☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* 31 & 32 ☘️☘️☘️☘️☘️

 ☘️☘️☘️☘️☘️

*SAI YANZU❔*

☘️☘️☘️☘️☘️


           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/


TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09



CHAPTER THIRTY ONE

 Hamida ce da Gwaggo tsaye a wajen. Gaba daya jikin Hamidan sai rawa yake yi na tashin hankalin da ya tunkaro ta.

 Ita duk badakalar da ake yi, ba wanda ya taba sanar da ita. Iyayenta ba su fada ma ta ba. Haka zalika shima uban gayya ko a fuska bai ta ba nuna mata akwai matsala a tattare da kasantuwar su tare ba.

 Duk maganganu da su ka yi shi da Sofi a kunnuwanta akayi su. Ta san yau yana azumi, saboda haka ta fita da niyyar tambayarsa mai zai yi buda baki da shi. Nan ta ji yadda ta kaya tsakaninsu da Sofi.

 Ta daga ido suka hadu da nasa idanun. Ba tare da ta ce komai ba ta juya ta shige dakinta. A dai dai lokaci da Sofi ta biyo shi cikin gidan domin ta sake rokonsa ta same shi yana kwallawa Hamida kira da nuna ta tsaya ta fahimce shi.

 “Ba abin da ke tsakanina da ita. Its not what you think. Please Hamida listen to me” su ne kalaman da suka riski kunnen Sofi. Sai yanzu ta gane watau itama wan nan bararojin so ta ke ta mallaki hadadden namiji irin DR AMA dinta.

 Da kuka ta juya ta nufi gidansu. Mommy da Daddyn ta ta nufa tana kuka tana sanar da su cewar saboda ‘yar Mallam Jibo dan uwanta ya ke wulakanta ta.

 Nan kuwa Mommy ta famfa shi da kyau. Ta nuna amsa cewar ita dama ta dade da sanin cewar Mallam Jibo na da mummunar manufa akan su.

 A fusace kuwa ya nufi gidansa, amma sai ya tuna masifun da ya yi a baya, ba su ba shi damar lankwasa Mallam Jibo ba. Sai ya canza shawara.

 Ya tuna a duniyarsu ta siyasa. Ka na nunawa talaka cewar shi din mutum ne mai muhimmanci. Yanzu zai yarda da duk karyar da zaka tsara masa.

 Yana takaicin halin da ya baro Sofi a ciki. Tun da yake da ita bai taba ganin ta shiga tashin hankali irin wan nan ba.

 Sun riga da sun sabar mata duk abin da ta nema ta na samu. Haka kuwa ta tada hankalinta da son mallakar DR AMA.

 Duk kokarinsa na ganin ya rarrashe ta ya ci tura. Kuka take kamar ance uwarta ta mutu. Ba kuma abin da ke fita daga bakinta sai ita dai a sa DR AMA ya aure ta. Idan bata aure shi ba kashe kanta zata yi.

 A bakin gate din gidan ya ajiye izzarsa da gadararsa. Walid ne ya sanar da Mallam Jibo zuwan Honourable.

 Bayan sun gaisa gaisuwa irin wacce ba su taba irinta ba. Saboda sabanin lokutan baya, wan nan karon a mutunce ya gai sa da shi.

 Duk da Abba ya yi matukar mamakin ganin da fuskar da ya tunkare shi, amma bai nuna masa hakan ba.

 Yana kokarin mikewa domin kiran Wabili ta kawo wa Honourable ruwa ta kuma zo su gaisa, Honourable ya tsayar da shi.

 Magana ya fara yi masa cikin kwantar da kai. Ya ce “kyaleta. Magana na ke son mu yi ni da kai”.

 “Ina jinka Yaya” ya amsa masa cikin girmamawa kamar yadda ya saba a can baya.

 Sai da ya nisa san nan ya ce “na san ni kaina abubuwan da na yi a baya ban kyauta ba. Amma duk da haka yanzu na gane kure na”.

 “Don Allah Yaya ka daina cewa haka koma menene ya wuce”.

 Ya share kwallar karya da ya matso da kyar. San nan ya ci gaba da cewa. Ina da burin in dawo da zumuncin da na yanke tsakanina da ‘ya’yan marigayi watau su Baffa ke nan”.

 Mallam Jibo cike da murna ya ce “ai kuwa Yaya idan haka ya kasance zan fi kowa farin ciki. Ai shi zumunci ba abin ayi wasa da shi ba ne”.

