☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* 24 & 25 ☘️☘️☘️☘️☘️

            *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/



CHAPTER TWENTY FOUR

 Hamida ce zaune a falon Wabili tana kokarin zubawa Baffa abinci. Sakwara ta daka ma sa da miyar vegetable da ta koya a wajen Zahra.

 Wayarsa ce ta yi kara. Ta daga ido ta kalle shi. Saboda ko yaushe tana masa mitar ba ya samun isasshen hutu. Ko yaushe ko yana kan computer din sa ko kuma yana waya.

 Hada ido su kayi, san nan ya kalli fuskar wayar ta sa. Dauka ya yi ya na fadin “yi hakuri in amsa wan nan. Boss di na ne da ga Japan”.

 “Kon nichiwa”, ya fada yana russunuwa irin gaisuwar kasar da ya ke karatu. Da yaren Japanese hakan na nufin ‘barka da rana yallabai’. Jin ya canza harshe ya sanya ta fara kokarin mikewa domin ta bashi guri, amma sai ya yi mata alama da ta koma ta zauna.

 Tana zaune tana kallonsa yana ta zabga turanci da kuma tsarma yaren Japanese a cikin zancen na sa. Ya dau kimanin minti ashirin suna waya da shugaban kamfaninsu na Hitachi.

 Bayan ya ajiye wayar ya yi kokarin mikewa da sauri. Duk wanda ya kalli fuskarsa ya san yana cike da farin ciki.

 “ko ba ka fada ba, na san labari mai dadi kake saurin zuwa ka sanar da Abba. Amma ka yi hakuri ka zauna ka ci abinci bari in kira Abban da kaina” ta fada ta na mai mikewa daga inda ta zauna.

 Da sauri ya ke cin abinci alamar umarninta kawai ya bi, amma hankalinsa ba ya kan abincin.

 Bayan kamar minti biyu suka dawo tare da Abban da kuma Gwaggonsu.

 “Me ya faru uban masu gida? Hamida tace in zo ka na son ganina”.

 Cike da murna a muryarsa  yace “Abba, shugaban kamfaninmu ne ya kira yanzu yana gayamin, sabuwar gwamnatin Nigeria ta na nemansu domin su shiga gasar neman kwangilar jiragen kasa da muke bukata. To shine ya wakilta ni a matsayin shugaban team din da za su wakilci kamfanin namu a majalisar dattawa ta kasar nan.

 Sauran zasu iso jibi saboda nan da kwana uku ya kamata muje majalisar.

 Saboda haka ya kamata gobe in je Abuja kafin su iso jibi in nema musu masauki san nan mu tsara yadda zamu gabatar da fasahar mu a gaban majalisar”.

 “Ikon Allah. Yanzu Baffa kai ne zaka majalisa har a tattauna da kai”?

 “Ai Abba ba ma ‘yan majalisar ne kawai ba. Ana kyautata zaton shugaban kasa da minister sufuri da kuma na kudi zasu halarci taron. Abba ka taya mu da addu’a. Allah ya bamu sa’a”.

 Sujudu shukur Abban ya durkusa ya yi. Duk da bai san matsayin da Baffan ya taka ba, amma tabbas ya san daukaka ce Allah ya kawo masa. Yana dagowa kuwa sai ga hawaye a fuskar Abban.

 Baffa har ya fara sabawa da hakan. Saboda duk sanda wani abun alkhairi ya same shi, sai Abban ya yi kuka saboda tuna abokinsa da ya kan yi.

 A ranar Wabili sai da ta dafa lafiyayyen abinci da ya ciyar da miskinai sama da dari biyu, saboda wan nan alkhairi da ya samu Baffanta.

 Shi kuwa Malam Jibo almajirai ya sanya suka dinga saukar Qu’rani ana sadaka duk don murnar abin arzikin da ya samu Baffa.

 Cike da addu’oin fatan alkhairi da Abba da Gwaggo suka cika Baffa da shi ya nufi Abuja. A Sheraton su ka yi masauki inda ya kama musu executive suite saboda su ji dadin aiki shi da sauran Team din da ya ke tsammanin za su iso daga Japan.

