☘️☘️☘️☘️☘️ *SAI YANZU❔* 22 & 23 ☘️☘️☘️☘️☘️

 


           *NA*

 

       *HANNE ADO ABDULAHI*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)


 

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.


INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/


FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/




CHAPTER TWENTY TWO

 Baffa ya sauka a Nmadi Azikwe International Airport, amma rashin sanin gari ya sanya sai da ya yi zaman jiran Ibu na awa biyu.

 Kalle kalle kawai yake yi yana yaba ci gaban da aka samu. Duk da dai ya san kasar da ya baro sun yi mana tazara, amma mu ma din ya yaba da azamar mu na kokarin shiga sahun kasashen da suka ci gaba.

 Wayar Ibu ce ta katse shi inda ya ke tambayar gate din da yake. Bayan ya sanar da shi bai haura minti goma ba sai ga shi ya karaso inda ya ke.

 UBER suka nema domin shiga gari. Ibu ne ya tambaye shi kwatancen gidan. Dan karamin katin da ya rubuta adireshin gidan da kuma lambar wayar Barrister, ya mika masa.

 “Ikon Allah! Alhamdu Lillah!” shine abin da Ibu ya ke fada bayan ya karanta katin da Baffa ya mika masa.

 “Hamdalar me kake jerawa ne”? Baffa ya tambaye shi.

“Saukin lamura na hangowa kaina”, shi ma ya amsa masa.

 A tunanin Baffa tsabar sanin gari ne ya sanya Ibu kwatancen inda za su je ba tare da wani shakku ba.

 Sai da su ka isa gidan ya ga Fadila da Fadil sun rugo sun rungume Ibu cike da murna da kuma dokin ganinsa, san nan kansa ya dada kullewa.

 Yana kokarin tamabayarsa inda suka zo saboda a tunaninsa ko wani gidan ‘yan uwansa suka fara zuwa kafin su je inda suka kudiri niyyar zuwa.

 Amma fitowar Barrister sai ya dada daure masa kai. Ya santa ne saboda hoton da Humaira ta taba aika masa na ita da Barrister. Maganar ta ce ta katse masa tunani, inda ya ji ta na fadin “autan Umma ina ka buya? Ko a waya ba a samun ka”.

 “Sorry Adda I went offshore. Kamfanin mu yana kokarin fara da aiki da wasu sabbin injuna, so I have to be there to supervise assembly na machinery din”.

 “Haka dai kullum. Offshore ko onshore. Idan kayi aure na ga yadda zaka yi”.

 “Adda yanzu ma uren na zo nema a wajenki”.

 Kunnensa ta kama ta dan ja alamar wasa, san nan tace “ka zo da bako ka tsaya shirme. Ko gurin zama ba ka ba shi ba. Ka tsaya shiriritar da ka saba. Bisimmilah matso ga kujera ka zauna” ta fadawa Baffa wanda mamaki ya dada kashe shi.

 Idan ya fuskanta da kyau Barrister yayar Ibu ce. Ibu ne ya katse masa tunaninsa inda yace da shi “bako matso ka zauna”, ya fada cike da zolaya.

 Bayan sun gaisa san nan Ibu ya sanar da ita matsayin Baffa. Bai kuma yi kasa a gwiuwa ba, ya sanar da ita muradinsa na son ta bashi damar neman auren Humaira.

 Da alamar zolaya ta ce “diyata karatu za ta yi. Aure ba yanzu ba”.

 Sakkowa yayi daga kan kujera ya zauna dai dai kafarta alamar kaskantar da kansa. San nan ya ce “please Adda kar muyi haka da ke. Baffa is my best friend, amma ya ce ke kadai zaki iya ba da uren Humaira.

 Ki taimaka min Adda. Ni ma ba yanzu nace ayi auren ba. I will be going for a course na shekara daya da rabi. Kawai so nake ki tsaya min komai ya hau hanya”.

