☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* 29 & 30 ☘️☘️☘️☘️☘️

 ☘️☘️☘️☘️☘️

*SAI YANZU❔*

☘️☘️☘️☘️☘️


           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/


TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09



CHAPTER TWENTY NINE

 Cike da bacin rai Abba ya nufi gida. Bai rufewa Wabili komai ba, ya zayyane mata abin da ya faru a gidan Honourable.

 Ita kanta wabili ta shiga rudani saboda ko ba komai ta fuskanci shakuwar da ke tsakanin Baffa da Hamida. Sai da ta nisa, san nan ta ce “amma a yanzu kam zai yi wahala Baffa ya amshi tayin da Yaya ya yi masa. Da ya dan jira ya jashi a jikinsa sun kara daidaitawa tukunna”.

 “Ni kaina ban san uban masu gida na rike da abubuwa da suka faru a cikin ran sa ba sai da ya amayar da abin da ke zuciyarsa.

 Da yawa ma, ban san ya san su ba. Saboda ni dai Allah ne shahidi na, ban taba zaunar da yaron nan na nuna masa wani rashin kyautawa da Yaya ya yi masa ba, amma na san kowa zargin da Yaya ya yi min shi zai bini da shi na tunanin ni nake cusa masa ra’ayin kar ya kyautatawa danginshi”.

 Wabili tace “Mallam ka daina damuwa. Allah ne shaidarka. Ina ce hatta ‘yan uwansa na kauye ka na kaishi wajensu. Kuma dawowar nan ma ina ce sai da ya je suka ganshi. Kuma duk hidimar arzikin da ya kamata ka na nuna masa ya yi musu.

 Na tabbata yadda ya san danginsu na can gida, shi kan sa ‘ya’yan Yayan ba su san su ba”.

 Hakane Wabili, amma kowa laifi na zai gani idan har Baffa yaki auren ‘yar uwarsa. Idan ya zo ki lallaba shi ya daure ayi auren, saboda yarinyar ta ban tausayi ba zaki gane irin kukan da ta rinka yi ba a kan son sa”.

 Tsaki ta ja san nan tace “ba ka jin irin tabarar. Yarinya budurwa ta zauna ana zancen aurenta da ita”.

 “A’a ai kin san kowa da irin ta shinsa. Su ai kina ga ‘yan gayu ne”.

“’Yan gayu ko ‘yan shirme. Ai na dauka yadda babban dansu ya koma ya ishe su ishara. Yanda ya ke mayar da ‘ya’yan mutane ‘yan jagaliya ga nasa nan ai ya zama daya daga cikinsu”.

 “MH Mh bar wan nan Magana Wabili, Allah ya raba mu da muguwar kaddara. Allah kuma ya shirya mana yaranmu”.

 Shi kuwa Baffa yana shigowa gidan bayan ya yi magariba ya tsaya ya yi isha, sai ya dauki motarsa Land Cruiser da kamfaninsu ya ba shi ya je dauko Sahibarsa daga bikin kawarta da ta gaya masa zata je.

 Yana tsaye a bakin mota tun da ta fito ya kura mata ido. Shi a a rayuwarsa bai taba ganin macen mai kyawun Hamida ba.

 Komai nata burgeshi ya ke. Ka ma daga doguwar fuskarta mai dauke da kyakkyawan siririn dogon hanci. Sai dan madaidaicin bakinta mai jere da fararen hakora, yar yar da su.

 Duk da kusan ko yaushe a cikin hijabi yake ganinta ko kuma babban mayafi, amma hakan bai hana kyawunta bayyana ba.

 Jikinta kamar na tarwada haka fatar ta take. Balle yanzu da yanayin rayuwa ya canza sai ya zamana fatar ta ta dada haske da murjewa. Kyawunta na kama da mutanen Ethopia.

 Sai da murmushi ya kubuce masa da ya tuno da dunkulalliyar yarinyar da ake son lika masa. In sun dauka farin ta ne zai rude shi to ba su dauka dai dai ba.