 Tun da suka zo kuwa suka dukufa wajen tsara yadda za su gabatar da fasahar su a gaban majalisar da kuma shugaban kasa. Baffa kuma suka zaba a matsayin wanda zai gabatar da komai a gaban majlisar saboda shine dan kasa.

 Yin hakan sai suke ganin zai basu damar jan hankalin masu saurare saboda ganin nasu ne a kan aikin.

 A ranar da za a zauna, Baffa cikin shigar bahaushe, in da ya sha kaftan ta shaddarsa mai kyan gaske da kuma hularsa zanna Bukar. Da ka gan shi ka san cikakken Hausa Fulani ne. a lokacin da suka zauna da sauran ‘yan team dinsa a inda aka tanadar musu, da yawa a zauren majalisar sun dauka ko ma’aikacin da zai kula da su ne.

 Amma bayan shugaban kasa ya zauna shi da ministoci uku da suka rako shi. Sai da aka gabatar da kamfanin Hitachi a matsayin kamfanin da ke kokarin ganin ya samu kwangilar sayarwa da Nigeria jiragen kasa, sai kawai kowa ya ga Baffa ya mike a matsayin wakilin kamfanin.

 Sai da ya gabatar da kansa inda ya ce “sunana Ahmad Musa Ahmad. DR a fannin Mechatronics Engineering.

 San nan cikin tsararraen turancinsa ya ci gaba da  yi musu bayanin irin jiragen da kamfaninsu ke da burin sayarwa ga kasar. Ba ka jin sautin komai sai na tsararren turanci Baffa. Sai lokaci lokaci ya juya harshe cikin harshen Japanese ya bukaci abokan aikinsa su tura masa wani hoto ta cikin projector da yake amfani da ita domin dada fahimtar da ‘yan majalisar nagarta jiragen da su ke so su sayar musu.

 Ya kai kimanin minti arba’in da uku ya na bayani. Kafin ya bada damar tambaya ga wadanda suke kokarin neman Karin bayani.

 Da yawa ‘yan majalisar sun gamsu da bayanin da kuma kwarewar da Baffa ya nuna a wajen gabatarwar ta sa. Sun kuma bayyana hakan a gareshi.

 Yayin da dan majlisa mai wakiltar Ogun ta tsakiya ya kara da nuna jin dadinsa na ganin dansu ne mai wan nan ilmin.

 Shugaban kasa ne da kansa ya nuna ya na son ya yi masa tamabaya. Ya kalli Baffa wanda ba wata alamar fargaba ko rashin yarda da kansa a tattare da shi, san nan yace “idan nabawa kamfaninku damar kerawa kasata jirage lissafin mu mutum biyar da zaka fara dauka a ciki”.

 Ya sake mikewa san nan ya fuskanci shugaban kasa ya ci gaba da bashi amsa da harshen turanci in da ya ce “na farko yaur excellency zan dan so in canza harafin ka na kasata ya koma kasar mu”.

 Aka dan yi dariya a majalisar na rahar da Baffa ya sako a cikin zancensa. San nan ya ce “zan roki alfarma mutanen da za su fara dana jirgin da zan kerawa kasata su zama shida.

 Mutum biyu na farko sune Gwaggona da Abbana saboda su suka hana ni kiran kaina maraya. Sai kuma Dr Adam Mukhtar, director na ci gaban ilmi boko a jihar Kano, saboda shi ya dora ni a tsanin duk matakin da na kai.

 Sai kuma gwamnar jiharmu Alhaji Inuwa Abubakar digil wanda ya yarda da kwazo na duk da ni kaina ban san zan iya karatun da ya bani damar in yi ba.

 Sai kuma kanwata Hamida. Sai kuma na karshe you your excellency sabo da na hango ka yarda da kwazon kamfaninmu tun da har ka na neman wadan da za a dana a jirgin”.

 Duk dariya aka saka a majalisar. Bayan nan suka mika report din su ga minister sufuri na kasa.