 Sai da ta dan zolaye shi san nan ta amince. Amma da sharadin sai in Humaira ta amince da shi.

 Da Baffa kuwa ya dage wajen yi mata godiya akan abin da tayiwa Humaira, take ta mai da masa da cewar “da na yi wa Humaira mugunta da na cuci kaina. Saboda idan Allah ya kaddara aure a tsakaninsu da Ibrahim, da yanzu muguntar kaina zata koma”.

 Suna cin abincin da mai aiki ta kawo musu, Humaira ta dawo da ga registration din da ta je yi a NILE University. Ba karamar murna tayi ba ganin yayanta agidan.

 Barrister ce ta mike ta shiga ciki, san nan ta kira Ibu. Bayan sun shiga ciki ta garagade shi da kar ya sanarwa da Humaira dangantarsu, saboda ba ta so ita Humairan taji kamar ya zama dole ta amshi tayin soyayyarsa saboda halaccin da yayarsa ta yi mata.

 Haka kuwa ya hakura ya danne zalamarsa bai nuna mata komai ba. Kwanan su biya a gidan inda kuma har suka tafi Humaira ba ta fahimci cewar Ibu kanin Barrister bane. A tunaninta abokin yayanta ne kawai.

 A kuma dan alamun da ya fara nuna mata, ta nuna dan jan aji kadan za ta yi kafin ta amince masa.

 A ranar da yayanta zai koma Kano a ranar itama ta koma cikin makaranat da zama. Duk kokarinsa na ganin ya biya kudin makarantar ta da kuma na hidimar yau da kullum, Barrister ta hana shi. Ta nuna ya barta ta karasa ladan ta.

 Duk da haka ya karbi account number Humaira, saboda ya dinga yi mata aike saboda shi ma a wadace yake.

 Bayan dawowarsa ya dage da ganin ginin da ya kewa Abbansa ya kammala kafin ya koma. Sashe biyu ne a cikin gidan. Karamin flat mai daki uku daga farkon gidan. Sai kuma babban gida wadatattace daga ciki.

 Dakin Gwaggonsa kadai ya fi dan tsukakken gidan da suka taso girma. Ga falonta da bandaki da kuma dakin baki mata. Haka shima banagaren Abban nasa kamar na Gwaggon. Ga dakin ‘yan matan ta da kuma na Walid daga gefe.

   Ya saya masa mota kirar Vasso sabuwa dal. Ga kuma kayan gidan da aka zuba musu. Ranar da ya dauki Abban nasa domin yaje yaga gidan, saboda tun da suka sayi filin Mallam Jibo bai sake zuwa wajen ba.

 Saboda haka bai san ana gini ba. Sai da ya je ya ga gida kamar dauko shi aka yi aka dasa shi a wajen.

 A ranar ya yi kuka kamar idonsa zai cire. Fadi yake “ina ma Mallam Musa yana raye yaga yadda Allah ya mayar da uban msu gida”.

 Duk makotansa sun taya shi murna da wan nan alkhairi da ya same shi. Har kauyensu can mayo lofe sai da Baffa ya tura mota ta dauko ‘yan uwansa domin su zo su ga alkhairin da ya samu dan uwansu.

 Bayan ya gama da wan nan ya roki Barrister alfarma saboda ya na so ya biyawa iyayensa da kannensa zuwa aikin Hajji.

 Saboda haka Zahra ce kawai ba a je da ita ba, saboda ta koma Warri. Har ila yau Baffa bai shirya haduwa da Honourable ba. Ba irin magiyar da Abbansa bai masa ba, sai dai ya yi murmushi ya ce “Abba ka kara hakuri. Idan naje na dawo da ga wan nan tafiyar zan neme shi da kaina.

 Walid da Hamida ya canza musu makaranta ya mai da su Queens and King scince academy. San nan ya dauko musu lesson teachers saboda jarrabawar fita da za su rubuta.