 “Yawwa haka na ke son ji. Yanzu hanya ta farko da na hango yiwuwar hakan shine hada Baffa da Safiya aure. Tun da dai duk duniya na san ba wanda ya isa ya sa Baffa ya yi abin da bai yi niyya ba, sai kai.

 Kai kadai ne zaka iya tankwara shi ya auri Safiya. Ka taimaka min ko don in samu in gyara dangantaka ta da yaran Musa”.

 Ganin yadda ya kaskantar da kansa ya na neman taimakonsa, sai ya sanya zuciyar Mallam Jibo ta dada karyewa.

 Ko banza shi kansa zai so Baffa da su Zahra su gyara dangantakarsu da wan mahaifinsu. Duk da ya san cewar raba Baffa da Hamida abu ne mai matukar wuya, amma ba zai so ya so kansa a kan dan uwan Baffa  na jini ba.

 Haka nan ya kudurtawa ransa cewar da yardar Allah zai yiwa Honourable abin da ya nema. Zai kuma yi iyakar kokarinsa ya tabbatar Baffa ya daidaita da Baffansa.

 Ya kudurta a zuciyarsa ganin cewa ya sadukar da farin cikin diyarsa domin cika buri marigayin amininsa, zai zamo wani babban abin alfahari.

 Ba zai manta yadda Mallam Musa ya ke nuna jin dadinsa da kuma yabon irin mu’amalar da ya kan ganshi ya na yi da nasa dangin ba.

 Ga shi dai nisa ne da su, ba na wasa ba, amma da kyar a rufa shekara biyu shi bai je ba ko su ba su zo ba

 Balle kuwa da wayar nan ta zaga gari ai kowa ya san abin da dayan ya ke ciki. Amma a wan nan karon, Mallam Jibo bai sanar da Baffa Petal harkarlar da ake ciki ba.

 Ya bari sai dagawar rana ya kira shi ya sanar masa rikicin da ya kunno wa soyayyar  Hamida da Baffa Wuta. To kuma a na wan nan sai ga Honourable ya zo ya russuna a gabansa yana rokonsa ya ba shi damar da zai gyara kurakurensa na baya.

 Shi kuwa a tunaninsa idan har ya yi haka ya san ya cikawa amininsa burin da ya mutu da shi a cikin ransa

 Honourable kuwa ganin ya yi nisa a tunani ya sanya shi saurin tsugunnuwa gabansa yana fadin “ka taimaka min kar inje gaban Ubangiji na da wan nan hakkin. Kai kadai ne zaka iya yi min wan nan taimakon”.

 Mallam Jibo ma kuwa da hanzari ya sauko ya durkusa kusa da shi yana fadin “don Allah ka mike. Har ni waye da zaka tsuguna kana neman wata alfarma a wajena. Kar ka ji komai. In sha Allahu komai zai yi dai dai”.

 A haka suka rabu da alkawarin duk abin da ake ciki zai kira shi yayi masa Magana.

 Da kyar ya samu Wabili ta fahimce shi. Ya na rarrashinta ya ke cewa “yanzu idan aka ji mun ki yarda Baffa ya auri ‘yar uwarsa kuma mun dauki tamu mun aura masa ai sai abin ya zamana kamar son abin duniya ne ya sanya muka yi haka.

 Kowa ya yi hakuri. Matar mutum kabarinsa”.

 “Ni ba wan nan ne damuwata ba. Yadda Hamidan za ta dauki zancen. Kaga tun dazu da ta ji su suna Magana da ita Safiyyan, tun dazu ta ke kuka. Shi kansa ba yadda bai yi ba ta saurare shi amma taki”.

 “Ita din banza da ba zata dauki kaddara ba. Kira min ita”.

 Nan kuwa suka saka ta a gaba da shi da uwar suna kokarin nuna mata amfanin sadukarwa da zata yiwa yayanta.

 Zuciyarta kamar zata fito ta bakinta saboda tashin hankali. Ta yaya zata iya rayuwa ba tare da Baffanta ba. Amma idan har hukunci da Baffa ya yanke ke nan akan su su biyu, zata sadaukar da farin cikinta in har yin hakan zai kawo wani sauyi na alkahairi a rayuwar Ya Baffa.

 A daren kuwa ta dauki karamar jaka ta zuba kayanta saiti hudu.