 A kofar majalisar ma ‘yan jarida ne damkar suna dakon fitowarsa, saboda tun da aka hanga aka ga Baffa na gida ne amma fararen fata sun nada shi jagoransu a kasar sa, kowa yake son yaji daga bakinsa.

 Nan ma suma suka tare shi da tambayoyi. Kuma duk cikin hikima da kwarewa ya ke amsa musu.

 Suna kaiwa masaukinsu kuwa wayar Chairman din su ta tare shi inda ya ke nuna farin ciki da yadda Baffa ya gabatar da komai.

 Abba da Gwaggo kuwa tun da aka fara hirar nan shi da Gwaggo suka kafa suka tsare a gaban talabijin. Shi yana falonsa da tsoffin abokansa da kuma su liman da mai unguwa na tsohuwar unguwar da suka ta so.

  Musamman ya gayyato su domin su zo su kalli hirar da za ayi da dansa a gidan talabijin. Dan gidan mai unguwa da ke karatu a jami’a shi ya dinga fassara musu wasu daga cikin abubuwan da Baffa ya fada.

 Duk da ba su fahimci fiye da rabi ba, amma murna ta cikasu. Ko ba su fahimta duka ba, sun dai san Baffa daukaka ce Allah ya kawo masa.

 Ita ma Wabilin a nata bangaren Hamida na fassara mata abin da Baffa ya ke fadi.

  A gidan Honourable ma da ke nan Kano duk suna a zaune a falon gidan. Saboda kasa jamiyarsu da jamiyar adawa tayi ya sanya su ka dawo Kano da zama. A wan nan lokaci suma suna zaune su na kallo. Amma ba tashar labarai suke kallo ba. Sofi ce ke kallo waken waken da ta saba.

 A garin canza tasha ta kamo tashar NTA news a dai dai lokacin da Baffa yake gabatar da kansa a wajen ‘yan jarida. Har zata canza amma sai kyawunsa ya dauki hankalinta ta fasa canzawar.

    *************



CHAPTER TWETY FIVE

   Amira na kwance a kan doguwar kujera Zahra na matsa mata kafarta. Saboda tun da cikinta ya kai wata takwas Mommy ta dawo da ita akan wai ta na wahala gwara ta dawo ta haihu a gabanta.

 Suna zaune har da Mommy da Honourable aka hasko hoton Baffa a talabijin din.

 “Wow! What a handsome guy”. Sofi ta fada. Kalamanta su suka ja hankalin duk mazauna falon suka dago kansu domin ganin mutumin da ya burge Sofi.

 Karaf idon Zahra a akwatin talabijin din inda aka hasko yayanta. Ita ma cike da mamaki tace “Lah ga Ya Baffa”.

 Dauke kallonsu sukayi daga akwatin talabijin din suka maida kan Zahra. Amira ce tace “kin san shi ne”?

  “Ya Baffa fa na gidanmu”, Zahra ta amsa mata. Wadan nan kalamai su suka ja hankalin Honourable ya maida hankalinsa kan Baffa dake tsaro turanci yana amsa tambayoyin da ‘yan jarida ke harba masa.

 Ba abin da ya raba shi da mahafinsa. Duk wanda ya san Mallam Musa ya kalli Baffa ya san jininsa ne. shi kansa Honourable din suna matukar kama da shi.

 Sunan da aka rubuta a dan kasan akwatin talabijin din watau DR Ahmad Musa Ahmad shi ya dada gogewa Honourable duk wani shakkunsa.

 Da sauri ya dauki remote ya karo sautin talabijin, nan kuwa muryar Baffa ta cika falon inda ya ke watso turanci kamar haifaffen garin Amurka.

 Duk da kasar da ya yi karatu ba turanci suke amfani da shi ba, amma yawancin koyarwa da turanci ake musu. Hakan ya sa bakinsa ya dada murjewa.

 Sai da suka gama sauraran tattaunawar Baffa da ‘yan jarida san nan aka shiga kakabin yadda Baffa ya koma. Zahra kuwa tayi funfurus ta ki sanar dasu komai akan Baffa. Ita ala dole ba ta san ko me ya ke ciki ba.