 Tana karasowa murmushi ya subuce a fuskarsu duk su biyu. Kallonsa ta yi ta ce “wan nan kallon na meye, kamar ba ka sanni ba. Nice dai Midan ka”.

 Murmushi ya yi san nan y ace “Midan Yaya ai kin kore ta. Wan nan is my lovely African Queen”.

 Motar ya bude mata ta shiga, san nan ya zaga bangaren driver ya shiga. Sauran kawayenta da suka zauna a tsohuwar unguwarsu ta hango. Suka jira suka iso. Sai da su ka ajiye su a gidajensu san nan suka karasa gida.

 A jere da junannsu suka shigo. Ba ka gane dacewarsu sai mutum ya gansu tare. Baffa da kyau da kwarjini. Hamida da kyau da aji. Su kansu mahifan na su da suka gansu a haka sun birge su.

   Gwaggonsu ta raya a ranta kauna ce a tsakaninsu ta kusan shekaru ashirin, amma ana kokarin rabasu. Addu’a ta yi musu a cikin zuciyarta na Allah ya zaba musu abin da ya fi alkhairi.

  Cike da annashuwar kasancewa da Baffa Hamida ta shigo gidan. Amma a yadda ta ga fuskar mahaifanta sai taji ba dadi. Saboda duk wanda ya kallesu ya san hankalinsu ba a kwance ya ke ba.

 Shi kuwa Baffa yau wasai ya ke jin zuciyarsa. Saboda ko ba komai ya samu sanadin mai dawa Honourable martanin wulakancin da ya yi wa iyayensa da shi kansa da kuma kannensa.

 Bai damu da yanayin da su Abban suke ciki ba. Sai ma tambayar Walid ya ke yadda wasan LALIGA na yau ya karke.

 “Yanzu Baffa ba zaka tsaya mu fuskanci abin da ya taso a gaban mu ka ma shashantar da maganar”? Mallam Jibo ya ce da shi.

 “Abban ba wani abu da ya tunkaro mu. Aure na mutum biyu ne. Daya kuma ba ya yi”.

 Har Abba zai ci gaba da Magana sai Wabili ta katse shi da cewar “Hamida je ki store ki dau taliya katan daya kuje ke da Walid ku kaiwa Uwa mai markade”.

 Jikinta a sanyaye ta mike ta shiga domin aiwatar da aiken Gwaggonsu. Baffa ya fuskanci wayon Gwaggon, amma sai ya yi shiru bai ce komai ba.

 Ba wanda ya sake Magana sai da Walid da Hamida suka fita, san nan Abba ya mai da hankalinsa wajen Baffa yace “uban masu gida ka kula da wani abu guda. Shi zumunci ba a yi masa rikon sakainar kashi. Kuma ina ga wan nan hadin zai taimaka wajen kara dinke ‘barakar da aka samu a baya”.

 Wabili ma ta café da cewar “kuma ita yarinyar ba ta da makusa. Da kyawunta da kuma ilmin ta”.

 Murmushi ya yi san nan ya tausa harshensa yadda ya saba mata shagwaba idan yana son wani abu. San nan ya ce “yanzu gwaggo sai ki yarda a bawa Baffan ki wan nan dunkulalliyar yariyar. Gaba dayanta fa, a cure take guri daya”.

 “Gidanku” ta fada tana mai yi masa dakuwa na ganin ya mayar da abin wasa.

 “Ai bar shi Wabili, ba kya ganin bai daukin abin da muhimmanci ba. Sai nake ganin ma kamar farin ciki ya ke ji ya yi fada da babansa”.

 “A’a sam Abba bana farin ciki da fada da shi. Sai dai nayi farin ciki da bashi amsar ayyukansa na shekarun baya. Kuma ma fa da Gwaggo ta ce tana da ilmi. Ba ta da wani ilmi karatu ne kawai. Shi ma ban tabbatar da ingancinsa ba. Tun da dai sauran yayyenta ba bu ma mai karatun kirki”.

