☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* 28 ☘️☘️☘️☘️☘️

 

           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/


TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=0



CHAPTER TWENTY EIGHT

 Mallam Jibo da Wabili ba su bari Hamida ta ji labarin da Honourable ya zo da shi ba. Sun fi son su ga inda hankalin yaron ya karkata.

 Baffa kuwa yana kokarin karasowa gida sai yaga la’asar ta kusa. Saboda haka nan masallacin Faruku ya tsaya domin gabatar da sallah kafin ya karasa gida.

 Saboda dan tsallake ne da tsohon gidan su da kuma sabon sai ya zamana har yanzu mutanen gidansu a nan suke sallah.

 Honourable yana hango shi ya nufe shi da hanzari yace “Mallam Jibo bai sanar maka ina nemanka ba”.

 A dan fuzge ya ke magana kamar ba ya son yin ta. San nan y ace “ai ban ma karasa gidan ba. Na tsaya yin sallah ne”.

 “Ok ba damuwa mu karasa gidan tare”.

 “A’a kaje zan zo bari in yi magana da Abba tukunna” Baffa ya bashi amsa.

 Sule mai shayi ne ya hango su tsaye ya nunawa Mallam Jibo su. Wajensu suka karasa. Nan kuma liman shi ma ya tsaya domin su gaisa. Kamar hadin baki suna tsaye sai ga mai unguwa.

 Burin Honourable ya janye Baffa saboda shi kadai ya ke son magana da shi. Domin yanzu wata kafafa ya ke da ke nuna yafi kowa matsayi a wajen Baffa.

 Kamar Baffa ya san abin da Honourable ya ke shiryawa, sai ya gayyaci duk wadanda suke tsaye a wajen domin su raka shi tattaunawar da zai yi da Honourable.

 Duk da ran Honourable bai so ba, amma kuma ya na son tabbatar musu da matsayin da ya ke da shi a wajen Baffa.

 A falon gidan su ka zauna shi kuma Honourable ya shiga domin kiran Mommy, saboda ta ba shi dokar a gabanta za ayi komai. Ganin dattawan unguwar kuwa bai hana shi kiran na ta ba.

 Nan kuma Amir ya shigo ya durkusu da irin ladabin ‘yan shaye shaye ya na gai da su. Burinsa ya samu wanda zai ba shi ko da naira dari ne a mazauna falon.

 In ban da kaurin wiwi ba abin da ke ta shi daga jikinsa. Shi kansa Honourable yanzu kunyar nuna Amir a matsayin dansa na fari yake. Ya girmi Baffa da sama da shekaru takwas, amma a gabansa ya zube yana masa fadanci saboda ya samu kudin cakun yau.

 Baffa tausayi yayan na sa ya ba shi ganin yadda ya banzantar da rayuwar sa, gaba daya. Shi kuwa Amir ya maida hankalinsa wajen Baffa ya na fadin “yallabai wallahi wayata ce aka sace shine nake son ka taimaka min in sai wata”.

 Baffa ya ce” ba damuwa ka same ni a gida an jima bayan magariba”.

 “Godiya na ke yallabai. Ai abokaina duk na shaida musu kanina ne zai kera jirgin da za adinga shiga. Eh Wallahi. Idan dai an fara hawa jirgin da zaka kera  eh Wallahi a dauke ni mai sayar da tikitin shiga jirgin. Kuma eh Wallahi ba uban da zai shiga sai ya biya. Eh Wallahi”.

   Mommy da Honourable da su ka shigo ba su ji dadin ganin Amir a falon ba. Amma haka suke dake. Mommy ta ce “Daddy ya abu na dangi kuma zaka gayyato bare”?

 Maganar ta yi mu su ciwo har za su mike Baffa ya hana su da cewar “Na san kowanne kira ne zai zaman mai muhimmanci gwara kuna nan din”.

 Daddy ya kalli Mommy ya ce da ita “tun da ya bukaci su zauna din gwanda su zauna. Duk da zaman da rashinsa ba abin da zai sa ko ya hana”.

 Duk ba su ji dadin yadda ya yi musu ba, amma suka nuna halin dattako ba su nuna bacin ransu ba.

 Aka kira Sofi ta shigo. Ta ci uwar kwalliya sai rangwada ta ke yi. Ba taji kunyar kowa ba ta nemi kusa da shi ta zauna.

 “Ya Dr ya kake”? ta tambayeshi cikin wata irin murya da ta lankwasa. Daga idonsa kawai ya yi ya kareta mata kallo. Duk sanda ya kalleta sai bacin ran abin da ya samu mahaifinsa ya fado masa.

 Ya daure yace “Lafiya”.

 “Kuma ran nan ka ce za ka dawo, sai kuma kaki dawowa”. Sai a lokacin ya yarda ashe idan ka na son mutum komai na sa burgeka yake yi. Bai taba ganin wanda shagabwa ta ke yiwa kyau ba irin African Queen dinsa.