 Baffa bai hadu da Abbansa ba. sai washegari da asuba a masallaci. Ya san ya kan kai bakwai na safiya a cikin masallacin saboda lazumi da kuma karatu da suke yi. Shima sai ya zauna yana nasa lazumin.

 Bai koma gida ba sai da gari ya fara haske. Yau dai ya kudurawa ransa duk abin da Hamida zata yi sai ta saurareshi. Murmushi ya yi na ganin kishinta karara a bayyane. A cikin zuciyarsa ya ke cewa “in ban da African Queen da shiririta, me zan yi da wan nan pumpkin din gani da elegant lady”.

 Tuno ta kawai ya sanya murmushi subucewa daga fuskarsa. A haka ya doshi cikin gidan domin gaisawa da iyayensa ya kuma shiga rarrashin rabin ransa.

 Yana dosar falon yaji Abba na fadin “shike nan na yi maganin wan nan. Shi Baffa Petal na kira shi na yi masa bayani. Idan an aurar da Hamida ga wani shi uban masu gida zai hakura ya auri ‘yar uwarsa”.

 Kamar zai shiga ciki sai kuma ya saurara saboda ya dada fahimtar me Abban yake nufi da aurar da Hamida. Waccen Hamidan ma Abba ya ke nufi?

 Maganar Wabili ce ta amsa masa tambayarsa, inda ta ke fadin  “Amma ka na ganin shi Baffa ba zai shiga tashin hankali ba idan ya ji ka raba shi da Hamida. Yanzu sun wuce can Mayo Lofe ke nan?”

 “Ai sai da naga motar su ta tashi ma na taho. Shi dai Walid na sanar da shi kar ya wuce kwan uku a can ya dawo saboda makaranta”.

 “Anya kwana uku. Yanzu fa aYola zasu sauka, san nan su hau motar Gembu. Da ga can su samu ta Mayo lofe. Ai kuwa za su sha hanya. Ya dai yi sati kawai. Saboda kafin ma su isa sai sun kwana a hanya. Kuma …..”

 Bai tsaya jin sauran maganarsu ba, ya juya da hanzari. Dakinsa ya koma. Bai bata lokacinsa wani dogon tunanai ba, saboda ya riga ya gama hasaso me Baffansa ya ke nufi. Hamida ta auri wani shi kuma a aura masa wan nan yarinyar da ba ta gama sanin kanta ba balle ta san na wani.

 Dama tun jiya ya lura Abban ya fara yi masa wani shagube yana dada karanta masa yadda da kaddara da hakuri da abin da zuciya ke so.

Sai yanzu ya fahimci inda karatun na sa ya dosa.

 Saboda ya saba kusan ko wane lokaci a cikin nasiha ta lamuran rayuwa ya ke yi musu, sai ya dauka irin hakan ne. Ashe Abba ya shirya rugurguza masa rayuwa ne.

 Bai tsaya wani dogon tunani ba, ya dauki makullin range rover din sa. Har ya fita ya dawo da hanzari ya bude wardrobe. Kaya ya cusa a jakarsa da shi kansa bai san me yake cusawa a ciki ba.

 Ya dauki wallet dinsa ya ga yana da isassun kudi. A bakin gate ya sanarwa maigadi da ya fadawa Abbansa tafiyar gaggawa ta same shi. Zai kira shi a waya.

 Ya na hawa titi ya kira wayar Walid. Ringing uku ya dauka. “Ya Baffa barka da asu……”

 “Don’t barka da asuba me. Where the hell are you?”

 In ina ya fara yi mai nuna alamun rashin gaskiya. Ga kuma kukan Hamida da ya dada dagula masa lissafi.

 Baffa ne ya sake daka masa tsawa ya ce “I am asking you kuna ina. Ka tsaya kana min maganar banza”.

 Shi kansa ya ji alamar tabbas Baffa a cike yake da bacin rai.

 “muna cikin Kano Line zamu je “……

 Bai barshi ya karasa ba,ya sake daka masa tswa “ban tamabayeka inda zaku ba. Ina tambayarka inda kuke”.

 “muna dai dai Police Academy ta Wudil”.

 “Ku sauka a nan. I am on my way”, shi ne kawai abin da ya ce ya kashe wayar.

        ************



CHAPTER THITY TWO

  Gudun minti ashirin ya kai shi inda suke. Hamida ya hango zaune kan akwatinsu ta kudundune kanta cikin hijabi.