 Abba ne ya sake kwantar da murya alamar son ya rarrashe shi. Yace “Baffa ka duba kalaman Yaya akai na. kuma yanzu yaji ka ki karbar ‘yarsa. Ba zan fita daga zargi ba”.

 “Ni da zaka yarda ma da sai ka hada ka auri biyu da wacce kake so da kuma ita Safiyyan” inji Wabili.

 “In hada wa da wa”?  ya fada yana mai zaro ido alarmar razana da kalaman Gwaggonsa.

 Sallamar Zahra ce ta yanke musu zancen. Bayan an gama gaggaisawa Wabili ta fara gaya mata shawarar da suka ba wa Baffa. Ita ma ba su san abin da ya korota daga gidan Honourable ba ke nan. Saboda zagi dai yau Mallam Jibo ya sha shi.

Yayin da Mommy ke zuga mijinta da nuna masa duk laifin Jibbo ne saboda shi ya mallake Baffa har ya ke iya musawa umarnin wan mahifinsa. 

 Ga uban gursheken kukan da Sofi take yi ta na fadin in har ba ta auri Baffa ba, kashe kanta zatayi. Mommy kuwa sai dada lallaba ta, ta ke yi tana fadin “share hawayenki. Aure ke da Baffa an yi an gama”.

 Ita kuwa ganin abin nasu ba arziki ta sudade  ta bar musu gidan. Dama kuma tayi sa’a Amal da Sadik suna gidan kakarsu. Amira kuma ta tafi asibiti check up.

 Hakan ya sa ba wanda ya ga sanda ta sulale ta fice ta nufi gidan su. Bayan Wabili ta gama yi mata bayani Zahran ta kalli Baffa tace “amma ya Baffa ka gaya musu wacce kake son aura ne ko kuma baka samu ba”.

 Murmushi ya zauna yayi san nan yace “kowa ai ya san matata. tun ranar da ta zo duniya aka ba ni ita. Kuma tun a lokacin na fara son ta. Ki na gani zan iya rabuwa da ita saboda waccan sakaryar”.

 Abba ya nisa ya ce “shi ne babbar matsalar. Idan nace maka ban san abin da ke tsakanin ka da kanwarka Hamida ba, na yi karya. Amma ka duba abu guda. A cikin wan nan ruguntsumi da kake da wan mahaifinka ni da bani da alaka da kai in kyale ka, ka rabu da shi in dauki ‘yata ta cikin in baka. Ka na ganin ban dagula lamura ba, maimakon in gyara su”?

 “Abba ni kake cewa baka da alaka da ni”? Baffa ya fada muryarsa na rawa mai nuna kuka na son kubuce masa.

 Nan kuma sai hankalin Abban ya tashi. A rikice har muryarsa na sarkewa na ganin mummunan yanayin da Baffa ya shiga saboda ya nuna ba su da dangantaka ta jinni.

  A rikicen ya fara fadin “ba nufi na ke nan ba. Amma ka lura da kyau ko ya nake da kai Yaya yafi ni kusanci da kai”.

 Kifa kansa kawai yana share hawaye wai shi Abba ya ce shi ba jininsa bane. Su kuwa nan suka daddage lallashinsa da kokarin nuna masa zumunci suke so su gyara.

 Amma duk da haka yaki ko gezau sai dada nuna bacin ran sa na nuna masa matsayinsa da Abba yayi.

 Daga karshe ma ya fita ya tafi dakinsa. Amma abin mamaki da Zahra ta bishi dakin sai ta tarar da shi yana waya da Hamida yana fadan ina ta tsaya bata dawo ba.

 Zahra mamaki ya kamata na ganin yanzu ya bar falon ransa a bace har da kuka, a she na karya ne. Tun da da ta shigo ko alamar bacin rai ba bu a ta re da shi.

 “Wai dama Ya baffa, dama ba kukan gaske kake yi ba? Ni fa rarrashi Gwaggo ta turo ni in yi”.