 Tuno sunanta kawai ya sanya shi sakin wani murmushi. Ita kuwa ta dauka da ita ya ke. Sai ta sake lankwashe murya zata ci gaba da shagwaba wacce shi kuma haushi ta ke ba shi.

 Mommy ce ta ce “ai ke dai in kinga Baffa mantawa kike da kowa. Ga mutane ba ki gaishe su ba”.

 Ta juya inda su Mallam Jibo suke zaune ta ce “ya kuke”?

 Suma da Kalmar lafiya suka amsa mata.

 Honourable ne ya yi gyaran murya, san nan ya mai da hankalinsa wajen Baffa ya ce “abin da ya sa na bukaci ganinka saboda na yanke hukuncin hada ku aure kai da ‘yar uwarka Sofi”.

 A firgice ya juya ya kalleta. Ita kuwa har da rufe fuska wai ta ji kunya.

 Mommy ta yi tsagal ta ce ai na gaya maka Baffa yana kaunar Sofi kamar yadda take kaunarsa. Kai dai Allah yayi muku albarka”.

 Sauran mutanen falon har da Mallam Jibo suka fara addu’ar Allah ya sanya alkhairi.

 “Dakata Hajiya” Baffa ya fada ya na mai fuskantar Mommy. Ita kanta ba ta ji dadin yadda Baffa ya kira ta da sunan Hajiya ba. Ita da ke nunawa danta ne halak malak, kuma sai ya nemi tsinkata.

 Ba ta gama da wan nan mamakin ba ta ji shi ya na cewa “Ina fatan ba ni kuke nufin hadawa aure da wan nan immatured yarinyar ba”.

 “Wacce irin maganar banza ce ka ke yi haka? Da kai da ita duka daya kuke a wajena. Aure kuma nayi niyya ba fashi. Idan ma wani ne ke zugaka ka natsu ka dawo hankalinka. Ka ma je ka fara shiryen shiryen da ya kamata. Ko kuma ka bawa Mommynku kudin ita ta san me ya kamata ta yi maka”.

 “Ai sadaka ma idan ka bani ita ba zan karba balle har akai ga zancen bada kudi”.

 Da karfi Sofi ta saki ihun kuka saboda ta fuskanci DR AMA ba ya son ta. Daddy ne ya ce “yi shirunki aure kamar an yi an gama. Watau wan nan ‘yar kasar waje da ka je shi ne kake son ka nuna ka fi karfin ni ubanka in tankwara ka”.

 Shi dai Mallam Jibo ya ma rasa me zai ce. Su Mallam Liman kuwa da Sule mai shayi da kuma mai unguwa sai kakabin wan nan abu suke yi.

 Mikewa ya yi da niyyar ficewa daga falon. Honourable da Mommy na kwalla masa kira, amma ya yi biris da su. Mallam Jibo ne ya dan daga murya alamun bacin rai, ya ce “To ayata? Ta burtu”. Watau yana nufin “ina zaka? Kar ka fita daga nan”.

Juyowa ya yi ya kalli Abban nasa saboda jin gargadin da ya yi masa mai nufin kar ya kuskura ya fita daga falon.

 Zuciyarsa wani zafi take na tukukin bakin ciki. Ya koma ya zauna. Amma zaman nasa sai ya zamana dama sun barshi ya tafi.

 Kallon Honourable ya yi san nan ya ce “SAI YANZU ka san ni danka ne? idan baka manta ba in tuna maka bakin cikin abin da kuka yi wa mahaifina ranar sunan wan nan sakaryar da ka ke son in aura”.

 “Kar ka kuskura ka zageni” Honourable ya fada a zafafe.

 “MH MH Daddyn Amir kar ka bari dokin zuciya ya ja ka. Ai na gaya maka dama sai kayi kokarin ka kunce kullin da aka yi masa. Ka san fa mutane ba abin yarda ba ne.

 Ka ba wa mutum amana ya ci ba sabon abu ba ne. In ma ban da rashin hankali mutane ta ina daga rike min sai ya zama gado na ne ”.

 Mallam Jibo kwalla ce ta fara zubo masa na fahimtar inda zancen Momi ya dosa. Tabbas shi take nufin ya mallake Baffa ta hanyar asiri.

 Baffa kuwa bai kula da halin da Abbansa ya ke ciki ba ya mai da hankalinsa kan maganganun da ya ke gayama Honourable.

 Ya ce “bakin ciki cin mutunci da tozarcin da kuka yiwa mahaifiyata shi ya yi sanadin mutuwarsu duk su biyu. Tun da suka mutu ko huduba ba ka iya yiwa yaran da suka mutu suka bari ba.

 Bayan nan ko gidan nan na zo korata kuke yi kamar kare. Kai Karen gidan nan ya fi ni daraja.

 Yanzu in za a kashe ka, ba ka san a ina na yi makaranta ba. Haka zalika ba ka san ina kannena suka yi na su karatun ba.