 Wani haushi ne ya dada kama shi. Allah ya sa Abba ne ya dora su a motar hayar nan. Amma tabbas da wani ne sai ya dauki mataki a kan sa.

 Wai Hamidansa ce a zaune a tsakiyar titi kamar wata ‘yar gudun hijira. Wani uban birki ya ci a gabansu, hakan ya san ya ta dagowa domin ta ga me ke faruwa.

 Saboda ita ba ta san yadda su ka yi da Walid ba. Tun jiya da Abbansu ya bata umarnin ta tafi wajen daginsa a can yayi niyyar aurar da ita.

 Tun daga lokacin kwakwalwarta kusan ta daina aiki. Sai ta koma kamar zombie. Idan ance ta zauna ta zauna. In ance ta tashi ta tashi.

 Saboda haka ko sanda Walid ya bawa driver kano line din da suke ciki umarnin ya tsaya zasu sauka a nan saboda umarnin da aka basu a gida na su koma, bin sa kawai ta yi suka sauka ba tare da tambaya ba.

 Da ya ce ta sauko sun fasa tafiya haka nan ta biyo shi. Allah ya sa ma ba wasu kaya garesu masu yawa ba. Kuma a saman boot din motar suke.

 Hawaye ne dai yaki tsayawa daga fuskarta.

Tsayawar mota a gabanta ya sanya ta dago. Kur idonsa a kan nata. Duk da ya fahimci tashin hankalin da ta ke ciki, amma hakan bai sa ya dai na jin haushinta ba.

 Gani yake itama ta bayar da gaggarumar gudummowa wajen kokarin da Abba ya ke na son rabasu.

 Ya sakko kamar zai yi mata Magana, amma sai yaji komai ya tsaya a makogwaransa ya kasa furta kalma ko daya.

 Walid ya zagayo wajensa da rawar jiki yana kokarin gaishe shi, amma wani irin kallon tuhuma ya jefe shi da shi.

 Dan rusunuwa yayi yana kokarin gaishe shi.  

“Ya Baffa Assalamu alaikum”. Wan nan itace gaisuwar da suka saba a tskaninsu.

 “Baka nemi aminci da ni ba, saboda, da kai ake son hada baki a kassara ni”.

 Yana kokarin bashi hakuri da kuma bayani ya daga hannu alamun baya son jin komai.

Umarnin shiga mota ya basu duk su biyun.

 Har ya yi u-turn da niyyar komawa Kano, ko me ya tuna sai ya sake juya kan motar ta kalli gabas.

 Shi da Walid suna gaba, yayin da Hamida ke kwance a baya. Sai sauke ajiyar zuciya yake daya bayan daya. Idan ya ji shesshekar kukanta sai ya ji zuciyarsa ta dada zafi.

 Shi kuwa Walid bawan Allah bai san hawa ba, bai san sauka ba. Abba ya saka shi ya raka Hamida Mayo Lofe. Baffa kuma ya zo ya kwashe su a hanya.

 Ga dai motar na kallon gabas. Abin da bai tantance ba, Mayo Lofe za su ko kuwa wani wajen za su. Ga dai mota ga kuma mai mota, amma yanayin fuskar mai motar ya hana fasinjan ciki tambayar in da su ka dosa.

 Wayar Ibu ce ta saukake tension din cikin motar. “My in law how you dey”? Ibu ya tambaya daga nasa bangaren.

 “Zan zama lafiya idan na isa inda na ke son zuwa na kuma yi abin da nake son yi”, Baffa ya amsa masa.

 “kaifa ka cika Magana in riddles. Ina zaka kuma me zaka yi”?

Sai da ya saci kallon Walid da kuma Hamida da har yanzu ta ke nannade a kwance a kujerar baya, san nan ya ce “Watashi wa kekkon shimasu”, Baffa ya amsa cikin harshen Japan. Watau ya na nufin zanje neman aure.

 Dariya Ibu ya kwashe da ita. San nan yace “A ina zaka neman? Ta biyu zaka kara ke nan? Tun da duk mun san kana da ta farko”.

 Yake yayi ya dan saci kallon Walid da ya zuba masa ido yana kokarin fahimtar zancen yayan na sa. “kar ka damu I will call, you idan na isa”. Bai jira amsar Ibu ba, ya katse wayar.