 Idonsa daya ya kanne ma ta. San nan ya ce “its called emotional blackmail. Don na hango Abba yayi niyyar sacfricing din mu saboda kawai ya biyawa wadancan mutanen bukatarsu.

 Ni kuwa ban yi niyyar sacfrising Hamida for a thousand women ba”.

 “Ya Baffa ‘yar bakar kakewa wan nan…..” maganar ta ce ta katse da ya kai mata dukan wasa, san nan suka kwashe da dariya a tare da shi da ita.




CHAPTER THIRTY

 A kwana biyun nan kuwa ba abin da Mallam Jibo ya bawa muhimmanci kamar kokarin rarrashin Baffa ya yarda ya amshi ‘yar Honourable watau Sofi a matsayin matar aure.

 Shi kuwa abin nasa kamar turi. Idan ma ya dauko zancen duk kokarin da zai yi wajen kifar da shi sai ya yi.

 Kusan duk abokansu na kuriciya da ya san Baffa na jin maganrsu sai da ya kai karar Baffa wajensu. Amma Baffa ya ki amincewa.

 Ganin wan nan ba mafita bace, ya tafi kauyensu in da sauran dangin ubansa suke wajen wani wan kakansu domin ko Allah ya sa Baffa ya yarda da kudirinsu.

 Shi kam ma da ya kira shi ya yi masa maganar sai ya mai da abin wasa. Yana fara zancen sai Baffa ya ce “kai dai tun da na bar maka tsohuwar matarka, ina ruwanka da wadda zan aura”?

 Mai unguwa da Liman duk sun shiga cikin zancen amma duk tulin kasar da suka Tarawa Baffa ba ta sa shi ya rusuna ba. Suma kuwa dama ba wani kwanta musu abin yayi ba. Saboda haka sai suka nuna wa Mallam Jibo da ya kyale shi da ra’ayinsa

 A can gida kuma Sofi ta haukacewa iyayenta. Ga ta dama yarinya ce da ta saba samun duk abin da ta ke so a rayuwa. Sai ta ke ganin dole ne shima Baffa ta same shi.

 Uban yayi aiken baffa ya zo, amma sam ya ki zuwa inda ya ke. Da ya ga ma Abbansa na takura shi akan maganar sai suka fara wasan buya. Burinsa ya kammala abin da yake yi ya gudu daga kasar.

 Burinsa a aura masa Hamida yanzu, amma ya san sarai Abbansa ba yarda zai yi ba a wan nan harkarlar da ke faruwa a gidansu.

 Ga kuma Ibu da ya takura amsa da son shi a daura na sa auren da Humaira. Da ya nuna masa scandal da ta sako shi a gaba. Ibu yace masa “bikin magaji ba ya hana na magajiya. Ni ka sallameni. Idan na samu cikar burina, ba sai in taya ka naka yakin ba.

 Amma ni yanzu hankalina ba a kwance ya ke ba ta yaya kake tsammanin zan baka moral support”.

 Hamida bata da masaniya abin da ke faruwa. Abu daya ta lura da shi duk lokacin da suke hira ya na yawan maimaita kalaman “duk rintsi kar ki yarda a raba mu. Duk kuma rudanin da zai faru ki yi kokarin bani goyon baya”.

 Bata fahimci kalamansa ba, amma ta daukar masa alkawarin da iznin Allah tana tare da shi.

 A wan nan rana Sofi ta gaji da alkawarin Bogi da take ganin iyayen ta na mata na alkawarin aura mata DR AMA. Saboda haka ba tare da ta shawarci kowa ba ta sha kwalliya ta nufi gidan Mallam Jibo. Duk da dogon takalmi da ta saka, amma gajarta da Baffa yake yi mata tsiya da ita sai da ta nuna.

 Kar ku dauka mummuna ce. Sam ita ma tana da kyau. Ga ta fara kal da ita. Kuma tana da kyakkywar fuska. Ga jikinta dumurmur da shi, saboda tana da dan garin jiki. Amma ita ma mace ce mai daukan ido.