 Malamar English daban sai kuma mai koya musu maths da physics. Da kuma wata malamar da ke koyar da su chemistry da biology.

 Duk malaman da ya debo domin lesson din mata ne. kudi masu yawan gaske ya ware domin biyan malaman.

 Ganin haka sai Malam Jibo ya bada damar duk yaran da za su rubuta jarrabawa a nan tsohuwar unguwarsu su hadu da nasa yaran domin daukar darasin. Hakan ya bawa dalibai da dama cin gajiyar alkhairin da Baffa ya nufa a kannensa.

 Ga shi dama kafin tafiyarsa, ya yi kokarin hana Mallam Jibo zama a shagon wanki, amma sai ya nuna masa akan cewa akwai samarin almajirai sama da ashirin da, da shagon wankin suka dogara. Kuma daman su na samun tsayayyiyar sana’a ya sanya sun shiga makarnatar koyon yaki da jahilci.

 Wan nan shi yayi sanadin da Baffa ya dada habaka shagon wankin saboda wadanda su ka dogara da ita su ci gaba da samun alkhairin cikin shagon.

 Ribar shagon kuma sai Mallam Jibo ya ke sadaukarwa ga sauran almajirai da ba su da galihu, in da ake basu sadakar dafaffen abinci sau uku a rana. Hakan yayi sanadiyyar rage yawan barace barace a unguwarsu.

 Ya yi zama na kimanin wata hudu a Nigeria, kafin ya tattara ya koma Japan.      





CHAPTER TWENTY THREE

 Humaira ta dage da karatun degree dinta, yayin da shi kuma Ibu ya ke ta kokarinsa na ganin sun samu fahimtar juna. Kuma Alhamdu Lillah, kauna da soyayya ingantacciya ta samu a tsakaninsu.

 Kamar kuma yadda Barrister ta tsara, sai da su ka yi nisa a dangantakarsu san nan Humaira ta gano shi kanin Barrister ne.

 A bangaren Zahra kuwa duk da jarrabawar ta tayi kyau, amma bata samu damar tafiya University ba. Amira ta yi sa’a Faruk ya tafi course na shekara daya. Kafin tafiyarsa har registration Zahra ta yi. Amma ya na barin kasar karatu ya sha ruwa.

 Ga matsin lambar da Saddam ya ke mata. Ya daina kokarin tabata saboda ta nuna ba ta tsoron yi masa rotse. Amma kullum ya na Warri wajen Amira saboda son Zahra.

 Ita dai addu’a kawai ta sa  a gaba. Ba ta son daga wa yayanta hankali, shi ya sa ba ta sanar da shi halin da take ciki ba. Haka nan ta san a yanzu za ta iya jan wuya ta bar gidan saboda Baffa shi ma wuyansa ya isa yanka.

 Amma in ta duba shakuwarsu da Amal da Sadik da kuma irin uwar da Allah ya basu, sai ta kasa jarumtar rabuwa da su. Ba su saba da kowa ba sama da ita. In za su shekara ba su ga uwarsu ba, ba abin da zai dame su. Amma ko dawowa su ka yi, Zahra ba ta nan an aiketa ko makamancin haka, yanzu za su shiga tashin hankali.

 Wan nan shakuwa ke sanyata, ta ke shanye wulakanci yayarta. Ga kuma uwa uba kirki da nagartar mahaifin yara. Yana mutunta ta da ganin darajar ta san nan ya na yabawa da kokarinta akan yaran da ma gidan baki dayansa.

 Sai da ya shafe sama da shekara a inda yaje course duk da dai Amira ta kai masa ziyara har sau biyu. Ba yadda bai yi ba ta tafi da yaran, amma taki saboda wai takura musu za su yi a cewarta.