 The last time da na zo gidan nan, zuwa nayi in sanar da kai na samu scholarship zuwa waje ka samun hannun a takardar a matsayinka na shakiki na. Amma in ban da wulakanci ba a bin da na samu.

 Ku saurareni ku ji alkhairin da ya same ni ku ka kasa. Na sake zuwa domin in gaisheku. Matarka ta sa Amir ya kunce kare ya tura min shi har suna fadin ya yagalgala ni.

 I have not forgotten any of those issues. Da kuka gane Amir ne ya saci Sarkar da aka lakawa mahaifiyata ai hakan bai sa kun nuna nadamar ku a akan abin da ku ka yi musu ba.

 Ka dauki kannena marayun Allah ka sayar da daya a duniyar siyasarka ka bayar da daya tana aikin bauta a gidan ‘yarka.

 Sai yanzu ka san ni danka ne. Sai yanzu ne ka san zaka bugi kirji ka ce kana da iko da ni. Sai yanzu ne zaka nuna karfin ikon ka a kaina. Sai yanzu ne ka ke jin kana da damar da zaka tursassa ni in yi abin da kake so.

 Sai yanzu ne ka ke jin na kai mizanin da zaka iya hada zuri’a da ni”.

 Muryarsa ta sarke alamar bacin rai ga idanuwansa da su ka yi ja. Su kuwa Mallam Sule mai shayi da mai unguwa sai gyada kai suna fadin “Hakkun an yi haka. Ita dama duniya ai juyin waina ta ke yi. Yau ka na kasa gobe kana sama”.

 Shi kuwa Mallam Jibo hawaye ne ya ke kwaranya daga idanunsa, saboda gugar zanar da Mommy da Daddy su ke masa.

 Shi kuwa Baffa Wallet din sa ya zaro daga aljihunsa ya fito da wasu nannadaddun kudi wanda da gani ka san sun dade a ajiye. Mommy ya mikawa ya na fadin “kin san wan nan kudin ko na meye? Tun wadanda ki ka bani ne da cewar in je ‘ko ‘yar kumbotso nan in je in sai form dinta, saboda ba zan iya karatu a university ba’.

 Sai abin ya bani mamaki da na ga duk abin da kuka mallaka kun kasa sayawa naku ‘ya’yan ilmi.

 Amma ni yanzu kun ga achivements di na shine yanzu ku ke ganin ni danku ne. Da ku ke son in auri wan nan yarinyar ku ba ku san duk sanda na kalleta ba na tuna komai sai mutuwar iyayena.

 To me she is attached ta a bad memory da kullum in na ganta sai na tuna mummunan al’amarin da ya same mu a rayuwa”.

 Mommy da ta rungume Sofi ta na kokarin lallashinta saboda kukan da ta ke zabgawa, ta kalle shi ta ce “yanzu Baffa sai kace ba musulmi ba. Ka taba ganin wanda ya mutu kwanansa bai kare ba”.

 Daga kafadarsa ya yi alamun ko oho. San nan ya ce “whatever. Abu daya na sani ko mata sun kare a duniya ba zan auri wan nan sakaryar ba” ya fada yana mai nuna Sofi da ke ta gursheken kuka a wajen.

 “Aure zan daura shi sai dai ka kasheta idan an kai maka ita” Honourable ya fada. San nan ya juya wajen matarsa ya ce “kwarai na yarda da maganar ki ta cewa asiri aka yiwa da na. Duk bakin cikin mutum sai dai ya mutu saboda ‘da dai nawa ne. Kuma aure zan daura shi nan da sati biyu”.

 “Za ka iya daura aure ko yanzu ma. Amma ina son in sanar da kai in ka ga dama ka daura min aure da ita sau dari. Ni kuma na yi alkawarin sakinta sau dari.

 Bakin ciki ya kama Honourable har bai san sadda ya juya ya kalli Mallam Jibo cike da masifa ya ce “kai kuma tsohon bafullatanin kauye. Ka sakar min kurwar ‘da na da ka kama. In ba haka ba shari’a ce za ta yi maganinka”.

 “Da wa zaka yi shari’a? Ba dai da Abbana ba. Okey za ka iya. Tun da ka kai dan uwanka ciki daya police station a kan kazafin da matarka ta yi ma sa, ba wani abin mamaki ba ne don ka kai amininsa in da ka kai kaninka ba.

 Amma yanzu ina son sanar da kai. Yanzu ba da ba ne. Duk abin da zaka yi kar ka kuskura ka tabamin Abbana. In da takamarka kai ne ka ke jan linzami dokin duniya. Yanzu ko hanyar da dokin ya kai ba ka isa ka bi ba….”

 Mallam Jibo dai da kuka ya fice daga gidan. Ya yin da sauran suka rufa masa baya. Shi ma kuwa yana gani haka ya mike ya na fadin “I believe I don’t have anything more to say”.

 Ya juya ya yi ficewarsa da ga gidan. Ihun kukan Sofi da kuma kiran da Mommy ke yi masa bai sa shi ya dawo ba.

Comments

Popular Posts