 Tun da ta ke ba ta taba haduwa da namijin da ta ji ya kwanta mata arai irin yayanta ba. Ta kuma yi niyyar samunsa kamar yadda ta saba samun duk abin da tai muradi a rayuwarta.

 Ita ta tukar motar zuwa gidan Abba. Ta tamabayi maigadi ko Baffa yana nan. Shi ya fada mata cewar dazu ya dawo daga Abuja, amma ya dan fita yana kyautata zaton ba nisa ya yi ba, saboda bai fita da mota, ba.

 Bata shiga gidan ba sai ta tsaya jiransa. Ba ta yi zaman sama da minti biyar ba sai ga Baffa ya dawo. Tun daga nesa ta ke kare masa kallo. Kowa ya ganshi ya ga kyakkyawan bafullatani. Sumarsa da ya yi wa low cut ba ta hana nannadadden gashinsa nunawa ba. Duk da ya fi Hamida haske, amma ba zaka kira shi da fari ba farat daya.

 Wayewa da ilmi da suka ratsa shi ga kuma iya daukar wanka su ke dada fitar da kwarjininsa. Ko ita kanta Hamida idan ta kalle shi ta kan raya ya fi karfinta, amma tattali da kulawar da yake nuna mata su suke dauke duk wani shakku daga zuciyarta.

 Sai da ya bude kofar gate din gidan zai shiga, san nan Sofi ta yi sauri ta bude mota ta fito ta nufi wajensa. Yana shiga gidan ta na rufa masa baya. Motsin da ya ji a a bayansa ya sanya shi juyawa.

 Yana ganin ita  ce ya dada daure fuskarsa. Hakan bai saka ta ji ko dar a zuciyarta ba. Ta karasa kusa da shi. San nan ta dada lankwasa  murya tace “DR na ya kake”?

 “Kalau na ke”. Shi ma ya masa mata a dake. Ganin yana kokarin tafiya ya barta ta yi saurin shan gabansa. Ba tare da tayi niyya ba kawai taji kuka ya kwace mata.

 Tabbas ba pretending ta ke yi ba. Kukan daga zuciyarta yake, amma ko a kwalar Baffa. Shi kukan na ta ma sai ya zamar masa hayaniya.

 “kin ga idan kuka zaki tsaya yi min ni ina da abin yi”, ya fada yana mai kokarin fara tafiya.

 “Don Allah ka tsaya ka saurareni”.

 “Ina jinki” ya fada, ba tare da ya saki fuskarsa ba.

“DR na me ya sa baka sona? Bani da kyau ne ko kuwa? Me wata mace zata nuna min? kyau dukiya wayewa da ilmi duk ina da su. Me na rasa da kake guduna? Ka tuna fa ni kanwarka ce. Me ya sa zaka gujeni?

 Ka daure ka karbi tayin soyayyata ni kuma na yi maka alkawari ba zaka taba nadamar zama da ni ba. Zan sadaukar da rayuwata wajen kyautata maka. Zan gwada maka soyayar da wata mace bata taba gwadawa mijinta ba”.

 Taso ta bashi tausayi ganin kukan da ta ke bil hakki da gaskiya. Amma ko yaya, ya tuna irin tashin hankalin da Innarsa da Babansa suka shiga ranar sunanta sai ya ji tsanar da ya ke ma ta ta yi yawa.

 Bakin verander gidan ya nema ya zauna. Ita ma ta mike ta biyo shi. Gefensa ya nuna mata ya ce “zauna a nan”.

 Hawayen da ke idanunta ta share. Har da murmushi saboda hango alamun nasara da ta yi.

 “Idan na tambaye ki zaki fada min gaskiya”?

 “Na rantse da Allah duk abin da kake son sani zan gaya maka sai dai in ban sani ba”, ta fada da hanzari.

 Hannuwansa duka biyu ya sanya ya shafi fuskarsa, san nan ya ce “ni waye a wajenki”?

 “kai causin di na ne”.

 “Yaushe ki ka fara so na”?