 Lokacin da ya dawo kuwa ba karamin bacin rai yayi ba ganin Zahra bata shiga jami’a ba. Ya saka ta ta sake rubuta JAMB, amma shi ma duk da ta ci ba laifi, ba ta samu zuwa Jami’a ba saboda Amira ta samu cikin da ba tayi murna da samun sa ba, saboda ta na ganin takura mata rayuwa zai yi. Sai da Faruk yayi mata jan ido wanda ta kai har ya nuna idan ta bi ra’ayinta na kokarin zubar da shi, to kuwa a bakin aurenta.

 Wan na furgagi ya sanya ta hakura da zubar da cikin. Aiki ya dada rincabewa Zahra. Kullum tana fama da Amira. Tace zata ci wan nan ta ce za ta ci wan can. Ita ce matsa mata kafa ko yi mata tausa, saboda ciwon jiki da ta ke yawan korafi a kai.

 Likita kuma ya bata shawarar ta dinga yawan motsa jikinta, sabo da shine maganin ciwon jikin, amma ta ki.

 Idan ta zauna a waje daya, shiga banadaki ne kawai ke tayar da ita. Mommy da Sofi suka zo da sunan jinya, amma in ban da aiki da suka karawa Zahra ba abin da suke yi.

 Haka nan za su barrarraje kamar ba gidan suruki ba. Aci banza a ci wofi. Kuma duk Zahra ce mai hidima da su. Shi kansa Maigidan tausayinta yake ji na yadda take fama da yawan ayyuka.

 Humaira na second semester a NILE, Allah yayi wa Senator Alkassim rasuwa. Ya na hanyarsa ta dawowa daga meeting wasu ‘yan bindiga dadi suka harbe shi, yayin da suka raunana Drivern sa.

 Ai kuwa Mommy na samun wan nan labari ta baro Amira da ke fama da laulayi a Warri ta garzayo Kano domin ayi zaman makokin surukinta da su, ita da mijinta.

 A gidansu na Kano aka yi zaman makoki. Inda Honourable ya ware bakin aljihu aka dinga abincin gidan makoki ana kaiwa gidan Senator.

 Rabon su da ganin Humaira tun da suka kaita gidan miji. Amma duk da haka ba suyi fushi da rashin neman nasu da bata yi ba. Sai ma tattala ta da suke.

 Ko yaushe Mommy na rakube da ita, saboda a tunaninta takaba ta ke yiwa Senator. Bayan an share makoki, Mommy ta sa Honourable akan ya tsaya tsayin daka a raba gado a ba shi na ‘yarsa. Amma labarin da Humaira ta sanar da shi na cewar ita ba auren Senator akan ta ya tayar masa da hankali.

 Zagi dai ranar ta sha shi har iyayenta da ke kabari ma sun samu rabonsu. Da farko ma karyata ta ya yi, sai da mahaifiyar Senator da kanta ta sanar da shi abin da ya faru san nan ya yarda.

 Bakin cikinsa da yawa. Ga makudan kudin da ya kashe a zaman makoki, saboda shanu biyu ya sa aka yanka, saboda zaman makoki kawai. Ban da sadakar kudi da ya dinga bayarwa ana yi, duk dan ya nuna kansa a matsayin shakikin amaryar Senator.

 Mommy kuwa har ta fara budget na kudin da za su samu idan an raba gadon Senator an bawa Humaira tuminin takaba.

 Idan zaku tuna lokacin da iyayenta suka rasu, sallamar mutane ya yi a su nan ba ya zaman makoki. Amma a wan nan duk wata bidi’a sai da ya tabbatar da an yi ta.

 A wan nan dare da Mommy ta samu labari ta zagi Humaira kamar Allah ya aiko ta. Sai fadi take “saboda kin raina ni, har kishiya ta baki shawara ki biye mata. Amma ni ba zaki sanar da ni ba”

 Cikin hawaye ta ce “Mommy ba ni da number da zan same ki”.

 “Dan ubanki da baki da number ta ba ki san gidan da na ke ba. Ga shi nan ai ta kai ki ta baro. Banza shashasha. Kuma dan ubanki ki shirya, tun da kin ki wan can auren ki ka yarda kishiya ta yaudare ki, Amir zan aura miki”.