 Nan kuwa Honourable aka dauki waya aka fara bugawa abokai akan su kunna talabijin su kalli dansa da ya dawo daga karatu daga kasar waje. Ita ma Mommy tata wayar ta shiga bugawa kawaye domin ta nuna musu Baffa a matsayin dan da suka rike.

 Yayin da Sofi ta mai da hankalinta wajen binciko tasoshin labarai domin ta kara ganin Baffa da kyau.

 Ita dai Zahra tsabar mamaki ya hana ta Magana. A lokaci daya duk sun rude da ganin inda Allah ya kai Baffa. A sace ta zare jikinta ta shiga dakin da suke zama ita da Amal da Sadik. Saboda suna wajen Hajiyar Faruk sai ya zamana ita kadai ke zama a dakin.

 Yini kawai ta ke yi, amma Amira ba ta yarda ta kwana a wani waje ita kuma tana daki daban. Saboda komai dare taji bukatar wani abu za ta tashi Zahra domin ta bata abin da take bukata.

 Kowa ya san idan cikin mata ya tsufa, bacci na musu wuya. Idan kuwa ta kasa baccin nan haka za ta tashi Zahra ta saka ta matsa mata jikinta. Yadda mai cikin ba ta samun bacci. Haka ita mai mai zama da ita ba ta samu.

 Wayarta ta dauko ta kira Gwaggon ta. Ita ma cikin tsananin murna take bata labarin abin da ta fahimta a talabijin din da kuma abin da Hamida ta fassara mata.

 Katse ta tayi tana bata labarin abin dariyar da ya afku a falon gidan Honourable.

 “ikon Allah! Sai yanzu ya san dan sa ne. lallai mutane ba su da kunya”.

 “Ai Gwaggo yanzu haka kokarin zuwa gidan ku suke. Ni kuwa ba zan sanar da su kun tashi ba. Idan sun je sa nemi in da kuka koma”.

 “To ai kema idan ba kwatanta miki zan yi ba ai ba ki san inda mu ka koma din ba. Saboda tun da muka dawo baki zo Kano ba sai yanzu. Kuma baki samu zuwa na din ba”.

 “Ai ko na sani gwaggo ba sanar da su zan yi ba”.

 Dariya suka yi dukkan su suna murna wa junansu na abin arzikin da ya samu Baffansu. Bayan sun yi sallama ta dawo falon ta ci gaba da kallon drama da ‘yan gidan su ke yi.

 A ranar kuwa Honourable ya daura damarar neman gidan Mallam Jibo. Yaje tsohon gidansa aka sanar da shi ya tashi da ga nan. Haka kuwa ya dinga bibiya sai da ya samu wanda ya raka shi gidan Mallam Jibon.

 Ganin gidan kawai ya sanya shi sanin Baffa ya taka babban matsayi. Yana arba da Mallam Jibo ya mika masa hannu yana fadin “zuwa na yi in yi murna. Kaga matsayin da dana, ya taka. Kai Allah yaji kan kanina. Ina ma ya na raye ya ga yadda Allah ya mayar da Baffa”.

 Cike da mamakin fara’ar da Honourable ya tare shi da ita ya daure yana mai yin yake domin kar Honourable ya gane mamakinsa akan abin mamakin da ya gni a wajen yayan marigayi amininsa.

 Shi da kansa ya dinga gaisawa da su mallam Liman da kuma mai unguwa da ya tarar da su makil a falon Mallam Jibo. Su kansu sun yi mamakin ganin sakin jikin Honourable. Duk izzar nan da isa da kuma takama babu su.

 Wayar Mallam Jibo ce tayi kara. Yana dagawa ya ga Baffa ne ya ke kiransa. Cike da murna ya ce “Sannu Uban masu gida. Ai gamu nan da su mallam Liman duk mun taru muna kallonka sai turance turawan nan kake yi”.

 Dariya ya yi. San nan ya amsa masa da cewar “Abba addu’arka ce ta ke ta bibiyata. Yau nayi niyyar dawowa, amma kuma yanzu Minister ya aiko ya na son dada tattaunawa damu. Kuma ga dukkan alamu zamu samu aikin da muke nema”.