 Sai a lokacin hankalinsa ya kai kan madubin mota wanda ya hasko masa Hamida ta nannade cikin Hijabinta. Sai a san nan ya saki wata katuwar ajiyar zuciya me nuna nauyin da ya rike a kirjinsa ya ragu.

 Hannun ya sa ya dan rage karfin AC dake baya wanda saboda mazauna bayan motar aka yi ta. San nan ya danna dan wani button a kan stearing da ya ke murzawa.

 Take kuwa kujerar bayan ta dan dinga kwanciya har sai da ta koma dan karamin gado a cikin motar. Gyaran kwanciyar da Hamida tayi shi ya tabbatar masa da zargin da ya yi, na bacci ya dauketa.

 Girgiza kansa kawai yayi. San nan a cikin ransa yace “watau ita har ta samu sukunin bacci duk da tashin hankalin da ta taimaka na shiga”.

 Abin da bai sani ba. Tun lokacin da ta ji maganarsu da Sofi, bacci bai kara ganin idonta ba, sai yau da ya sace ta.

 Sai da suka zo shiga garin Gombe wanda sun dauki awa biyar cur Baffa yana zura gudu. A gidan mai ya tsaya domin yiwa motarsa full tank saboda ya ga man yayi kasa.

 Shigarsu gidan mai itama ta dan farka. Ya na shan mai, Walid ya kira mai dabino, saboda tsoron fuskar Ya Baffa ta hana shi nuna tsananin yunwar da ke addabarsa. Yana kokarin biyan mai dabinon dukkansu su ka ji muryar Hamida a shake mai nuna alamun ta sha kuka ta koshi.

 “Walid karbo min ruwa”, ta ce da kanin na ta.

 Sai a lokacin hankalinsa ya bashi cewar ba bu wanda ya karya gashi har sha biyun rana ta gota.

 Bai yi musu magana ba, ya biya kudin motarsa. Dan zuwan da ya yi gaishe da iyayen abokinsa Ibu ya sanya ya dan san garin kadan.

 A gate din wani babban hotel ya yi parking. Sai da ya yi musu booking daki san nan ya dawo inda yayi parking ya sa suka fito daga motar.

 Ita dai biye take daga ita har Walid din. Ba su ga fuskar tambaya ba, saboda haka suka shiga dakin.

 “Walid shiga kayi alwala yanzu azahar za ta yi, sai muyi kasaru”.

 Bayan Walid ya shiga bandaki ya dan saci kallon Hamida wacce ta sunkuyr da kanta ta kasa hada ido da shi.

 “Ai dole ki ji kunyar kallona, saboda you intend to betray me”.

 Jin kalmomin da ya jefe ta da su ya sanya ta sake fashewa da kuka.

 Kwafa kawai ya yi. Yana kokarin sake Magana Walid ya fito daga bandakin. Ficewarsa ya bata damar shiga itama ta dauro alwala.

 Sun dauki kimanin awa daya a hotel din, saboda sai da suka ci abinci suka yi sallah san nan suka shiga mota suka ci gaba da tafiyarsu.

 Karfe hudu suna Numan. Sai da suka isa Ngurore san nan suka dauki hanyar Mayo Belwa. Suka wuce garin Zing, Jalingo da Bali, san nan suka isa junction din Mambila.

 Kauyen Mayo Lofe yana tsakanin Ba’isa da Gembu. Duk da hawan tsaunuka da kuma yawan kwanoni, amma awa hudu ce ta kaisu kauyensu daga Numan.

 Karfe tara saura suka isa kofar gidan Baffa Petal wanda ya kasance shine kanin mahaifin Mallam Jibo kuma mahaifin matarsa Wabili. Shine babba a zuri’arsu gaba daya saboda na gaba da shi sun rasu. Ya na zaune gida daya da kanwarsa watau Chibbu, wanda tun bayan rasuwar mijinta ta baro cameroo ta dawo gida da zama.

 Baffa Petal baya tsammanin isowarsu sai washegari, amma sai gasu sun shigo masa cikin farkon dare, da kuma bakon da ba su san da zuwansa ba.

 Nan kuwa matar baffan watau Nenne ta shiga kokarin hidima da su. Hatta surukanta mata guda biyu sai da suka taso aka shiga hidimar baki da su.

 Bayan sun dan natsa sun yi sallah sun dan taba abinci, Baffa Petal yayi kokarin jan Baffa domin kai shi masaukin da suke sauka shida Mallam Jibo idan sun zo.

