sama da ashirin amma AMA bai yanke sallah ya amsa ba”? Ibu ya fada cikin zolaya. Karbe wayarsa ya yi yace “ni fa bana son a dinga shiga harka ta da iyalina”.

 Gaba daya na dakin suka kwashe da dariya jin furucin Baffa na kiran kansa mai iyali. Duka duka auren na sa bai karasa awa ashirin da hudu da daurawa ba, amma ya fara amsa sunan mai iyali’.

 Shigowar kiran Abbansa ne ya katse dariyar da suke yi. Sai da ya dan rusuna kamar Abban ya na ganinsa. San nan ya ce “Abba barka da safiya”.

 “Anya uban masu gida zan amsa gaisuwarka kuwa, duba da irin laifukan da kayi min”.

 Shiru Baffa ya yi ya kasa bashi amsa. Jin hakan ya sa Mallam Jibon ba shi umarnin zuwa gida domin yana son su tattauna yadda za a yi batun Sofi.

 Saboda shi so yake a je a daura auren ta itama a yau din nan.

 Baffa yana ajiye wayar yace “miss call. Abba ba abin da zai sa in auri yarinyar nan.

 Bayan ya bawa Ibu labarin abin da ake ciki sai kawai suka yanke shawarar kin zuwa wajen Abban.

 Sai da kuwa suka yi azahar san nan suka shirya shi da abokansa da su ka dau ankon farar shadda wa gambari wadda suka yiwa dinkin babbar riga. Dukkansu sun saka hular saki sai Baffa ne kawai ya banbanta da ya saka zanna bukar.

 Sai walainiya suke. Suka nufi gidan domin halartar budar kai irin na Fulani da za ayi.

 A can gidan ma Mama Barrister ta sa masu decoration sun gyara farfadar gidan Mallam Jibo aka jere kujeru da kuma shimfida carpet a tsakiyar inda amarya da ‘yan rakiyarta za su zauna.

 Sai da mutane suka zauna san nan ta shigo an lullube ta da turmin atamfa ga kuma wani da aka shimfida wanda za ta taka zuwa mazauninta a kan karfet din.

 Humaira ce a gaba tana rera waka cikin fullatanci inda ta ke cewa

“gafaranku masu gida.

Ga bakuwar alkhairi mun kawo

Ku fito ku nuna mata kauna

Ku fito ku nuna mata murna

Ga bakuwar alkahiri mun kawo”.

 Sai da suka zaunar da ita a tsakiyar carpet din san nan aka fara hidimar budar kan.

 Wabili ce a matsayin ta na uwar ango ta fara da fansar amarya da makudan kudi, san nan sauran dangi suma suka bi sawunta.

 Hatta makotan da su ka yi zaman arziki da su sai da suka fanshi amarya da abin da Allah ya hore musu.

 Sai bayan an gama Tarawa amarya kudi inda ta kuwa tara su da yawa san nan Zahra ta bude fuskar amarya ta kuma rada mata sunan gidan aure. Ta rada mata Hibba.

 Wan nan ya zamo al’adar fulanin Yola da Taraba, in dai aka kawo sabuwar amarya za su rada mata suna.

 Da yawa kuma da wan nan suna surukai ke kiranta da shi wata ma har sunan ta na asali ya bata.

 Bayan an gama da budar kan amarya, sai suka matsa gefe ita da kawayenta a ka shiga dauken dauken hotuna

 Daga nan kuma aka gyara filin da amarya ta tashi, ango ya shigo shi da abokansa. Nan kuma mata aka shiga na sa budar kan. Kusan duk wadda ta bawa Hamida naira daya, to naira biyu take bawa Baffa.

 Ga shi dama da yawa daga cikin wadanda suka halarci bikin suna cike da yawan alkhairansa gare su. Saboda haka kowa da niyyar nan da malam bahaushe kan ce ‘gai da mai gaisheka ko ba zai amsa’ suka zo bikin.