 “Kai madalla na yi murna kwarai. Ga su mai unguwa da su Liman har ma da Yaya duk gasu ku gaisa”.

 Kafin kowa ya karbi wayar, Honourable ya yi hanzari ya fizge wayar da ga hannun Mallam Jibo.

 Tun da ya fara Magana Baffa ya dauki muryarsa. Sai yanzu ya tuna shi Mallam Jibo ya ke kira da Yaya.

 Nan kuwa ya dage yana kuranta da kuma yaba kwazon Baffa. Har yana fadin ai su jininsu haka yake. Daukaka ce a tare da su.

 Amma ya manta ga Amir nan da ya zama da shi da babu duk daya sai kuma Saddam shima dan uwan dayan.

 Shi dai Baffa da eh ko ah ah ya ke amsa masa. Da kyar ya hakura ya bawa sauran suka gaisa da yiwa Baffa murna.

 Baffa dai meeting bayan meeting ya tsare shi a Abuja. Kuma Alhamdu Lillah kamfaninsu ya samu kwangilar. Take kuwa chairman din su ya yi wa Baffa alkawrin kashi 10 bisa 100 na duk ribar da suka samu a aikin. Saboda a ganinsa kwarewar Baffa ita ta basu damar samun wan nan aiki.

 A nan gida kuwa close marking Honourable ya ke yiwa Mallam Jibo. Koba komai ganin gidan da sun hakikance Baffa ne ya ginawa Mallam Jibo ya sanya Mommy ta zuge shi da ya tabbatar ya jawo dansa jikinsa.

 Ta kance “kar ka bari wan nan arzikin ya wuce mu. Da dai naka ne ba na kowa ba. Ban kuwa ga dalilin da kana raye wani zai ci arzikinsa sama da kai ba”.

 Hakan ya sanya shi zarya tsakanin gidansa da na Mallam Jibo. Kullum sai ya je gidan domin ya gani ko Baffa ya dawo. Banda uwar waya da ya ishe su da ita ta tambayar yaushe Baffan zai dawo Kano.

 Allah ya sani Mallam Jibo ba da gangan ya ki sanar da shi ranar dawowar Baffa ba sai domin shima bai sani ba. Saboda ayyuka sun rike shi a can.

 Hatta chairman din su sai da ya zo Nigeria, saboda nasarar da su ka samu. Sai da aka gama ciken ciken takardu, komai ya hau hanya. San nan ya koma.

 Wata daya ya bawa Baffa hutu, amma ya sanar da shi bayan nan ya dawo saboda su karasa aikin da gaggawa. Sun yi sa’a ma su na da coach coach na jiragen kasa. Da kuma kayuwansu, saboda haka hadawa ce kawai ta rage.

 Amma dole Baffa yaje ya tabbatar da ingancin jirage da za a kawo su kasar nan. Sai kuma aikin hadawa, da kuma tsara programme din da zai kula da kaiwa da komowar jiragen.

 Shi kuma wannan aikin IT department din su ne. Sa’a daya, sun tsai da shawarar amfanin da tsofaffin hanyoyin jirage saboda a rage yawan kudin da za a kashe. Gyaran da za a yi musu kadan ne su zama za su iya daukar sabbin jiragen.

 A bangaren Sofi kuwa ta fada kogin soyayyar dan uwanta. Ta bishi Instagram page din sa da shafin sa na twitter da face book. Anan ta ga sunan da yake mafani da shi watau suna sa na kuruciya da abokansa suka fi saninsa da shi watau AMA.

 Kullum yini take yi tana kallon hotunansa da bibiyar abin da yake yi. Ya yin da shi kuma a na shi bangaren bayan aikin da ya sa agaba, sai soyayyarsa da kanwarsa Hamida.

 Komai dare ya dawo daga meeting ko wacce irin gajiya ya dauko sai ya kirata a waya sun kashe kusan awa daya suna hira. Hakan da ya sabar mata ya sanya ko mai dare in dai bai kira ta ba, ba za ta yi bacci ba sai ta jira kiran nasa.

Comments

Popular Posts