 “Ranar da na ganka a TV. You were wearing a kaftan kalar sky blue da hula da ta yi matching da kayan. I can remember that day kamar hoto a raina”, ta fada cike da murnar abin kirkin da ta yi.

 “Ke nan kafin lokacin ba ki iya tuna inda kika taba ganina”.

 Cike da shagwaba ta ce “ai Mommy ta ce tun bani da wayo ka bar kasar nan shi ya sa ban san ka ba”.

 “Hakane”. Sai da ya sake nisawa san nan ya ce “ke nan a ranar ki ka fara sona”?

  “ Yes! Ranar farko da na ganka a TV. That was when I fell in love with you”.

 “So kafin nan ba za ki iya tuna kin taba gani na a wani waje ba”?

 “Ai na gaya maka my DR ranar na fara ganinka”.

 “Ni kuma saurara kiji tawa amsar. Na sanki tun ranar da aka haife ki. Ranar da aka haifeki Innata da Gwaggona kwana suka yi suna bauta a gidanku.

 Kwananki biyar suka dauki tuwo malmala biyu su ka bani in kaiwa Abbana da Babana, kanwar babarki ta ce musu barayi masu satar abinci a gidan mutane.

  Zan iya tuna ranar sunaki iyayenki suka kai mahaifiyata da tshohon cikin kannena police station a kan Sarkar da yayanki ya sata.

 Kwananki tara a duniya mahaifina ya rasu sakamakon wulakancin da mahaifinki ya yi masa.

 Watanki biyu da kwana goma sha bakwai tawa mahaifiyar ta bishi, saboda bacin ran iyayenki zuciyarta ta buga ta bi babana.

 Kina da shekaru takwas na kai ziyara gidanku ki ka watsa min ice cream a jiki na. kina da shekara goma na je gidanku ku ka tura karenku ya kashe ni.

 But its like you cant remember any of those moments”.

 Kuka ne ya sake barke mata na ganin in da ya dosa. Cikin kukan ta ce “amma ai duk ba laifi na ba ne. su Mommy sun yi maka laifi amma ba ni na yi maka ba”.

 “Very good” ya ce da ita. “yanzu saura wata tambayar. Kin tambayeni me ki ka rasa. Yanzu zan gaya miki. Baki da iyayen da su ka san darajar zumunci. Baki da iyayen da su ka san tausayin talaka.

 Kin rasa komai. A duk sanda na kalleki you bring back bad memories a zuciyarta. Saboda haka zamana da ke ba zai yiwuwa ba. Saboda ba zan zauna da abin da duk sanda na kalleshi sai naji tashin hankali ya zo min ba.

 Kuma abin mamaki, sai yanzu da ki ka ganni a TV ki ka ji ki na sona. Sai yanzu da na zama wani abu ki ke ganin na kai matsayin da za ki iya mu’amala da ni. Da ace na zama kamar yayanki Amir za ki iya aurena”?

 Shiru ta yi ta kasa ba shi amsa. Mikewa ya yi ya na fadin “go back home. For the first time ki sa a ranki ba komai kika nema zaki samu ba”.

 A yanzu kam zuciyarta ta gama baci da wulakancin da AMA ya ke mata. Mikewa ta yi ta share hawayenta. San nan ta ce “DR AMA ka shirya. Aure da ni kai kamar an yi  an gama”.

 Kada kafadunsa ya yi alamun bai dameni ba, san nan ya ce “wan nan kuma ya rage naki”, ya fada yana mai karasa shiga falon gidan.

 Yana shiga Kalmar InnaLillahi wa inna ILaihi raji’un ta subuce daga bakinsa, saboda ganin Hamida a tsaye a bakin kofar shiga falon.

 Ba tsayuwarta ce ta daga masa hankali ba illa yanayinta da ya gani. Gaba daya jikin ta rawa yake na alamun ta shiga tashin hankali wanda ke nuna tabbas ta ji zancensu shi da Sofi.

Comments

Popular Posts