 Wabili dai sai share hawaye ta ke da wayo. Na murnar ganin yadda Baffanta ya zama da kuma tunawa da mahaifansa da suka rasu.

 Saboda ita kam tun da su Chibbu suka saka ta a gaba da nasiha, ta saki. Dama dan goyon bayan da take bawa mijinta ba wai mai yawa ba ne. kawai dai biyayya ce irin ta matan kwarai, da duk abin da miji ya ke so shi suke takura kansu su karba ko da hakan bai musu dadi ba.

 Hamida dai ba ta samu kebewa da Baffa ba sai da aka zo yin hoto da ango da amarya. Daurewa tayi ta saci kallonsa, sai ta yi sa’a shi ma ita ya ke kallo.

 “Ka yi hakuri”. Shine abin da labbanta ya furta ba tare da ta daga sautin muryarta ba. Matsa hannunta da yayi da dan karfi shi ya tabbatar mata da ya ji abin da ta fada.

 Da daddare kuwa suka runguda zuwa dinner. Amarya cikin tsadajjen leshin ta da gwaggwaro da kuma mayafin da ya dace.

 Kawayenta da ankon su na indian lace da raw silk. Yayin da abokan ango har da bakin Japanese suka yi ankon yadin filtex.

 Tsarin bikin bai yi kama da auren gaggawa ba. Sai tsaruwarsa ta kasance kamar an dade ana tsara shi.

 A daren aka mika amarya sabon sashen ta na gidan Mallam Jibo inda Baffa ya gina musu.

 To su dai sun samu cikar burinsu. Amma a gidan Honourable, ba haka zancen ya ke ba. Zahra sai da ta sabule kwalliyarta, san nan ta sadada ta koma gidan. Saboda ta yi alkwarin ba a bakinta za a fara jin wan nan labari ba.

 Ta kuma yi sa’a ta dawo ba da dadewa ba Amira ta dawo daga asibiti, saboda ta dauka ma haihuwa ce sai da su ka je aka ce juyi ne.

 Duk yinin yau Sofi ba ta samu ta caja wayarta ba sai yanzu ta tsinto chager ta ta.

Ta soka caji. Tana kawo wuta kuwa ta dauka ta bude Instagram. Ai kuwa nan ta yi karo da mugun gani. Tar hotunan auren Baffa da Hamida suka dinga haska wayarta.

 Wani uban ihu ta saka wanda ya sanya Amira da Mommy isa inda ta ke da hanzari domin jin me ke faruwa.

 Gaba daya ta sandare a wajen ta kasa amsar tambayar da Mommy da kuma Amira ke mata. Zahra kuwa tana jin ihun ta san na meye sai kawai tayi zamanta a daki ta ci gaba da hidimar shirya Amal da Sadik cikin kayan bacci.

 Shima Honourable ihun ne ya jawo hankalinsa zuwa falon gidan. Zuwan sa ne ya sa Sofi fara ihu tana fadin “Daddy ka cuce ni. Mommy kin yi min karya”!

 “Wai me ke faruwa ne”? Daddyn ya tambaya. Hannunta na rawa ta nuna masa hoton auren DR AMA da Hamida.

 Wata irin ashariya ya mako, san nan ya ce “Na rantse da Allah ba mai rabani da Jibo a garin nan. Na rantse da Allah sai na daure shi har igiya tayi rara”.

 Mommy kuwa sai fadi take “ai kuwa kar ka kyale shi. Shi din banza yaushe ya isa ya ja da kai. Karyar tasa ai duk ta Baffa ce. Shi din kuma danka ne halak malak bai kuwa isa ya raba ka da shi ba”.

 “Ai bar ni da shi zan nuna masa ni kwallon shege ne. yanzu zan je gidan nasa in nuna masa bai isa ba. Yau zai san ba karya ake ba da a ke kirana Honourable Iliyasu Ahmad Dagumawa ba”.

     *****************

Comments

Popular Posts