 “Idan har ta yarda ba”? muryar Dr Farida kawar Barrister ta katse ta. Kamo Humaira da ke tsaye ta na hawaye tayi. Ta zaunar da ita a bakin gadon dakin. Sai da ta share mata hawaye da suka zubo a fuskarta, san nan ta ce “daina kumfar baki. Ai sau daya ake yiwa yarinya auren dole. Ko kin manta bazawara ce. Saboda haka ita ke da ‘yancin zabawa kanta miji. Bayan haka tana da alwalin da ya fi ku kusanci da ita”.

 Mommy bakin ciki kamar ta zabgawa Dr Farida mari, haka take ji. Da da ne cewa zata yi Amir ya fi karfin auren Humaira, amma yanzu ganin ya zama dan kwaya tuburan shi ne ta ke son ta manna ma ta shi.

 Nan dai ta dawo tana labartawa Honourable abin takaicin da aka yi mata a gidan Senator Alkassim. Ba karamin bakin ciki su ka yi da butulcin da a cewarsu Humaira tayi musu ba. A haka Humaira ta samu ‘yanci wanda Barrister da kawayenta da kuma kungiyar sa kai da suka kafa domin tallafawa yara mata marasa galihu, su ka kwato mata.

 Duk da haka Barrister sai da ta ware wani kaso mai tsoka daga cikin gadon Senator da aka bata ta rabawa Humaira da kuma mata biyu da Senator ya taba aura ya saki.

 Sauran kason nata kuwa gaba daya ta zuba shi a kungiyar sa kai domin taimakawa yaran mata.

 A dai dai wan nan lokaci kuma shi ma Baffa yana ta kokarin ganin ya canza akalar dangarta sa da Hamida. Ba kunya ya tashi daga yayanta ya koma masoyi na hakika.

 Kusan kullum ne sai ya kirata a waya. Hira kuma ta shakuwa ya ke janta ta daita. Sai ka gansu suna hira zaka karyata zancen Baffa ba shi da yawan Magana. Da ita kadai ya ke zagewa yayi hira son ransa.

 Da kuwa ya samu ta kammala jarrabawa tana zaman jiran sakamako sai soyayya ta barke a tsakaninsu. Abba da Gwaggo sun fahimci inda suka dosa, musamman idan yazo. Saboda yanzu tun da ya koma da kyar ya haura wata uku bai shigo Nigeria ba.

A haka har ya samu nasarar zama mataimakin professor wanda kwazonsa ya kai shi wan nan matsayi. Wani taron karawa juna ilmi ne ya kawoshi Ghana. Ana gamawa kuwa ya runguda zuwa Nigeria, saboda ya ga iyayensa da kuma kannesa. Hamida ta samu ta fara karatu a skyline inda ya zabar mata Sociology.

 Duk da ita a ranta ta fi son ta karanta Medicine ko Pharmacy. Amma tun da Ya Baffa ya zabar mata ra’ayinsa, ita ma kuwa ko furta zabinta ba tayi ba. Itama ta waye. Idan ka ganta ba za ka ce Hamidan lungun unguwa uku ba ce. Zaka dauka tun farko rarrafen carpet ce tashin video.

 Ta koma wata irin chocolate colour mai dan haske. Bakin ma da su Humair suke mata ba’a a kai ya koma wata irin kala mai kyawun gaske. Ashe dama bakin nata ba mai yawa bane. Saboda yanzu hasken ya rinjayi bakin. Ta koma wata hadaddiyar budurwa.

 Ga kyawun diri. ‘Yar shafal da ita. Sai kuma gashi baki sidik na fulanin asali. Fuskar nan doguwa mai dauke da siririn hanci da kuma dan madaidaicin bakin ta mai cike da siraran hakora farare tas da su.