 Amma fir ya ki yarda saboda ya kafa ya tsare akan sai Baffa Petal ya saurare shi.

 Dariya ya yi msa san nan ya ce “dama ba ka bata lokacin ka ba, saboda wan nan ‘yar bakar a nan zata zauna”.

 Duk da haka Baffa yaki kyale Baffa Petal sai da ya sa ya tattao sauran ‘ya’yansa guda biyu da ke zama tare da shi a cikin daren.

 Bai yi nauyin baki ba ya zayyane musu abin da Abbansa watau Mallam Jibo ya ke da niyyar yi. Ya kuma nuna musu shi kam bana ya shirya ya sabawa umarnin Abban nasa.

 An tafka muhawara inda yayyen Mallam Jibo suka dage a aurawa Baffa, Hamida yayin da shi kuma Baffa Petal yake tunani irin na Mallam Jibo.

 Duk sun san yadda Mallam Jibo ya sha fama da Honourable, saboda haka ba su ga dalilin kuntatawa yara domin shi ya samu biyan bukatarsa ba.

 Baffa Bawuro yace “idan kun lura yanzu ma ba zumuncin ya ke son kullawa ba. ‘Yarsa ya ke son biyawa ta ta bukatar kamar yadda ya saba a ko da yaushe.

 Ai kowa ya san shi ba ya iya dauke kansa a kan abin da ‘ya’yansa suke so. Tun da idan abin na sa na Allah ne ai sai ya dubi san ran Baffa amma ba na ‘yarsa ita kadai ba”.

 Ba su tashi daga zaman muhawarar ba sai da Baffa ya samu alkawarin za su aura masa Hamida kamar yadda mahaifinta ya wakilta su da su aura mata wanda suka ga ya dace.

 Bayan fitar su Ba Jauro, kakan ya kalle shi yace “wai duk akan wan nan bakar kake tashin hankali. Ga fara an baka”.

 Shima cikin harshen fulatancin ya mayar ma sa da cewar “kai kuma da kake zakewa a auran da ba na ‘ya’yanka ba fa”?

 Dukan wasa Baffa Petal ya kai masa. Daga nan kuwa dakin kakarsu Chibbu ya shiga. Hamida na zaune cike da tashin hankali na rashin sanin abin da zai faru da ita da kuma bacin ran da Ya Baffanta ke ciki.

 Ko kalma daya bai furta ma ta ba tun da suka baro Kano har isowarsu Mayo Lofe. Ita a ganinta itace abar tausayi. Ko matsayar karatun ta ba wanda ya yi tunani, tun da Abba turo ta ya yi a aurar da ita a kauye.

 Amma ta lura shi ita ya dora wa laifin bakar kaddarar da ta tunkaro ta. Kuma hakane a zuciyar Baffa. A tunaninsa ya kamata ta yi fada da kowa saboda su kasance da junansu.

 Amma ya lura itama tayi niyyar sadaukar da shi kamar yadda Abba ya yi niyya. Ya kuma kudurta sai ya hora ta, saboda ta fahimci kaunarta ba karama ba ce a zuciyarsa.

 Ganin yaki kulata, ya maida hankalinsa kan rama zolayar da Chibbu ke masa, ya saka ta, ta mike ta yi tafiyarta dakin Nenne.

 Kalmar “coward” da ya raka ta da ita ce ta daki kunnuwanta. Sai da ta fice daga dakin san nan ya dauke idanuwansa daga kanta. Yana jiyowa su na hada ido da Chibbu wadda ta tsira masa ido.

 Suna hada ido tace “mh matsoraci kawai”.

Mika yayi akan babban gadon ta na karfe mai dungu, san nan ya ce “ni kuwa ni ne jarumi da na shiga filin daga ba tare da taimakon ki ko na yayanki ba”.

 “Dan nema. Haka ka ce, sai in sa a fasa baka ‘balejo”.  Haka ta ke kiran Hamida dashi watau ‘yar baka ke nan da fulatanci.

Shi ma kuwa cikin zolaya ya ce da ita “Iyayen nawa su yanke hukunci ki yi mana katsalandan”.

 Ta na zolayarsa ta yi kokari kora shi masaukinsa, amma ya ki. Nan dai yayi kwanciyarsa  suna wasansu na jika da kaka, har bacci ya yi awon gaba da shi.

Comments

Popular Posts