 Yanzu kuwa da cima da kuma makwanci suka canza sai ta kuma hadewa. Hatta da telan da ke mata dinky sai da Baffa ya saka ta ta samu hadadde daga wajen sababbin kawayen da tayi a Queen scince academy.

 Idan suka jero suna tafiya sai ka rasa wanda ya fi kyau tsakanin ita da Baffa. Gaba daya Baffa ya daga mata darajar rayuwa.

 Fita su kayi shi da Hamida, wadda in dai yazo suna tare a koda yaushe. Ta raka shi ya yi wa Barrister gaisuwa san nan suka shiga super market. Sayyar kayan gida suka yi. Suna shigowa suka hadu da Chibbu kakar Hamida wadda Baffa ya biyawa aikin Hajji. Sun dawo kuma ya hanata komawa Mayo Lofe yace ta zauna ta dada hutawa.

 Suna  shigowa tace “hm kala gorko bangi debbo balejo fu, cede mako on chi kai”. Watau tana nufin “ duk wanda ya auri bakar mace kudin sa ne bai cika ba”.

 Dariya yayi. Sai da ya zauna kusa da ita san nan ya mayar mata da harshen hausa. Yana jin fulatanci saboda zamansa a wajen Mallam Jibo da Wabili. Amma nisan kiwon da ya yi sai ya dan yi rauni. Saboda haka ya na ji amma ba ya iya mayarwa.

 Cikin harshen hausa yace “ba sai a hada min da ke ba. Kin ga in na biya sadakin baka sai a hadamin da tsohuwa fara”.

 “Na fi karfinka. Shadi mijina yayi ya auro ni kai kuwa ko iskar bulala ba za ka iya dauka ba balle ita bulalar kanta” ta mai da masa cikin fulatanci.

 Mikewa ya yi ya fita yana ce da Hamida “don’t forget za mu fita anjima akwai dinner abokina da na gaya miki. And please don’t keep me waiting”.

Da ka ta amsa. San nan tace “What will you have for dinner”?

 “I thought we are going out. Ki huta kawai”

 “Mh mh kar muje kace ka kasa cin abin da aka ba ka a wajen”?

 “Ba sai in kwana da yunwa ba” ya fada da alamar zolaya.

 “Not when iam around”.

 Ita dai Chibbu tana kallonsu sai da ya fita Wabili ta shigo san nan tace “su wadan nan ‘ya’yan naku yaushe zaku yi musu aure, ko jira kuke sai sun bara da kansu.

 Wabili kasa bata amsa tayi. Sai da Mallam Jibo ya shigo san nan ta sake maimaita abin da ta gaya wa matarsa. Sai da ya dan nisa, san nan yace “Chibbu ba wai auren ne bana so a tsakaninsu ba. Amma ki duba matakin da Baffa ya taka, sai na ke ganin yafi karfin Hamida.

 Bayan haka bana son in tilasta masa abin da watakila ba shi ne a zuciyarsa ba. Kuma bana son mutane su zarge ni cewar ganin daukakar da Allah ya yi masa ya sa nake son hada shi aure da ‘yar cikina.

 Amma duk da haka ina kan yi musu addu’a. ke ma ita nake fatan ki taya mu da ita”.

 Bayan kuwa tayi isha. Ta dau wanka inda ta sanya wani lace mai kyawun gaske. Ta daura rawsilk a kanta. Fuskar nan sai sheki take yi. Ba ta cika fuskarta da kwalliya ba, saboda wani irin natural beuty da take da shi.

  Takalmi da jaka ta saka mahadin lace din. San nan ta yafa mayafi kalar kayan. Tun da ta fito ya kure ta da idonsa saboda kyan da tayi. Kusan ma ace ya manta da idanun iyayensa da kuma na kakarsa da ke falon.

 Sai da suka fita san nan Chibbu ta kalli Mallam Jibo tace “har yanzu kana tantamar abin da ke zuciyar ta sa? Amma ka jira zai bara din yadda kake so”.

Comments

Popular Posts